‘Yan takarar shugaban kasa a 2027 sun bude wani sabon babi bayan an bude yakin neman zabe a hukumance a ranar Laraba da ta gabata.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, sun zabi hanyoyi daban-daban don tallata kansu a ranar farko ta yakin neman zaben 2027.
Yayin da Tinubu ya zabi ganawa da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na ranar farko na yakin neman zabensa karo na biyu, Atiku ya tafi kai tsaye ga ‘yan Nijeriya ta hanyar yin bidiyo kai tsayi a shafinsa na sada zumunta na Facebook, yana amfani da dandalin wajen suka ga manufofin tattalin arziki na gwamnatin Tinubu.
A gefe guda kuma, Obi ya kaddamar da yakin neman zabensa da sakon da ya ta’allaka kan kwarewarsa da halinsa da jawo hankalin bukatar masu jefa kuri’a da kuma duba manufofin wadanda ke neman mulkar kasar.
Hanyoyin da ‘yan takarar shugaban kasa suka dauka na yakin neman zabe sun bambanta, yayin da aka kada gaggan yakin neman zaben shugaban kasa a hukumance a ranar 19 ga Agusta, 2026, kafin zaben shugaban kasa na ranar 16 ga Janairu, 2027.
Haka kuma ‘yan takarar shugaban kasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, sun yi alkawarin gudanar da yakin neman zaben cikin lumana da maida hankali kan batutuwa masu amfanar da al’ummar Nijeriya.
Tinubu a ranar farko bai fara da taron kamfen na shugaban kasa kamar yadda aka saba ba na kaddamar da yakin neman zabe mai daukar hankali ba.
Maimakon haka, ya zauna a fadar shugaban kasa da ke Abuja ya jagoranci taron kwamitin zartarwa na tarayya, taronsa na farko tun bayan ranar 29 ga Yuni, 2026.
Yayin da takwarorinsa suka fara bayyana hujjojinsu ga masu jefa kuri’a, Tinubu ya ci gaba da nuna ayyukan da ya gudanr a shugabancinsa da ke mai da hankali kan gwamnati.
Taron kwamitin zartarwar ya dauki wasu matakai game da tattalin arziki da ilimi da ababen more rayuwa da sauran fannonin gudanarwa.
Shi kuwa, Atiku a ranar farko ta yakin neman zabe ta ba shi damar kai tsaye kan tattauna batun tattalin arzikin kasar nan.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya yi amfani da shafinsa na Facebook a ranar Laraba wajen alkawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2027.
Atiku ya kalubalanci matakin da gwamnatin Tinubu ta dauka na cire tallafin mai.
Ya tambayi abin da ake yi da kudin da aka samu bayan dakatar da tallafin, yana jayayya cewa ya kamata ‘yan Nijeriya su ga fa’idodi a bayyane daga wannan tsarin ta hanyar gudanar da ingantattun ayyukan raya kasa.
Sakon nasa ya sanya ayoyin tambaya kan cire tallafi a jawabin farko na yakin neman zabe, yana bai wa masu zabe wani sabon shiri da ya bambanta da manufar Tinubu.
Atiku ya kuma yi amfani da fara kamfen din don neman karin bayani kan kudaden da gwamnati ke kashewa.
Amma shi kuwa Obi a ranar farko bai yi bayani kan sauyin manufofi mai daukar hankali ba, sai dai ya yi ne game da kafa sharuddan da yake so ‘yan Nijeriya su yi amfani da su wajen hukunci kan zaben shugaban kasa.
Ofishin yada labaransa ya gabatar da shi a matsayin dan takarar da ke da hankali, yana kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da kwanaki 150 na kamfen don duba tarihi, halaye da shawarwarin manufofin dukkan ‘yan takarar shugaban kasa.
Sakon bude kamfen na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC ya fi mai da hankali ne kan zaban cancanta maimakon yin alkawari kan wasu shirye-shirye.
Tawagar yakin neman zabensa ta yi hujjar cewa yakin neman zaben ya kamata ya zama dama ga ‘yan Nijeriya su binciki karfin wadanda ke neman shugabancin kasa kuma su duba tarihinsu na baya kan alkawuran da suke yi wa masu jefa kuri’a.
Shirin da Obi ya gabatar ya hada da ci gaban Nijeriya daga cima zaune zuwa masu fitarwa ta hanyar masana’antu, rage yawan kudin gudanarwa, karfafa ilimi da kiwon lafiya, inganta tsaro da samar da karin damar tattalin arziki.
Wannan sakon yana da daidaito da matsayin siyasa da Obi yake kokarin ginawa game da habakar tattalin arziki.
Hanyoyi uku sun ba da hasashen farko na yadda yakin neman zabe zai iya faruwa a cikin watannin masu zuwa.
Tinubu, a matsayin wanda ke rike da mukamin yanzu, ya farawa daga matsayin samun damar yin yakin neman zabe bisa tarihin mulkin da yake yi, wanda ya dauki manyan matakan tattalin arziki, yayin da kuma yake kare wadannan matakan da tasirinsu ga rayuwar ‘yan Nijeriya.
Atiku na neman juyar da rashin jin dadin mutane zuwa hujja don sauyi na siyasa, inda ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur ya zama daya daga cikin alkawuran da ya fara dauka idan aka zabe shi.
A nasa bangaren, Obi na kokarin sanya kwarewa, daukar alhakin da inganta tattalin arziki su kasance tambayoyi da za su yi tasiri a zaben.
Saboda haka, ya roki masu zabe su kimanta ‘yan takara fiye da tsarin jam’iyya, taron yakin neman zabe da kuma taken siyasa.
Ranar farko na bude yakin nema zaben ta bayyana fiye da ayyukan kowane daya daga cikin manyan ‘yan takara guda uku.
Ta bayar da alamar farko na hujjojin da kowane dan takara yake shirin gabatarwa ga masu jefa kuri’a.
Sakonnin farko na manyan ‘yan takara guda uku za a iya juya su zuwa goyon bayan masu jefa kuri’a a yayin da kamfen din 2027 ke samun karfi.














