An gudanar da gasar adabin ne don bunƙasa ilimin ‘ya’ya mata karo na uku mai taken ‘Fatima Dikko Raɗɗa girls child education summit and literacy contest’
Ita dai wannan gasa an samar da ita ce da nufin karfafa guiwar ‘ya’ya mata musamman abin da ya shafi karatunsu tun daga matakin firamare har zuwa jami’a ta yadda za su riƙa samun wakilci a fannonin rayuwa.
- ‘Yansanda Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Wasu Rukunin Gidaje A Katsina
- Gwamna Dikko Ya Amince Da Bude Asusun Bai-daya A Jihar Katsina
A karo na uku na wannan gasa, an zakulo ɗalibai daga ɓangarori huɗu da suka haɗa da ƙanana da manyan makarantun sakandire da masu karatu a matakin digiri na daya da na biyu domin fafatawa a wannan gasa wanda kungiyar ‘read Right Multipurpose education society’ suka saba shiryawa.
Ɗaliban da suka fafata a cikin wannan gasa su kimanin ɗalibai 41 daga ƙaramar sakandire sai kuma ɗalibai 54 daga babbar sakandire, sai ɗalibai 19 masu karatun digiri da kuma mutum biyu masu karatun digiri na biyu.
Daga cikin mahimman batutuwa da aka tattauna a wannan gasar ta bana sun haɗa da batun samar da tsaftattaccen ruwan sha da irin rawar da mata ke takawa wajan samar da tsaftataccen ruwan sha da batun ciwon daji ‘cancer’ da dai sauransu
Haka kuma kowanne rukuni an fitar da na ɗaya zuwa na uku, inda aka ba su kyaututtuka da kuɗaɗe domin ƙara masu ƙwarin guiwa musamman abin da ya shafi karatunsu.
Tun da farko shugaban kungiyar ‘Read Right Multipurpose education society’ Aliyu Nasir Ƙanƙara ya bayyana wasu ayyukan wannan kungiyar inda ya ce, an samu gagarumar nasara a cikin wannan shekarar ta 2023.
“Mun ƙaddamar da rabon littattafai a ƙaramar hukumar Musawa da Dabai a ƙaramar hukumar Danja, mun yi gangamin wayar da kai kan sha’anin shugabanci da kuma bayar da abinci a lokacin watan Ramadan da ya gabata”. Inji shi
Ya ƙara da cewa a shirinsu na a koma makaranta ”Back to School Campaign’ sun samu nasarar mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta 7,500, sannan sun yi taron wayar da kai dangane da matsalar rikice-rikecen cikin gida da sauran batutuwa da suka shafi al’umma.
Ita ma a nata jawabin kwamishiniyar ilimi a matakin farko, Hajiya Hadiza Yar’adua, ta yi bayanin cewa irin wannan gasa na nuna irin yadda aka nuna kulawa ga ilimin ‘ya ‘ya mata
Kwamishinan ta ce ko ba komi l, an sanar da wata sabuwar hanya ta karfafa guiwar ‘ya’ya mata wanda hakan ba zai sa a bar su a baya ba ta bangarori da dama.
“Yanzu muryoyin ‘ya ‘ya mata za su fara yin amo na gaskiya, musamman abubuwan da suka shafi ilimi na zamani da kuma na addini” inji ta.
Kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Katsina, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta nuna mahimmancin yin ilimin ga ‘ya’ya mata musamman a wannan lokaci da ake da ƙalubale kala-kala na rayuwa.
A jawabinta mai ɗakin gwamnan jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Raɗɗa, ta nuna farin cikinta kan yadda ɗalibai suka nuna ƙwazo da jajircewa a lokacin wannan gasa da ta gudana.
Hajiya Fatima Dikko Raɗɗa ta ce, haƙiƙa sun zama abin alfahari ga al’ummar jihar Katsina ta yadda da irin haka ne za su canza alƙiblar ilimi musamman na ‘ya’ya mata a jihar Katsina da arewacin Nijeriya.
An kammala wannan gasa ta adabi da bunkasa ilimi ‘ya’ya mata da aka yi kwanaki biyu ana gudanarwa tare da raba kyaututtuka ga waɗanda suka samu nasarar lashe gasar a Katsina.