Bayan da aka cimma tarihi mai cike da daukaka na shekaru dari, da shiga wani sabon zamani, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) ta shiga wani muhimmin lokaci mai matukar ma’ana a tarihinta.
A safiyar ranar 23 ga watan Oktoban shekarar 2022, a babban dakin taron jama’a dake nan birnin Beijing, cikakken zama karo na farko na sabon kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, ya zabi mambobi 24 na hukumar siyasa ta kwamitin koli karo na 20, inda aka zabi Xi Jinping, da Li Qiang, da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi, da Ding Xuexiang da kuma Li Xi a matsayin zaunannun mambobin hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kana aka sake zaben Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin. Aka kuma amince da mambobin sakatariyar kwamitin koli, sannan aka tabbatar da mambobin hukumar soja ta kwamitin kolin. Bugu da kari, aka amince da shugabannin hukumar ladabtarwa ta kwamitin koli karo na 20 da aka zaba a cikakken zama na farko.
A muhimmin lokacin da aka kama turbar sabon tafarki na gina kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu a dukkan fannoni, da kokarin cimma babban buri na biyu, wato zamanintar da kasar Sin zuwa kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu, yayin da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta cika shekaru 100 da kafuwa, daukacin jam’iyyar, da dukkanin al’ummun kasar nan, suna fatan zabar wata babbar kungiya mai hadin kai da karfi da za ta jagorance su, wajen daukar nauyin dake bisa wuyanta. A karkashin jagorancin babban sakatare Xi Jinping, za a ci gaba da karfafa nasarorin da aka cimma, da shawo kan matsaloli, da kuma tinkarar hadurra da sauye-sauye yadda ya kamata, ta yadda za a samu nasarar cimma burika a fannoni daban daban a sabon zamani da sabon tafarki.
“Jam’iyyarmu babbar jam’iyya ce mai mambobi sama da miliyan 96, wadda ke rike da mulki a wata babbar kasa mai yawan al’umma fiye da biliyan daya, don haka, muna da babban nauyi a wuyanmu, nauyin dake kanmu ba karami ba ne. Dole ne ta kafa hadaddiyar kungiyar jagoranci a siyasance, mai hadin kai, karfi da kuma aiki tukuru. Maganganun da babban sakatare Xi Jinping ya yi, suna da ma’ana da hangen nesa.”
Bisa cikakken shirin kwamitin kolin jam’iyyar tare da Xi Jinping a matsayin jagora, an gudanar da ayyukan tantancewa da zabar sabbin shugabannin kwamitin koli yadda ya kamata.
Tun daga farkon shekarar 2022, babban sakatare Xi Jinping ya saurari ra’ayoyin sauran mambobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin koli, kan yadda za a zabi ’yan takarar sabuwar hukumar da za ta shugabanci kwamitin kolin JKS.
Dukkansu sun yarda a saurari shawarwari da ra’ayoyi na wasu manyan jami’ai da nagartattun mutane fuska da fuska game da sabbin ’yan takara na sabuwar hukumar siyasa, da na zaunannen kwamitin, da na sakatariyar kwamitin koli na JKS, da manyan jami’an majalisar gudanarwa, da mambobin hukumar soja na kwamitin kolin, da sabbin ’yan takarar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, da dai sauransu.
A farkon lokacin zafi na shekarar 2022 a Zhongnanhai, inda kwamitin kolin JKS da majalisar gudanarwar kasar ke aiki, da misalin karfe 7 na safe, wani babban jami’i mai mukamin gwamna ko minista ya zo nan da wuri don shirya wata tattaunawa mai mahimmanci. A kwanaki biyu da suka wuce, ya samu sanarwar zuwa birnin Beijing, kuma bayan da ya iso Zhongnanhai ya san abin da tattaunawar ta kunsa.
A dakin hutu, ya karanta abubuwan da aka tsara gudanarwa, ciki har da “Shirye-shiryen da suka shafi Tattaunawa da Bincike”, “Jerin sunayen shugabannin jam’iyyar da na gwamnatin kasar”, “Jerin sunayen jami’ai ’yan jam’iyyar masu mukamin gwamna ko minista”……
An fara tattaunawa a hukumance da misalin karfe 9 na safe. Shugabannin kwamitin tsakiya sun yi musabaha gaba da gaba da mahalarta taron, inda suka saurari ra’ayoyi da shawarwari kan zaben sabbin shugabannin kwamitin tsakiyar.
Wannan ya nuna yadda ake gudanar da tattaunawa da bincike a fili.
Tun daga watan Afrilun shekarar 2022, babban sakatare Xi Jinping wanda ya ke fama da aiki a kullum, ya kan kebe lokaci na musamman don tattaunawa da kuma neman ra’ayoyi daga mambobin hukumar siyasa ta kwamitin koli masu ci, da sakatarori na ofishin sakatariyar kwamitin kolin JKS, da mataimakin shugaban kasar, da mambobin hukumar soja ta kwamitin koli, da yawansu ya kai 30.
Bisa shirin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, daga watan Afrilu zuwa Yuli na shekarar 2022, manyan shugabannin kwamitin koli da abin ya shafa, sun saurari ra’ayoyin manyan shugabanni ’yan jam’iyyar da na hukumomin mulkin kasa, da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar, da manyan jiga-jigan ’yan jam’iyyar wadanda suke rike da mukaman gwamna ko minista, da manyan hafsoshin rundunonin soja, ciki har da kwamandoji da kwamishinoni na siyasa da dai sauransu, da kuma mambobin kwamitin koli na JKS karo na 19, wadanda yawansu ya kai 283. A nasu bangaren kuma, shugabannin hukumar soja ta kwamitin kolin JKS sun saurari ra’ayoyin kwamandojin soja da takwarorinsu manyan hafsoshi, da yawansu ya kai 35 game da sabbin mambobin hukumar soja ta kwamitin kolin jam’iyyar.
Sannu a hankali za a zabi manyan shugabannin ta hanyar bincike da nazari da tattaunawa, da sauraron ra’ayoyi, sake tattaunawa da yanke shawara yayin taruka don tsaida kuduri da ma sauran matakai. Dukkan matakan yin zaben, sun nuna kyautatuwar tsarin jam’iyya da na gwamnati na zaben shugabanni, da imani da hangen nesa da jam’iyyar ke da shi.
Bisa ra’ayoyi da shawarwari daga sassa daban-daban, babban sakatare Xi Jinping ya yi musayar ra’ayoyi da shawarwari a kai a kai da sauran mambobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS kan manufofi da tsare-tsare na kafa sabuwar hukumar shugabancin sabon kwamitin kolin. Bayan tsara kwarya-kwaryar shirin, babban sakatare Xi Jinping ya sake sauraron ra’ayoyin mambobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa, da mambobin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, da sakatarorin sakatariyar kwamitin kolin JKS. A kan haka ne aka gabatar da shirin sabbin mambobin shugabannin kwamitin kolin JKS.
Hukumar ladabtarwa da hukumar kula da harkokin jami’ai na kwamitin kolin JKS ne suka gabatar da shirin ’yan takara mambobin sabuwar hukumar ladabtarwa ga kwamitin kolin jam’iyyar JKS ta hanyar neman ra’ayoyi daga bangarori daban daban. Sannan, hukumar soja ta kwamitin kolin JKS ce ta shirya tarukan tattaunawa ta tabbatar da takardar dake kunshe da ’yan takarar mambobin sabuwar hukumar soja da za a kafa, sannan ta gabatar da wannan takarda ga kwamitin kolin JKS domin neman amincewa.
A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 2022, zaunannen kwamitin hukumar ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya kira taro, don tattauna jerin sunayen sabbin mambobin hukumomin shugabanci na sabon kwamitin kolin JKS. A ranar 29 ga watan Satumba, an zartas da kuma amincewa da su a yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS.
A ranar 22 ga watan Oktoba, wadannan sabbin mambobin sabon kwamitin kolin JKS da na kwamitin ladabtarwa dake karkashin jagorancin kwamitin kolin JKS da aka zaba, sun samu amincewar wakilan da suka halarci babban taron wakilan jam’iyyar karo na 20.
Sannan a ranar 23 ga watan Oktoba, an zabi da kuma amincewa da sabbin mambobin hukumar siyasa da mambobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa a yayin cikakken zama karo na farko na kwamitin kolin JKS karo na 20.
Mambobin sabbin hukumomin shugabancin kwamitin kolin JKS dukkansu suna da kwarewa wajen ciyar da aikin zamanantar da kasar Sin gaba, kuma suna da jajircewa wajen sauke nauyin dake wuyansu. Bugu da kari, sun samu amincewa sosai daga wajen jami’ai a matakai daban daban da jama’a fararen hula.
Da karfe 12 na ranar 23 ga Oktoba na shekarar 2022, a babban dakin taron jama’a, Xi Jinping, wanda aka sake zaben sa a matsayin babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sauran mambobin sabon zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin, sun gana da ‘yan jaridun kasar Sin da na ketare wadanda suka ba da rahotannin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20.
Daga bisani, babban sakatare Xi Jinping ya kewaya zauren taron, a madadin sabbin shugabanin kwamitin kolin jam’iyyar, inda ya yi nuni da cewa, yayin da aka doshi sabon tafarki, dole ne a ko da yaushe a ci gaba da sanya jama’a a gaban kome, da kuma dogaro da jama’a. Kuma dole ne a yi aiki tukuru, da sa kaimi ga juyin-juya-hali kan jam’iyyar, da yada dabi’un gama gari na daukacin bil-Adama.
Wannan shi ne imanin da jagoran kasar ke da shi a sabon zamani, da nauyin da ke bisa wuyansa a sabon tafarki, da yadda zai jagoranci jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda aka kafa ta yau shekaru sama da 100 da suka gabata wajen kara samun nasara, da farfadowar al’ummun kasar baki daya.