A makon jiya ne aka yi wa Alhaji Shehu ‘Yarmusa (Garkuwan Legas) nadin bazata na Garkuwan Jihohin Yammacin Nijeriya, wannan ya faru ne yayin da Alhaji Shehu da mutanesa suka kai wa Sarkin Sasa Ibadan, Alhaji Haruna Mai Yasin ziyarar ta’aziyya a fadarsa sakamakon rasuwar matarsa.
Inda bayan da ya lura da yawan jama’ar da ke tare da shi ya sai Sarkin ya yi tambaye cewa, wadannan mutanen nan dukka tare da wa suke aka ce masa tare da ni suke, sai ya ce, to lallai za a yi nadi, na ce ai hakan nan muka zo, ba mu zo da komai ba sai ya ce, ai nine komai”,
- Rikicin Masarautar Kano: Sarki Bayero Ya Fara Bayyana A Bainar Jama’a A Kano
- Masarautar Gwandu Ta Farfaɗo Da Hawan Doki Na Shekara-Shekara
To hakan nan ya umarci a kawo kujera ya cire rawani a wuyarnsa ya sa aka nada min Sarautar Garkuwuwan Yammacin Nijeriya. “Wannan daga Allah ne, na tashi daga Garkuwan Legas zuwa Garkuwan Jihohin Yammacin Nijeriya”.
“Daga nan ya shiga gida ya dauko mani cikakken kayan sarauta (Riga Da Wanndo da Jampa da Rawani), wannan karamci ya sa mutane da mada kuka, har ni da kai a na yi kuka saboda murnar wannan karimci da daukakar da Sarkin Sasa ya yi mani” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, “Ina mika godiya ga dukkan al’ummar da muke tare da goyon baya da gudummwar da suke bani, ina kuma mika godiya ga marigayi Sarki Dogara a kan ada ni a matsayin garkuwan Legas da ya yi min a lokuttan baya.”
A nan gaba dai za a sanar da rana da lokacin da za a yi cikakken bikin nadin wannan sarautar.