Gwambawa a karkashin Kungiyar Tsofaffin Daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ‘yan ajin 1984 da kuma Kungiyar ‘Yan Ajin Digiri na Biyu a Fannin Nazarin Harkokin Kasashen Waje da Difilomasiyya (MIAD) da suka kamala a 2008, sun shirya wa ACG James Sunday kwarya-kwaryan bikin taya murnar samun karin girman a Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS).
James Sunday ya samu Karin girma daga Kwanturola na Jiha zuwa mukamin Mataimakin Kwanturola Janar (ACG)
An gudanar da kwarya-kwaryar taron bikin ne a harabar makarantar sakandaren ta kimiyya da ke Gombe a farkon makon nan.
Daruruwan mutane da ‘yan’uwa da abokan arziki da suka halarta, sun yi ta fatan alheri ga babban jami’in tare da addu’ar samun nasara a sabon mukamin nasa.
Da yake Karin bayani ga wakilinmu, ACG James Sunday ya yi godiya ga wadanda suka shirya bikin wanda ya ce saboda kauna ce tsantsa suka yi masa haka, kana ya gode wa Kwanturola Janar ta NIS, CGI Caroline Wura-Ola Adepoju da Ministan Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa tabbatar musu da Karin girma kana ya nanata kudirinsa na ci gaba da aiki tukuru domin sauke nauyin da tsarin mulkin kasa ya dora musu.
- Buhari Zai Halarci Taron Tattaunawa Da Kungiyar Tuntuba Ta Katsina
- Tinubu Ga Gwamnoni: Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya
ACG James Sunday wanda ya kammala makarantar sakandaren ta Gombe kuma daga bisani ya halarci Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Gombe inda ya kammala tare da samun lambar yabo a matsayin dalibi mafi kwazo a shekarar 1987, har ila yau ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna tare da nazartar Ilimin Fasahar Masana’antu.
Ya fara aiki da Hukumar Shige da AFice ta Kasa a 1989 inda ya halarci makarantar horaswa ta jami’an hukumar da ke Kano tare da kammalawa da samun lambobin yabo da suka hada ta minista da kuma ta darakta wanda ake bai wa jami’I mafi kwazo.
Shi ne ya zama jami’in hulda da jama’a na farko (PRO) a NIS da ya fara rike matsayin daga matakin babban ofishin jiha a Jihar Ribas, sai kuma ya zama na ofishin babbar shiyya ta Zone B mai shalkwata a Kaduna daga bisani kuma ya zama Babban Jami’in Hulda da Jama’ar ta NIS baki daya a shalkwatarta da ke Abuja
Shi ne ya fara zama jami’in sashen aikin hadin gwiwa a tsakanin Rundunar ‘Yansandan Duniya da NIS wanda sashen ne ya samar da hanyoyin da hukumomin biyu suka kafa sashen sadarwa a shalkwatar ‘yansanda ta kasa daga bisani aka yi nasarar kaddamar da manhajar rundunar ‘yansandan duniya da ke aiki dare da rana kullum. Wannan ya taimaka gaya wajen hadin gwiwar aiki a tsakanin Nijeriya da ‘yansandan duniya musamman a tsakanin hukumomin tsaro da NIS ke jagorantarsu a wannan fannin.
Bugu da kari, ACG James Sunday, ya zama jami’i na farko da aka nada mai bai wa ministan cikin gida shawara a kan harkar tsaro a lokacin da ake tsananin bukatar basirar wani kwararre ta fuskar tattara bayanan sirri domin magance fashe-fashen gidajen yari da kuma yin gyaran fuska ga ayyukan gidajen yari. Ya yi wannan aikin ne a matsayin jami’in da aka ba da aron sa.
Yanzu haka, ACG James Sunday, shi ne babban jami’i shalkwatar NIS ta shiyyar Zone C mai kula da arewa maso gabas da ta kunshi Jihohin Adamawa, Bauhci, Borno, Gombe, Filato da kuma Yobe,
ACG James Sunday jami’i ne da ya yi shuhura a fannin aikin yada labarai da sadarwa wanda ake matukar girmamawa a gamayyar hukumomin tsaro ta FOSSRA da ta kunshi daukacin jami’an hulda da jama’a. Har ila yau, marubuci ne da ya wallafa littafai, da Makalu, kana yana da sha’awar wasan kwallon dawaki da na golf, sannan mutum ne mai son Ubangiji, magidanci da yake da aure da kuma ‘ya`ya masu albarka.