A ranar Asabar da ta gabata ce, Sarkin Doma, Alhaji Ahmadu Aliyu Oga Onawo ya yi bikin cika shekaru 20 bisa karagar Sarautar Doma a Jihar Nasarawa.
Taron shi ne karo na farko a tarihin Masarautar Doma, wanda manyan baki daga sassa daban-daban a fadin kasan nan suka samu hakarta. An gudanar da taron a filin makarantar firamare da ke cikin garin Doma.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Xi Ya Taya Tebboune Murnar Sake Zama Shugaban Algeria
Manyan sarakuna da suka hada da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar da Etso Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, shugaban majalisan sarakunan Jihar Taraba Aku-Uka na Wukari, Dakta Manu Ishiyaku Ada Ali da kuma manyan sarakuna da dama daga Arewa da Kudancin Nijeriya sun halarci garin Doma domin taya murna ga Sarkin Doma.
Dukkan Sarakuna Jihar Nasarawa karkashin jagorancin shugaban majalisan sarakuna jihar, Mai Shari’a Sidi Bage Muhammad Sarkin Lafia su ma sun kasance a wannan wuri. Taron ya samu halartan jami’an gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi.
An gudanar da kade-kade da raye-raye na al’adun gargajiya na kabilun Kwararafa a wurin taron, makada da mawaka na gargajiya da makadan fada daban-daban sun nishadantar a filin taron.
Dukkan Kabun da ke zaune a garin Doma cikin ado da kwalliya suka halarci wajen taron. Mahaya dawakai ba a barsu a bayaba. Kade-kade da raye-raye sai wanda idanunka ya kai ko kunne ya jiyo maka.
Masu jawabi sun bayyana Sarkin Doma, Alhaji Ahmadu Aliyu Oga Onawo a matsayin Sarkin da ya cancanta a yaba masa wajen tabbatar da zaman lafiyan al’umman Doma. Sun bayyana cewa kafin hawansa kujerar Sarautar Doma, akwai rashin jituwa tsakanin al’ummomi da ke rayuwa a yankin Doma, amma tun da ya zama Sarkin Doma babu dare babu rana sai da ya tabbatar ya hada kan dukkan kabilun da ba su jituwa da juna, wanda ya samar da zaman lafiya da kaunar juna tsakanin manoma da makiyaya.
A cewarsu, ya hada kan dukkan kabilun suna mu’amala tare har ma da auratayya, wanda babu bambanci na rikicin addini a tsakanin kauye ka za da kauye kaza.
Lallai Sarkin Doma ya samu kyakyawar shaida daga ‘yan’uwansa sarakuna na Jihar Nasarawa da ma Nijeriya gaba daya. Sannan kuma ya samu kyakyawar shaida daga Gwamnatin Jihar Nasarawa da ‘yan majalisar dokokin jihar.
Malam Muhammad Ogoshi ya ce Sarkin Doma yana burgeshi, saboda baya raina duk mutimin da ya zo wajenshi. Ya ce duk abin da ya faru a gari ko kauye idan ya samu labari zai je wajen.
Itan Hasana Abubakar ta yaba da yadda sarkin ya kawo ci gaba a garin na Doma.
Sadiya Ogoshi ta ce zaman lafiyan Doma ya tabbata ne ta dalilin hadin kai da sarkin ya kawo. Ta ce yanzu baki daga Arewa sun shiga Doma suna gina gidaje suna aure suna aurar da yaransu a Doma.
Rubkat Emmanuel ta ce, “Mu a Doma sai dai mu gode wa Allah, saboda sarkinmu ya yi wa mutanin Doma komai.”
Ta roki Sarkin Doma da ya shawarci gwamnati ta kawo banki, domin garin Doma yana samun ‘yan kasuwa masu sayan agushi da ridi da sauransu.