An yi bikin makon tunawa da ranar cutar tabin hankali a brnin Landan a ranar 18 ga watan Mayu na shekarar 2023, kuingiya mai zaman kanta, Annomo Health, tare da hadin gwiwar Lobeday & Co, sun gabatar da wani taro wanda ya yi bayanai kan ganowa da maganin cutar tabin hankali inda masana daga sassa daban- daban suka yi bayanai game da cutar.
Taron na ilmantarwa ne da aka yi a aondan tare da zimmar bayanan da aka yi kan yadda cutar take, inda masana suka yi musayar ra’ayi kan cutar da samar da hanyoyin da za a kula da taimakawa masu fama da ita.
- Gwamna Dikko Ya Amince Da Bude Asusun Bai-daya A Jihar Katsina
- Rikicin APC: Kujerar Abdullahi Adamu Tana-kasa-tana-dabo
Duk da yake dai ana yi wa cutar kallon ba wata abar da wasu suka faye maida hankalin su kanta ba, cutar tabin hankali wani hali ne da ake shiga sanadiyar samun matsala na akalla wurare biyu kamar wasu abubuwa na mutum su daina aiki kamar ba a iya tunawa da wani abu ko rasa yin abinda mai hankali zai yi kan wani al’amari. Wadanda su kayi bayanai a taron sun hada da Dakta Arshad Rather da kuma Dakta Conor Clerkin-Oliber.
Dakta Rather shahararre kwararren likita ne (geriatrician) Likitan da ya kware kan kulawa da rashin lafiyar tsofaffi a Asibitin Landan da ya yi shekaru masu yawa yana kulawa da magungunan rashin lafiyar tsofaffi, ya yi bayanai masu amfani kan mafita a matsalar tabin hankali a bayyane da mai shafar hankali da mutane daban-daban suke fuskanta masu fama da cutar tabin hankali.
Ya yi bayanai na mafita kan magungunan da suka shafi cutar sai ci gaban da aka samu da ba dadewa aka yi ba wajen hanyoyin da za a iya amfani wajen maganin.
Hakanan ma akwai Dakta Conor Clerkin-Oliber Likitan da ya yi nazarin magani ne domin ya kware musamman kan magungunan da suka sha bamban da yin tiyata, mai bincike kan cutar Tabin hankali shi ma ya yi bayani akan sabbin magunguna kulawa da cutar tabin hankali.
Dukkan kwararru ta bangaren kula da lafiya sun yi bayanai ne kan ci gaban da aka samu sanadiyar bincike- binciken da aka gudanar, taimakon da aka samar da kuma magani.
Da take na ta jawabin wurin taron babban jami’i na kungiyar kula da lafiya ta Annomo Health, Dakta Chichi Menakaya wadda ita ce mai masaukin baki a taron ya ce Annomo Health da Lobeday sun shirya taron ne a matsayin wani taimakon da suke son badawa a sahu- sahun bayanai bi da bi dangane da matakai na tsufa da niyar ilmantar da al’umma domin su san al’amarin cutar tabin hankali ba wani abin tashin hankali ba ne.
Maudu’an da aka yi magana kansu kamar yadda Dakta Menakaya ta ce sun hada da,yadda za a gano cutar da wuri, da maganinta, yadda za a fuskance ta da hanyoyin da za abi na inganta rayuwar wadanda suke fama da cutar tabin hankali.
Sauran maudu’an sun hada da irin gudunmawa ta musamman da kayan da za a yi amfani da su wajen kulawa da cutar, da yadda za a taimaka wa wadanda suke taimaka wa marasa lafiya da iyalansu a gaba dayan lokacin da za a yi cikin cutar tabin hankali.