Yanzu dai a Kano babu batu mai daukar hankali da ya wuce batun rusau ba, magana ce mai saukin fahimta amma siyasa da son zuciya ya sa ana ta tababa da raba hankalin mutane akan ta.
Ba’a bukatar dogon zance domin gaskiya a bayyane take, gine-gine da aka yi su a daidai suna kan daidai, wadanda kuma aka gina su ba bisa ka’ida ba suna nan ba bisa ka’ida ba, domin gaskiya gaskiya ce koda babu mai binta, karya kuma karya ce koda kuwa kowa ita yake yi.
Babu mai hankalin da zai yi farin ciki da asarar wani don haka ake jajantawa wadanda suka yi asara, amma dai gwamnati na da iko ta yi amfani da masalahar al’umma koda wasu za su yi asara a sakamakon hakan.
Idan za’a iya tunawa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sa an rushe wani katafaren gini da aka fara a jikin gidan Kadiriyya dake Unguwar Kabara, kuma cikin dare Hukumar KAROTA ta je ta bada tsaro aka baje wannan gini bisa cewar an yi shi ba bisa ka’ida ba, masu ginin sun ce sun cika duk wata ka’ida da ta dace wajen ginin, amma kuma Karfin Gwamnati da watakila masalahar al’umma ya sa ginin ya zama tarihi.
Haka kuma an samu irin wannan matsala a cikin kasuwar kantin Kwari an ga gwamna na wancan lokacin yana bayar da umarnin “akai wannan ginin kasa idan wani ya zo zai yi zanga-zanga shima a kai shi kasa” shima masu ginin sun ce sun cika sharuda da ka’idoji wajen yin ginin.
Don haka dole a duba dalilan da gwamnati ta bayar na rushe wadannan gine gine musamman a yi la’akari da uzirin wuraren ibada, makarantu da sauran su,
Wannan ta sa ko a ranar da Gwamna Abba Kabir ya karbi rantsuwar kama aiki an ji ire-iren kalaman jagoran Kwankwasiyya shima daga bakinsa, wanda tun a lokacin cikin wasu masu irin wadannan kadarori ya duri ruwa.
Domin irin wannan rusau jama’a sun shaida shi a lokacin da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya karbi mulki daga hannun Sanata Malam Ibrahim Shekarau a 2011, inda a ranar da kungiyar ‘yan kasuwa suka je masa ziyarar taya murna, kuma aka ji matasan ‘yan kasuwa na ihun “filin Kofar Na’isa” wanda a wannan rana cikin dare Kwankwaso ya dirar wa wannan fili ya rushe shi baki daya, wanda cikin wadanda suka mallaki fili a wannan wuri har da manyan ‘yan kasuwar Kano irinsu Alhaji Aminu Dantata.
Saboda haka fara aiwatar da wannan aikin rusau da Gwamna Abba ke yi a halin yanzu ba wani sabon lamari bane, domin daman dai sun alkawarta rushe dukkan ire-iren wadannan wurare.
Da yawa na kallon wannan aiki a matsayi ramuwar gayya da rashin tausaya wa ‘yan Kasuwa, domin kamar yadda bincike ya tabbatar da cewa kaso 85 na wadanda aka rushe wadannan wurare duk haya suke ba su ne ainihin masu wuraren ba, wannan ta sa jama’a ke kallon aikin a matsayin ramuwar gayya, a cewar wasu masu fashin baki, kamata ya yi kafin daukar wannan mataki a bai wa masu kasuwanci a wadanann gine-gine wa’adin kwashe kayansu, amma dai hakan ba ta samu ba, sai ma yadda gwamnatin ke zuwa cikin dare su afkawa wadannan gine-gine.
Abu na biyu kuma da ya sa wasu ke shakkun ingancin wannan aikin rusau shi ne yadda gwamnatin a matakin farko ba ta dauki matakin kare dukiyar wadanda wannan lamari bai shafe su ba, kasancewar gwamnatin na ganin yadda wasu matasa dauke da kayan aiki ke afka wa rumfunan mutane suna fasawa tare da kwashe masu kaya, domin an ga haka a tsohon ginin Triump wanda ba ma a rushe shin aka je ba, amma matatsa suka afkawa wurin tare wasoson duk wani abu da suka yi ido hudu da shi.
Ire-iren wadannan gine-gine dake cikin jadawalin wuraren da gwamnatin ta ayyana rushewa ko take kan aikin rushewa, wurare ne da gwamnatin ke zargin tsohuwar gwamnati ta rabawa ‘yan lelenta da masu kwalli a ido, wanda suka hada da filayen da aka raba a filin Idi, kasuwanni, masallatai, makarantu, makabartu, asibitoci da gine-ginen dake Badalar da ta zagaye birnin na Dabo, kuma zuwa yanzu an ga saukar jirgin rusau din tuni ya isa tsohon ginin Otal din Daula, Filin Sukuwa, Filin Idi, da kuma wadanda yanzu ke kan layin gamuwa da irin wannan fushi na Gwamnati.
Matar rusau din a daren Juma’a wayewar garin Asabar tawagar masu rusau din suka dira rukunin gidajen da gwamntain Abba Kabir ke zargin Gwamnatin Ganduje ta raba wa filayen makarantar ‘School of Management’ wanda kuma tun cikin makon da ake bankwana da shi aka hangi hukumar tsara muhalli ta Jihar Kano ta shafa wa wasu gidaje jan fanti, wanda hakan ke nuni da cewa kowane lokaci gwamnati za ta iya sauka da jirgin rusau dinta, hakan ne kuma ya faru a wannan dare na Juma’a inda aka dirarwa wadannan gidajen, ganin irn yadda ake ruguje masu gidaje wasu magidanta suka zabi yin shahadar fito na fito da masu aiki, duk kasancewar akwai dandazon jami’an tsaro, hakan dai bai hana aiwatar da wani bangare na aikin ruguzau din ba.
Na tattauna da wasu daga cikin wadanda suka yi fito-na-fito da ma’aikatan rusau din, ga kuma irion furucinsu.
Wani magidancin cikin mazauna gidajen da Gwamnatin Abba Kabir ta dirarwa a gidajen dake Makarantar Management kan titin zuwa Jami’ar Bayero, ya bayyana yadda cikin dare aka dirarwa gidajensu da rushewa, ya ce “MatataTana da tsohon ciki ni kuma ga shi an fasa min kai, ba abin da za mu ce sai Allah ya isa.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a cikin daren da lamarin ya faru, Alhaji Aliyu Abubakar ya bayyana cewa tun da fari an zo an shafa wa gidajen nasu jan fanti, wanda hakan ta sa muka je hukumar muka same su, amma suka fada mana cewar umarnin ne daga sama, mun kuma nuna masu dukkan tàkardunmu na cika ka’idojin mallaka wanda kuma daga wannan hukumar suka fito, amma suka ce sai dai mu je mu ci gaba da addu’a,” in ji shi.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana dalilan gwamnati na rushe ire-iren wadanan wurare, musamman shataletalen dake kofar shiga fadar Gwamnatin Jihar Kano wanda Gwamnatin Abban ta rushe, kamar yadda aka sani an gina wannan shatale tale ne a bikin cikar Jihar Kano shekara 50 da zama jiha.
Da yake mayar da martani kan koke-koken jama’a kan wannan lamari ta bakin daraktan yada labaran gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa cewa ya yi, aikin wannan shatale-talen ba shida inganci kuma zai iya faduwa da kansa a shekara guda.
Da yake yi wa manema labarai karin haske kan wannan lamari na rushe-rushe a ranar Larabar da ta gabata, Sakataren Gwamnatian JIhar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya ce, shatale-talen na dauke dagin Kiristoci ne, wanda a cewarsa wannan ba karamin cin zarafin Addinin Islama bane.
Bichi ya kara da cewa, wannan ginin na shatale-talen na kawo cikas ga direbobi ta hanyar hana su hango abin da ke gabansu. “Shatale-talen na hana hangen gaba ga masu ababan hawa, sannan abu na biyu kuma idan ka yi amfani da na’urar daukar hoto za ka hangi dagin Kirista akan ginin shatale-talen.
“Kasancewar kaso 99.9 na jama’ar Kano duk Musulmi ne. Saboda haka ba daidai bane yin amfani da alamun dagin Kiristoci akan irin wurin, hakan rage kimar Musulunci ne.”
Sakataren Gwamnatin ya ci gaba da cewa, “Malamanmu sun shaida mana cewa, duk lokacin da Annabi Muhammad (SAW) ya ga wani abu komai kankantarsa dauke da alamun Cross a kansa, yana tabbatar da cewa an lalata wannan abu.
“Kuma abin mamaki duk wasu hotuna da aka dauka a Kano, sai ga irin wadannan alamun Cross, ko da kuwa sabuwar Gadar Muhammadu Buhari dake Hotoro na ga irin wannan dagin na Kiristoci, don haka ina tabbatar maku da cewa shirye-shirye sun kammala na cire duk inda aka hangi irin wannan dagin kiristoci.
Da yake karin haske kan rushe rushen da gwamnati ke ci gaba da shi a halin yanzu a wasu sassan kwaryar Birnin Kano, Dakta Bichi ya ce dukkannin wuraren da ake rushewa an gudanar da su ba bisa ka’ida ba wanda wasu jami’an tsohuwar gwamanti suka yi watandar su.
Ya kuma jadadda cewar gwamnati za ta biya diyya ne ga wadanda ke da ingantattun shaidar takardu mallaka.” Duk wanda ke kokarin mallakawa kansa wuraren amfanin al’umma irin Asibitoci, Makarantu da filin Idi babu shakka ba shida lafiya kuma ya kamata ya je ya ga likita.”
“Idan wani ya wawashe filayen gwamnati kuma gwamnati ta kwace abinta, babu yadda za ka bukaci a biya ka diyya.
Dukkanin wdancan gine-gine da muke rushewa an yi su ba bisa ka’ida ba kuma aka rabar da su a tsakanin jami’an tsohuwar gwamnati.
Saboda haka duk wanda ke neman diyya sai ya gaggauta saduwa da wanda ya sayar masa da kayan, domin kudaden cinikayyar wadannan wurare ba aljihun gwamanti aka saka su ba.
Dakta Bichi ya ci gaba da cewa, “Idan gwamnati ta kwace kayanka domin gina wasu wuraren bukatar al’umma, ya zama wajibi gwamnati ta biya wannan mutum diyya, amma babu irin wannan mataki a irin wadanan da ake magana a kansu a halin yanzu.
A karshe sakataren gwamnatin Jihar Kano ya bayyana cewa babu shakka wannan gwamnati za ta ci gaba da kwato kadarorin gwamnati da aka cefanar a wajen Jihar ta Kano.
Yanzu haka dai akwai sauran wurare masu yawa dake dakon isorwar jirgin na rusau kansu, wadanda suka hada da gine-ginen gidajen sayar da man fetur dake zagayen Badala dake kan titin zuwa Jami’ar Bayero, wuraren sayar da motoci da sauran wuraren da ake gudanar da harkokin kasuwanci duk dai a kan wannan titin na zuwa Jami’ar Bayero, haka kuma akwai wasu wuraren da a halin yanzu aka shafa masu jan fanti dake alamta cewar nan ba da jimawa ba rusau din zai iya karasowa kansu, da kamar wasu gine-gine a kasuwar sayar wayoyin hannu da sauransu.
Shima wani likita dake aiki a kasar Faransa ya roki Gwamnatin Jihar Kano da ta yi masa adalci kar ta rushe masa gidan da ya gina a unguwar Salanta, likitan ya bayyana haka cikin wata takarda da ya rubutawa Gwamnatin Jihar Kano inda ya bayyana cewa ya kashe makudan kudade wajen ginin gidan, sannan kuma ya cika duk wasu ka’idojin mallaka tare da samun izinin ginin gidan daga bangaren gwamnati.
Suma Kamfanin dake aikin ginin Otal din Daula tuni ya himmatu domin garzawa gaban kotu don kalubalantar matakin Gwamnatin Kano na rushe ginin da suka shiga yarjejeniya sahihiya da Gwamnatin Jihar Kano, hakan ta sa kamfanin ke neman diyyar Naira Biliyon 10 a matsayin diyyar ta’adin da aka yi masu na rushe wannan gini da suke.
Bahaushe dai na cewa ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare, zuwa yanzu ita dai gwamnati na kara jan damara tare da jadadda aniyarta na ci gaba da aiwatar da wannan aiki wanda ta ce tana yin sa ne domin dawo da kimar Jihar Kano, sannan kuma a kwato kadarorin gwamnati da wasu shafaffu da mai su ka yi watandar su a tsakaninsu.
Yayin da su kuma jama’a musamman wadanda wannan rushe rushe ya shafa ke kara yin tagumi tare da neman daukin Allah bisa wannan hali da suka tsinci kai a cikinsa.
Wani dogon rahoto da Jaridar THE NATION ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ya ce, hankalin Jama’a da dama mazauna yankin unguwar Salanta da ke cikin birnin Kano ya tashi, yayin da mazauna unguwar suka yi tir da matakin da gwamnatin jihar ta dauka a yankin na ci gaba da rusa wasu gine-gine da ake zargin sun saba wa doka.
Wuraren da gwamnatin Kanon mai ci ta rushe sun hada da wani gini mai hawa uku mai dauke da shaguna sama da 90 a filin wasan tsere, Nasarawa GRA, wanda kudinsa ya haura Naira biliyan 100 da kuma Otal din Daula mai daki 90 da ya lakume zunzurutun kudi har sama da Naira biliyan 10.
Mutane da dama ne suka rasa wuraren sana’o’insu saboda rugujewar da aka yi kuma ana ci gaba da ruguje wasu gine-gine domin yin takunkumi ga abin da gwamnati ta kira mamaye filayen jama’a.
A jiya ne gwamnati ta tabbatar da mutuwar mutum biyu da ta bayyana a matsayin masu kwasar kaya bayan rugujewar.
Gwamnatin ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu, amma ta gargadi Jama’a da su nisanci gine-ginen da aka ruguje, inda ta yi gargadin cewa kusantar wuraren yana hatsari ga lafiyar Dan’adam.