Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Ogbeni Aregbesola ya bayyana cewa ba ƙaramin dace aka yi ba da aka samu Isah Idris Jere a matsayin muƙaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS).
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba jim kaɗan bayan ya yi wa muƙaddashin Kwanturola Janar ɗin ado da sabon muƙaminsa a ɗakin taro na Hukumar Gudanarwar Rundunonin Ma’aikatar Cikin Gida (CDCFIB), da ke Unguwar Area 1 a Abuja.
Aregbesola wanda ya maƙala muƙamin tare da taimakon wani na hannun daman Isah Idris Jere, Alhaji Ibrahim Usman Yakasai, ya bayyana cewa suna da tabbacin zaɓin da Shugaba Buhari ya yi masa a matsayin wanda zai jagoranci hukumar ta NIS, zai amfanar da ƙasa da ‘yan ƙasa bisa la’akari da ƙwazonsa na aiki.
“Tabbas Isah Jere ya cancanci wannan matsayi, mutum ne mai ƙwazo. Godiya ga Shugaba Buhari da ya amince a naɗa shi a matsayin muƙaddashin CGI, daga yanzu kar wani ya ƙara ce masa DCG, ya zama cikakken Kwanturola Janar, duk da cewa za a riƙa kiran sa a matsayin muƙaddashi.
“Jere yana magana da harsuna daban-daban, idan yana magana da yarabanci sai na ji mamaki. Haka harshen Ibo ba za ka ce ba harshensa na gado ba ne. Na kasa haƙuri, wata rana na tambaye shi, Jere ina ka koyi waɗannan harsunan, sai ya ce mun ya yi mu’amala da aiki a wurare mabanbanta na ƙasar nan. Shi ya sa nake ganin harsunan da ba ya ji na ƙabilun ƙasar nan kaɗan ne kawai.
“Haƙiƙa mun samu shugaba mai son aiki, mai ƙwazo, wannan abu lada ne da Allah ya ba ka a madadin ƙwazon da kake nunawa. Ina taya ka murna tare da iyalai da ‘yan’uwanka a kan wannan muƙami.” In ji shi.
Ministan ya kuma yi tsokaci a kan tsaikon da ake samu na Biza da Fasfo, inda ya ce, “Babu inda ba a samun ƙarancin fasfo a duk duniya. Na faɗa na kuma ƙara faɗa. Amma yanzu bisa abubuwan da aka sa a gaba, za a shawo kan komai. Kullum ina karanta ƙorafe-ƙorafen mutane a social media, amma nakan tambayi kaina, wai ma mene ne wanan? Sai na tuna cewa duk duniya ta na’ura ake neman fasfo. Dole sai an bi na’ura, don haka muka kawo tsarin da kowa zai iya nema a duk inda yake, daga nan za a ba shi lokacin da zai zo ya amsa. Kodayake ya danganta da yawan tururuwar jama’a a yankin da mutum yake nema. Misali, a Ikoyi, tururuwan jama’a da ake samu a can ya kai kusan kashi 50 na yawan tururuwar da ake samu a dukkan ofisoshin fasfo.
“Ina roƙon ‘Yan Nijeriya su ba mu goyon baya, su fallasa masu badaƙala a bayan fage. Mun yi alƙawarin cewa za mu ɗauki mataki na ba-sani-ba-sabo. Kuma yana da kyau mutane su fahimci cewa, bubuwan da ake yaɗawa galibinsu zuƙi ta malle ne. Kai, in da ma akwai wani abu da ya fi gaban a kira shi da ƙarya to shi suke yi.” Ya bayyana.
Tun da farko sai da, ɗaya daga cikin Kwamishina a Hukumar Gudanarwar, Mista Bassey ya gabatar da muƙaddashin CGI Isah Idris Jere a gaban ministan da sauran waɗanda suka halarci ƙwarya-ƙwaryan bikin, kafin a fara duk abubuwan da suka wakana.
Da take gabatar da taƙaitaccen tarihinsa, Sakatariyar Hukumar Gudanarwar, Hajiya Aisha, ta bayyana cewa an haife shi ne a garin Jere da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna a ranar 30 ga Disambar 1962. Ya yi karatunsa na Firamare a Makarantar LEA Jere, sannan ya tafi Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Katsina, kana daga bisani ya halarci Jami’ar Bayero da ke Kano inda ya yi digiri a fannin aikin jarida. Ya fara aiki da Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja daga bisani ya sauya ya koma Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa.
Ita ma da take tsokaci a kansa, Wakiliyar Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Cikin Gida, Misis Morimi, ta yaba da kyawawan halayensa, tana mai cewa “a kowane lokaci idan aka kira shi yana amsawa, duk lokacin da aka ce masa ga wata matsala ta taso nan da nan zai yi tsayin daka wajen magancewa. Mutum ne da ya yarda da kansa, yakan zo shi kaɗai cikin kayan gida, ba shi da tsoro game da tsaron kansa. A gaskiya mun ga sabuwar fuska a wannan matsayi da za ta zama mai albarka ga NIS,” in ji ta.
Da yake mayar da jawabi bayan ɗaura masa muƙamin, Muƙaddashin Kwanturola Janar Isah Idris Jere, ya yi godiya ga Allah Ta’ala da ya sahale masa wannan matsayin. Kana ya gode wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Minista Aregbesola da dukkan shugabannin gudanarwar hukumar waɗanda suka ba shi goyon baya tun daga lokacin da ya karɓi ragamar riƙon hukumar a bara.
Ya ƙara da cewa, “Burina shi ne na mayar da hankali wajen bunƙasa NIS ta iya gasa da kowacce irin ta a duniya. Manyan abubuwan da na fi mayar da hankali a kai su ne batun inganta tsaron iyakokin ƙasa ta hanyar amfani da na’urorin aiki na zamani, da ƙara inganta harkokin fasfo domin ɗorawa a kan nasarorin da aka samu da rage yawan cunkoso da kuma tabbatar da walwalar jami’ai.
Manya da ƙananan mataimakan muƙaddashin Kwanturola Janar Isah Idris Jere suka rufa masa baya zuwa Hukumar Gudanarwar Rundunonin na Ma’aikatar Cikin Gida domin ɗaura masa muƙamin nasa.
Idan ba a manta bad ai, a makon da ya gabata, CGI Isah Idris Jere ya yi wa manyan jami’ai 94 da suka samu ƙarin girma ado da sababbin muƙamansu a shalkwatar hukumar da ke Abuja, yayin da ragowar huɗun aka yi musu a Ma’aikatar Cikin Gida.
Jimillar sabbin waɗanda aka ƙara wa girma zuwa muƙamin ƙananan mataimakan Kwanturola Janar sun kai 24 da Kwanturololi 70 waɗanda duka aka yi musu ado da sabbin muƙaman nasu a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya samu halartar takwarorin NIS da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida da sauran manyan jagororin Hukumar Gudanarwa ta CDCFIB.
Daga cikin manyan jami’an da aka saka musu sabbin muƙaman nasu akwai DCG Oluremi Talabi, DCG Josephine Kwazu, DCG Modupe Anyalechi da kuma DCG Muhammad Aminu Muhammad.
Daga cikin ƙananan mataimakan Kwanturola Janar na NIS din kuma akwai ACG Kemi Nandap, babbar jami’ar da ke kula da shige da fice a Filin Jiragen Sama na Murtala Muhammad da ke Legas, da babban jami’in harkokin ofishin CGI da aka sauya kwanan nan, ACG Ahmad Bauchi Aliyu da kuma Kwanturola Mustapha Ahmad, mataimaki na musamman ga CGI a fannin gudanar da ayyuka.