Menene Google Drive?
Google Drive wata ma’ajiya ce da kamfanin google suka tanadarwa duk wanda ya mallaki account xin ‘Gmail’ kuma kyauta ne. G-drive ya kan ba da damar ajiya na kimanin wurin ajiya (storage space) 15GB kuma ya tsare maka shi, wato ya ba da tsaro (security) ingantacce. Ya kan iya adana bayanai iri-iri, kama daga rubutu (document), murya (audio), hotuna (pictures) da kuma bidiyo (video).
Yaya Google Drive Yake?
Mafi yawancin wayar hanu qirar (smartphones) tana zuwa da shi kuma kyauta yake a cikinta. Idan aka duba wayar da kyau cikin nutsuwa za a ga application xin me suna Drive kamar yadda yake a hoto.
Idan ba a samu ba, sai a sauke shi, wato a yi download daga google playstore, zai sauke shi cikin a wayarka. Sai a buxe shi, za a ga waxannan abubuwa;
Sune kamar haka:
1) Folder
2) Upload
3) Scan
4) Google Docs
4) Google Sheets
5) Google Slides
Yaya Ake Ajiya A Google Drive?
Yadda ake ajiya a google drive shi ne, da farko za ka buxe upload, nan take zai buxe maka local storage, wato abubuwan dake cikin wayarka (memory). Da zarar ya buxe, sai a zavi abin da ake so a ajiye xin. Page wanda yake xauke da abubuwan da aka ajiye a cikinsa zai bayyana.
Shikenan an yi ajiya a cikin google drive xin, duk lokacin da ake buqata sai a yi amfani da shi. Wani lokacin idan an ajiya (upload) sai ya nuna waiting for WiFi. To hakan yana faruwa ne musamman idan wannan ne lokaci na farko da mutum ya fara amfani da google drive xin.
A wasu lokutan kuma idan ana da matsalar network (data) ana fuskantar hakan. Idan aka yi upload, sai a ga yana nuna waiting for WiFi, to ga yadda za a yi masa.
A saman wayarka akwai wasu layuka guda 3 a kwance daga gefen hagu (option) kusa da Search in Drive, za a ga wani feji zai buxe sai a danna Settings. Zai qara buxe wa, to daga can qasa an rubuta ‘Data Usage’ a gefen rubutun akwai wani xigo shuxi (blue) sai a danna.
Shikenan wannan matsalar an yi maganinta.
Akwai abubuwa masu yawa waxanda google drive kan iya taimaka wa wajen yin amfani dasu. Google Drive yana ba da damar ajiyar kowane irin file kamar yadda na muka ambata a baya. Za a iya adana file komai girmansa idan bai wuce nauyin 15GB ba. Kadan daga cikin mahimman amfaninsa shi ne:
1) Upload: Yadda za a xora abu a kan google drive, kamar yadda na kawo misali a baya.
2) Scan: Goigle drive ya kan ba da damar yin scanning na takardu masu mahimmanci, kamar na karatu kuma a adana shi a cikin drive, kuma ya kan ba da damar yin amfani da su a duk lokacin da ake da buqatarsu. Kamar a wajen rijista ta yanar gizo, lokuta da dama a kan buqaci takardun kammala karatu ta hanyar tura wa a website na neman aiki ko scholarship da sauransu. Scan yana taimaka wa sosai wajen kiyayewa haxarin gobara, ruwa da abubuwa makamantansu da kan iya kawo lalacewar takardu ko vatansu. Idan kana da google drive babu kai ba yawo da takardu a hannu.
3) Folder: Folder tana taimaka wa wajen rarrabe files da aka adana.
4) Ana iya qara girman memory storage space daga 15GB zuwa 100GB, 150GB, 200GB zuwa sama da hakan amma wannan siya ake yi, wato (Drive Upgrade).
Za mu yi bayaninsa a nan gaba.