Ayau shafinmu na ra’ayi ya tattauna ne da Aliyu Suleiman inda ya ce, mai gidan shi Khamisu Mailantarki dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP baya shakkun fitowa takara da Gwamna mai mulki, ko kuma gwamnatin da ke kan mulki.
Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, domin a baya Mailantarki ya nuna cewa shi mutum ne mai jama’a. Su kuma jama’a su ne kasuwa, ba yawan rumfuna ba.
“A baya abu ne mai wahala a fito yin kokawar gaba-da-gaba da gwamna mai mulki a Jihar Gombe. Amma yanzu abu ne mai sauƙi, kuma idan mu ka yi gaba-da-gaba, mu ka haɗa ƙwanji a ranar zaɓe, to kayar da gwamna abu ne mai sauƙi a wuri na.” Inji Mailantarki, bayan an tsayar da shi takarar gwamna a ƙarƙashin NNPP.
Daga cikin laƙanin da Mailantarki ke taƙama da su, akwai jama’a, waɗanda su ne ya ce su ka roƙe shi ya fito takarar gwamna, domin su sake yi masa irin ruwa da ƙanƙarar yawan ƙuri’un da su ka taɓa yi masa a 2011. Wannan karon ma gaba ɗayan jihar ce, ba wai a ƙananan hukumomi 3 kamar na zaɓen 2011 ba.
Wani laƙanin da Mailantarki ya ce ya ke taƙama da shi, shi ne iƙirarin sa cewa gwamnatin APC ba ta tsinana wa Gwambawa abin a zo a gani har a yaba ba.
Ba wai girma ake buƙata ga wuƙar da za a feɗe giwa ba, a’a, mai kaifi ake nema komai ƙanƙantar ta.
Yayin da ake gwabza yaƙin neman zaɓen gwamnoni a faɗin jihohin Najeriya, zaɓen da zai kasance cikin sahun gaba wanda za a yi kallon kwatagwangwamar kokawa a Arewa, shi ne zaɓen gwamnan Jihar Gombe, wanda a cikin ‘yan takara har da Khamisu Mailantarki, wanda jam’iyyar NNPP ta tsayar takarar gwamna a Gombe.
Kada mai karatu ya yi shakku, tababa ko tantama cewa Mailantarki zai iya kayar da Gwamna Inuwa Yahaya a zaɓen 2023. Wanda bai san Mailantarki ba, shi ne zai tsaya ya na wasiwasin wannan nazari.
A zaɓen 2011, Mailantarki ya fito takarar Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa a Majalisar Tarayya a ƙarƙashin CPC, jam’iyya maras galihu a lokacin. Me ya faru, talakawa da masu halin Ƙananan Hukumomin Gombe/Kwami/Funakaye sun zuba masa ƙuri’un da babu wani Ɗan Majalisa da ya samu kusan yawan ta shi a 2011, kakaf ɗin su har su 360 a Najeriya.
Yayin da Mailantarki ya samu ƙuri’u *122,987*, abokin takarar sa na PDP kuwa ƙuri’a 44,206 ya samu. Shi kuma na ANPP ya tashi da ƙuri’un da ba su wuce a jefa cikin aljihun riga malum-malum ba, wato guda 8,760 kacal.
Fitar Mailantarki daga APC a cikin watan Mayu, 2022 ke da wuya, sai NNPP ta ba shi takarar gwamna.
Alamomin Mailantarki zai firgita manyan namun dajin siyasar Gombe na cikin gwamnati ta fara ne tun daga lokacin da NNPP ta ba shi takara babu hamayya. Wakilai 342 daga Ƙananan Hukumomi 11 duk su ka amince da shi, babu hamayya.
Sannan kuma shi da kan sa bayan ya lashe zaɓen fidda-gwanin da wakilai 342 ɗin zu ka zaɓe shi, ya ce, “a tarihin Jihar Gombe ba a taɓa yin zaɓen fidda-gwanin da ya kai na sa zama sahihi ba. Wannan ma alama ce mai nuni da cewa Mailantarki ya samu tagomashi a faɗin jihar kenan.
Ko ma dai me ke nan, ganin yadda guguwar Mailantarki ke kwashe manya da ƙananan ‘yan APC da PDP, su na watsi da laima da tsintsiya su na rungumar kwandon kayan marmari, hakan alama ce mai nuna cewa za a kwashi ‘yan kallo a ranar kokawar zaɓen 2023.
Tabbas Gwamna Inuwa Yahaya na da aiki a gaban sa. Kuma duk irin inuwar da Inuwa ya shiga da rana, to zai kasance cikin tunanin hasken Mailantarki. Duk cikin duhun da Inuwa Yahaya ya shiga da dare, sai ya yi tunanin hasken Mailantarki. Kai, ko cikin hasken lantarki ko hasken taurari da farin wata Inuwa Yahaya na APC ya shiga, zai ya riƙa tuna hasken Mailantarki.
Farin jinin Mailantarki zai iya sakar wa sauran ‘yan takara sukuntumau, ta yadda ko haske fitilar cocila su ka gani, su ce hasken lantarkin Mailantarki ne
Wataƙila ma ko a mafarki, ba zai rasa yin mafarkin hasken lantarkin Mailantarki ba.