Babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Di Jinping ya ziyarci dakin ibadar Three-Su dake birnin Meishan na lardin Sichuan dake kudu maso kudancin kasar a ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 2022, domin ganewa idonsa yanayin da birnin ke ciki, wajen kare kayayyakin tarihi, inda ya bayyana cewa, “Ana iya ganin rana daga digon ruwa, ana kuma iya ganin girman al’adun al’ummar kasar Sin daga dakin ibadar Three-Su, wanda ya shaida alfahari da al’adun kasar.”
Dakin ibadar Three-Su, tsohon gidan shahararrun marubuta uku na daular Song ta arewa wato tsakanin shekarar 960 zuwa ta 1127 a tarihin kasar Sin, wadanda suka hada Su Dun da ‘ya’yansa biyu Su Shi da Su Zhe.
- Shugabancin APC: NEC Za Ta Bayyana Matsayar Ganduje A Yau
- Kungiyoyin Magoya Bayan Kano Pillars Da Katsina United Sunyi Taro A Kano Domin Sulhunta Tsakanin Su
A ranar 2 ga watan Yunin bana, babban sakatare Di Jinping ya halarci taron tattauna yadda ake gada da raya al’adun kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda ya jaddada cewa, ci gaba da ingiza wadatar al’adu, da gina kasa mai karfi a bangaren al’adu da wayewar kan al’ummar kasar Sin ta zamani, sabon burin Sinawa ne a sabon zamani. Ya dace a kara tabbatar da alfahari da al’adu, a sauke nauyin da ya dace, a kuma yi kokari domin samar da sabbin al’adu a zamaninmu na yanzu, da gina wayewar kan al’ummar Sinawa a sabon zamani.
Alfahari da al’adu sakamakon fahimtarsu
An sauya tsohon gidan zuwa dakin ibada a zamanin daular Yuan wato tsakanin shekarar 1271 zuwa ta 1368, yakin da aka yi karshen daular Ming tsakanin shekarar 1368 zuwa ta 1644 ta haddasa rushewar dakin, daga baya an sake gina dakin ibadar a shekarar 1665 gwargwadon tsohuwar siffarsa a baya kuma a wurinsa na da.
Ruwa ya mamaye gefuna uku na dakin ibadar Three-Su mai dogon tarihi, daga “dakin tarya baki” zuwa “dakin yin addu’a”, kuma daga “dakin adana dan fallen katako domin tunanin kaka kakanni” zuwa “dakin kwana da karatu da ake kira Laifengduan”, ana iya yawo a cikin wannan dakin ibada, ana kallon abubuwan mamaki da fitattun hikimomin iyalai na Su.
Babban sakatare Di Jinping ya taba bayyana cewa, “Horon iyali, dukiya ce mai daraja da aka bai wa ‘yan baya. Don haka ya dace a mai da hankali kan aikin ba da horo da ilmi ga iyalai domin karfafa tunanin ‘yan baya na kishin iyali da kishin kasa, ta yadda za su taka rawar gani kan ci gaban kasa, gami da zaman takewar al’umma baki daya.”
Su Dun ya karanta litattafai da dama, bayan uwargidansa Cheng ta haifi ‘ya’ya biyu wato Su Shi da Su Zhe, sai suka koya musu ilmi daban daban, inda suka kasance zakaru a jarrabawar da aka shirya domin zaben jami’an gwamnati a zamanin daular Song ta arewa. Daga nan Su Dun da Su Shi da kuma Su Zhe su uku sun yi kokari matuka domin bauta wa al’ummun kasar yadda ya kamata.
Di Jinping ya jaddada yayin da yake rangadin aiki a dakin ibadar Three-Su cewa, ya zama wajibi ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da jami’an gwamnatin kasar, musamman ma manyan jami’ai su martaba ka’idojin da aka tsara, kuma su nuna himma da kwazo da tsimi da ma kaucewa cin hanci da rashawa, da zama masu da’a dake nunawa hali na kwarai irin na ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki.
Tun bayan da aka kammala babban taron wakilan JKS karo na 18 a shekarar 2012, Di Jinping ya kara ba da muhimmanci kan tunani da hikima dake cikin al’adun kasar Sin, kuma ya kan yi bayani kan tunaninsa na tafiyar da harkokin kasa da maganganun da magabata suka taba bayyanawa.
A cewarsa, “Nacewa kan alfahari da al’adu, amincewar kansa ne mai tushe da girma, kana karfi ne mai dorewa. Mun girma ne bisa wayewar kai ta kasar Sin, kamata ya yi daukacin ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da al’ummar Sinawa ‘yan kabilu daban daban, mu girmama al’adunmu, haka kuma mu tabbatar da tunanin alfahari da al’adunmu.”
Shugaban dakin adana kayayyakin tarihi na dakin ibadar Three-Su Chen Zhongwen ya yi tsokaci cewa, “Kalaman Di sun kara fahimtar da mu al’adun kasar Sin, wannan ya sa mun kara alfahari da al’adunmu.”
Tafiyar da harkokin kasa bisa alfahari da al’adu
Darektan ofishin nazarin al’adun Three-Su na birnin Meishan, wanda ya shafe shekaru 10 yana nazari kan horon iyalin Su Liu Kingkuan ya gaya mana cewa, irin wannan tunani na kishin iyali da kishin kasa da al’ummar Sinawa suke gadawa tun zamanin baya, yana cikin zukatu da biyayyarsu daga zuriya zuwa zuriya, a maimakon koyar da wasu ta baki kawai.
Yanzu ‘yan wasan fasaha matasa suna kokarin gadar da al’adu da suka koya, misali ‘yan wasan fasaha na gidan wasan kwaikwayon jama’ar lardin Sichuan wadanda suka haifa bayan shekarun 1980, inda suka kirkiro wasan kwaikwayo mai taken “Su Dongpo”, wato sunan Su Shi da aka fi sani, ta hanyoyi uku wadanda suka hada da wasan kwaikwayo a daki, da wurin yawon shakatawa, da kuma a dakin adana kayayyakin tarihi.
Wadda ta kirkiro wasan kwaikwayon Deng Ying ta bayyana cewa, “Yayin da muke samar da wasan kwaikwayo, ba ma kawai muna mai da hankali kan fasahar wasan ba, har ma muna ba da muhimmanci kan yadda za mu samar da wasan kwaikwayon da zai samu karbuwa daga masu kallo, sakamakon haka, al’adun gargajiya na al’ummar Sinawa sun samu ci gaba kamar kirkire-kirkire.”
Deng Ying ta kara da cewa, “Wasu ‘yan kallo sun kalli wasan kwaikwayon da ‘yan wasan fasaha na gidan wasan kwaikwayon jama’ar lardin Sichuan suka nuna a dakin wasa a wurare daban daban dake fadin kasar Sin sau takwas, hakika amincewarsu ga wasan kwaikwayon da muka samar ta karfafa gwiwarmu wajen alfahari da al’adun kasarmu.”
Mataimakin darektan wasan kwaikwaiyon “Su Dongpo” Tang Zhong shi ma ya yi tsokaci cewa, “Yayin da muke gada abubuwa masu inganci daga kaka da kakanninmu, mu kan yi farin ciki, wannan shi ne ma’anar alfahari da al’adu wanda daukacin Sinawa dake rayuwa a kasar mai fadin muraba’in kilomita miliyan 9 da dubu 600 suke yi.”
An lura cewa, Su Dongpo ya taba rubuta wata jimla cewar, “Inda zuciyata take shi ne garina.” Jimlar dake nuna soyayya mai zurfi da Sinawa ke nunawa garuruwan da aka haife su, da kishinsu ga iyalai da kuma kasarsu.
Al’adun Three-Su na ci gaba da taka rawa a sabon zamani
Shugaban makarantar firamare ta Dongpo dake birnin Meishan Du Ke ya gaya mana cewa, “A bangwayen makarantarmu, an rubuta wakokin da shahararren marubuci Su Dongpo ya rubuta, muna fatan daliban makarantarmu za su girma yadda ya kamata, kuma za su kasance mutane masu kirki, da farin ciki, da kwazo, da himma, da kuma masu ilmi.”
Mataimakin shugaban sashen yada manufofi na hukumar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta birnin Meishan kuma shugaban hukumar kula da al’adu da rediyo da talibijin da yawon shakatawa ta birnin Wang Feng shi ma ya bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, hukumomin da abin ya shafa na birnin Meishan sun dukufa kan aikin shigar da al’adun Dongpo cikin manhajan makarantu da unguwannin mazaunan birnin, inda ake koyar da kwasa kwasai iri daban daban. A cewarsa, muddin aka fahimci al’adun gargajiya, aka kuma yada su yadda ya kamata, to, za su ci gaba, tare kuma da samun karbuwa daga duk fannoni a fadin kasar ta Sin.
A nasa bangaren, shugaban dakin wasan kwaikwayon wake-wake da raye-raye na birnin Meishan Yuan Diao yana mai cewa, “Muna yin kokari domin fito da hanyoyin musaya da gadon hikima da tunanin magabata.” Inda aka samar da wasan kwaikwayon wake-wake da raye-raye mai taken “Dongpo” ta hanyar da ta hada fasahohin rubutun wakoki, da zane-zane, da rubutun kalmomi, da wake-wake da kide-kide, da wasan kwaikwayo na gargajiya da sauransu. Ana sa ran masu kallon wasan za su samu damar kashe kwarkwatar ido.
A bakin kofar dakin ibadar Three-Su, an dasa bishiyoyi uku, kuma yanzu haka sun zama manyan bishiyoyi, kamar manyan mutane uku wato Su Dun da Su Shi da kuma Su Zhe suna tsaye suna kallon juna domin waiwayen abubuwan da suka faru a baya, da kuma nuna fatan alherinsu ga zamani na gaba. Ko shakka babu al’adun Three-Su za su ci gaba da taka rawa a sabon zamani, kamar yadda babban sakatare Di Jinping ya bayyana, yayin taron tattauna yadda ake gado da raya al’adun kasar Sin cewa, “Ya dace a gudanar da kwaskwarima da kirkire-kirkire bisa tushen kare al’adun gargajiya masu inganci.” (Marubuciya: Jamila)