Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin namu zai koya muku yadda ake Dublan
Abubuwan da za ku tanada:
Fulawa, Sikari, Baikin Fauda, Gishiri, Mai, Lemon tsami, Bota:
Ga Yadda zaku hada:
Da farko za ku samu Tukunya sai ku zuba sukarin a ciki, ku dora shi a wuta ya narke ya yi zafi ya dan tafasa, sai ku kawo lemon tsami guda daya ku matse a ciki sai ku bar shi ya dan dahu sannan ku sauke.
Sai ku samu roba me dan girma, ku zuba fulawar a ciki sannan ku kawo Baikin Fauda ita ma ku zuba sai ku zuba dan Gishiri kadan ba da yawa ba sai ku zuba Bota idan kuma ba kuda Bota za ku iya zuba mai ku kwaba da shi, sai ku kwaba sosai ku juya shi ya juyu sosai, sannan ku samu abin murzawa ku yi ta buga shi, idan ya bugo sosai sai ku yayyankashi ku nada ku soya.
Idan kuka soya sai ku rika tsomawa a cikin sikarin da kuka dafa. Nadin Dublan kala-kala ne duk wanda kika yi ya yi idan kika kalli yadda yake.