A kwanan baya an gudanar da taron koli na duniya a kan intanet a garin Wuzhen na kasar Sin inda kwararru da masana har ma da manazarta suka taru domin waiwaye adon tafiya kan irin ci gaban da ake samu a bangaren intanet da kuma alkiblar da aka dosa.
A yayin gudanar da wannan taro, rahoton da Cibiyar Binciken Harkokin Intanet ta kasar Sin ta fitar na 2024 ya nuna har yanzu kasar Sin tana jan zarenta a matsayi na biyu wajen samun ci gaban intanet a duniya tare da maki 69.00. Bugu da kari, kasar ce a kan gaba wajen gabatar da bukatar neman ikon mallakar sabbin abubuwan da aka kera masu amfani da kirkirarriyar basira ta AI. Hukumar Kula da Ikon Mallakar Kayan Fasaha ta Duniya ta ce kasar ta shigar da bukatun neman hakkin mallaka fiye da 38,000 daga shekarar 2014 zuwa 2023.
- Kasar Sin Za Ta Samar Da Ababen Hawa 100,000 Don Aikin Taksi Da Na Amfanin Kai Nan Da Shekarar 2030
- Shehu Mahy Inyass Ya Sanar Da Sauye-sauye A Tafiyar Tijjaniya A Nijeriya
Bayan haka, kasar Sin ta kara himmar bunkasa fasahar sadarwa inda zuwa watan Yunin bana aka samu masu wayoyin salula miliyan 889 dake amfani da fasahar intanet mai karfin 5G da kasar ta kirkiro.
Zurfafa bincike da aiwatar da shi da kasar Sin ke ci gaba da yi a fannin kimiyya da fasaha yana haifar da da mai ido. Kasar ta nuna irin ci gaban da take samu a fannin fasahar zamani a yayin da ta yi amfani da tawagar sintiri na tsaro da babu dan Adam ko daya a ciki sai karnukan mutum-mutumi da jiragen ruwa da motoci marasa matuka masu amfani da kirkirarriyar basira, yayin gudanar da taron kolin intanet na duniya a garin Wuzhen.
Su wadannan karnuka na mutum-mutumi an sanya musu kaifin basira ta yadda suke iya daidaituwa da wurare mabambanta da kuma ko wane yanayi na aiki. Ko wane kare a cikinsu yana iya tafiyar tsawon mita uku zuwa shida a cikin dakika guda. Sannan ta hanyar kyamarar da aka makala masa yana iya tattara bayanan bidiyo na duk inda aka tura shi tare da aikawa a kan lokaci zuwa cibiyar karba da bayar da umarni. Hikimar hakan ita ce daukar mataki nan take da yin gargadi a kan duk wata barazana da ka iya tasowa.
Har ila yau kasar Sin ta kera wannan kare na mutum-mutumi ne ta yadda za a iya amfani da shi ta fuskar gudanar da aikace-aikace mabambanta. Hakan ya sa aka sanya masa lasifika don isar da sako ga wurin da aka tura shi, da na’urar kararrawa mai abin latsawa guda daya don ankararwa, da akwatin kiwon lafiya na wucin-gadi domin taimaka wa bayar da taimakon gaggawa, da sauran wasu ayyuka da suka shafi motsi da hannu da taka muhimmiyar rawa wajen yada labarai da kuma aikin ceto.
Haka nan, da yake garin da ya karbi bakuncin taron yana kunshe ne da manyan hanyoyin ruwa, an yi amfani da jiragen ruwa marasa matuka na zamani da kasar Sin ta kera wadanda suka yi aikace-aikace cikin sarrafa kansu bisa amfani da fasahar sadarwa ta 5G wacce ta taimaka wajen nuna bayanan ayyukan sa-ido da kuma gwajin yanayin ruwa a kan lokaci. Duk dai a tawagar ta sintiri, an yi amfani da motoci marasa matuka domin tabbatar da tsaro ta hanyar fasahar zamani.
Tabbas, bisa yadda kasar Sin ke yaye injiniyoyi sabbin jini sama da miliyan 4 a kowace shekara da kuma makudan kudin da take zubawa don zurfafa binciken kimiyya, za a ci gaba da ganin nasarorinta a bangaren fasaha mai matukar alfanu ga rayuwar dan Adam a duniya baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)