- Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Yara A Garin Jere
- MazanDa Aka Kama Suka Kubuta Sun Yi Bayani Dalla-dalla
“A ranar da abin zai faru, Auwal ya kai amaryarsa Rabi’atu asibitin Unguwar Masukwani tun da safe saboda laulayin juna biyu da take da fama da shi. Da yamma bayan Isha’i dan’uwansa Rabi’u ya ziyarce shi tare da matarsa Aisha. Suka dan jima suna hira, zuwa can Rabi’u ya ce dare ya fara yi bari su tashi su koma sashinsu.
Sun tafi ba da dadewa ba, Auwal yana kwance a tabarma a tsakiyar falonsu ita kuma amaryarsa tana zaune a kujera suka ci gaba da hira, kwatsam sai ga ‘yan bindiga suka shigo musu, to dama ba su rufe kofa ba saboda dare bai yi ba sosai. Suka ce ka tashi mu tafi, ya ce babu inda zan je, sai suka ce to za mu tafi da kai da matarka ya ce babu inda za mu je, to a wannan lokacin ya mike tsaye ya tare kofar shiga falon, kawai sai suka harbe shi a hannu!
“Hannun ya yi kamar an kwankwatsa da adda, ‘yar fata ce kawai take rike da shi. Suka yi yunkurin fitar da matar ya sake ce musu babu inda za ku je da ita, daga nan ne suka harbe shi a ciki, harbi uku suka yi masa. Nan take ya fadi cikin jini sai suka tafi da matar. To duk abin da ake yi akwai kaninsa Barde yana daki yana ji amma ba hali ya fita, da (Barde) ya ji (‘yan bindigar) sun fita shi ne ya fito da gudu cikin gida ya yi ihu ya ce sun kashe Danlami (Auwal).
Nan fa mutanen gida aka fiffito, to hatta lokacin da mutane suka zo duk da halin da angon yake ciki amma yana cewa ku daga ni, sun tafi da matata, ku daga ni har dai bakinsa ya rufu ya kasa magana.” Wannan shi ne takaitaccen jawabin da majiyarmu ta yi game da kisan da ‘yan bindiga suka yi wa wani ango Auwal Isah suka kuma tafi da amaryarsa Rabi’atu mai dauke da juna biyu a garin Jere da ke babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, yankin Karamar Hukumar Kagarko a ranar Juma’a da dare.
Karo na uku kenan da ‘yan bindiga ke shiga cikin garin Jere suna sace mutane. Na farko sun yi a Unguwar Cabiho inda suka sace wani matashi sai da aka ba su kimanin Naira Miliyan 20, na biyu a Unguwar Ma’aji, sun sace sama da mutum bakwai sai da aka ba su kimanin Naira miliyan 25 har da mashuna guda uku, bayan sun kashe mutum biyu a cikin wadanda suka sace a can inda suke garkuwa da su.
Kwata-kwata bai fi wata daya da sako mutanen da suka sace a karo na biyu ba, suka kuma dawowa suka kutsa har tsakiyar garin suka kashe ango, suka tafi da amaryarsa, suka sace mata da yara a gidan tsohon Kwamishinan Yaki da Fatara na Jihar Kaduna wanda yake shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Kagarko, Hon. Abdulrahman Ibrahim da aka fi sani da ‘Apo’.
A cewar majiyarmu, “Barayin sun shiga gidan Hon. Abdulrahman dare bai ma wani yi sosai ba a lokacin don bai wuce karfe 11 ba. Ikon Allah, duk sauran matansa sun rufe kofa sai Hajiya Ladidi kawai, ita kuma ba ta rufe ne ba saboda akwai bakin da suka zo bikin aure za su kwana a wurinta.
To akwai wasu yara maza da suke kallo a dakinta, amma da ‘yan bindigar suka zo sun samu sun silale ta kofar kicin ta baya. Sai suka tafi da matarsa Hajiya Ladidi da ‘yarta ta goye, da kanwarsa Rabi’atu da ta zo bikin auren daga Zariya, da kanwar matar da suke kira da Walidah.”
Har ila yau, majiyar tamu ta bayyana cewa, barayin sun yi yunkurin shiga gidan Yariman Jere, Alhaji Abdulkarim amma ba su samu nasarar balle kofar gidansa ba.
Wakazalika, wata majiya ta ruwaito mana cewa, barayin sun kutsa cikin garin ne ta hanyar Kasuwa Sabo, inda suka yi awon gaba da wani maishayi Malam Yakubu da wani da ya zo shan shayi da ake ce wa Baba Isah sai kuma wani matashin magidanci mai suna Mubarak.
Da yake bayyana mana yadda ya yi arba da barayin, Malam Mubarak ya ce, “Ina kan hanyata ta dawowa daga can babban gidanmu, daidai bayan dogon gini ina haska tocin wayata, kusa da katangar gidan Alhaji Abba, kawai sai na ji an ce zo nan, ina matsowa suka kama kwalar rigata suka tsugunar da ni tare da su Yakubu da aka kama. Can dai Allah ya ba ni kwarin gwiwa da na ji zan iya sabule rigar, kawai sai na mike na zura a guje. Daya daga cikin barayin, shi ne katon cikinsu ya bi ni muka rufa a guje, to sai magazine (sinkin alburushi) dinsa ta fadi, shi ne na shiga wani gida da gudu na ce wa samarin da na tarar a zauren gidan su gudu ga ‘kidnappers’ nan. Suka shigo da gudu bayan sun rufe kofa, na yi tsalle na kama katangar gidan zan tsallaka kawai sai saman katangar ya rufto mun. To sai na ji shi wanda ya biyo ni din ya harba bindiga ya koma. Shi ne na samu na fito na karaso gida.” In ji shi.
An ruwaito cewa Shugaban ‘Yansanda na Babban Ofishin Shiyyar Jere, ACP Umar Faruk ya kira sojoji da ke Katari domin su kawo dauki, sai dai mutanen garin sun ce babu wani abin a zo a gani da suka tabuka, domin ‘yan bindigar ba su jima da tafiya da mutanen ba amma suka ki bin su sai dai harbe-harben da suka rika yi a sama kawai.
Da yake mana karin haske kan lamarin, wani dankasuwa a Jere Malam Muntari, ya bayyana cewa “daya daga cikin wadanda aka kama Malam Yakubu ya ce sojojin sun je can wurin hanyar jirgin kasa kamar dai suna so su shawo kan barayin, amma a banza, harbi kawai suka yi ra-ta-ta-ta-ta. Daga nan barayin suka ce kowa ya kwanta (su da wadanda suka sace), kuma suka ce a yi baya, ma’ana a sauya hanya.”
Bugu da kari, wani da darayin suka sako washegari, ya bayyana cewa, daya daga cikin matan da suka kama, kafafuwanta na ta jini sai da ya cire rigarsa ya barke ya ba ta don ta nade a kafa. Ya ce tun da aka kama su, barayin suka ba shi yarinyar da ake shayarwa ya saba ta. Sun je wani wuri suna hutawa sai ogan cikinsu ya ce masa ya kama hanya ya tafi.
Mun yi kokarin jin ta bakin ‘yansanda game da abin da ya faru, sai dai ba su bayar da wani bayani ba, domin mun kira Babban Kwamandan Shiyya na Jeren, ACP Umar Faruk ya ce a tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunarsu ta Jihar Kaduna har ma ya aiko mana da lambar wayarsa. Sai dai mun yi ta kira wayar ba ta shiga. Sannan mun tura sakon way ana tes shi ma shiru. Haka nan wakilinmu na Kaduna Shehu Yahaya ya neme shi inda ya ce masa yana cikin taro amma idan ya fito zai yi masa magana, har zuwa lokacin kammala rubuta wannan rahoto dai shiru.
Wata majiya daga ‘yansandan ta tabbatar mana da sunayen wadanda suke hannun ‘yan bindigar da suka hada da Laurat Abdulrahman, Safiyah Abdulrahman, Rabi’at Ibrahim, Rabi’at Abubakar Zakariyya (amaryar da mijinta ya yi shahada) da Walidah Surajo Musa, dukkansu mata da yara.
Da suke gabatar da jawabi a wurin jana’izar marigayi Auwal Isah, wasu daga cikin Malaman Jere, Imam Abdulrahman Musa da Imam Ibrahim Tahir da Malam Ibrahim Zakari, sun karfafa gwiwar al’ummar garin su mike tsaye wajen bayar da gudunmawa kan sha’anin tsaron garin, inda suka yi kiran kara sa ido sosai a kan bakin fuska da gyara tarbiyyar yara da kuma kara himma ga addu’o’i.