Manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga gasar Firimiya ta ƙasar Ingila Arsenal da Liverpool ne su ka haɗu a filin wasa na Emirates da ke arewacin birnin Landan domin fafatawa a wasan mako na 9 na gasar Firimiya ta bana.
A minti na 9 da fara wasan kyaftin din Arsenal Bukayo Saka ya jefa kwallo a ragar Liverpool kafin shima kyaftin din Liverpool Virgil Van Dijk ya farke kwallon mintuna 10 tsakani.
Gab da za a tafi hutun rabin lokaci sabon ɗan wasan Gunners Mikel Merino ya jefawa Arsenal ƙwallo ta biyu kuma ta farko da ya taɓa ci tun bayan zuwansa daga Real Sociedad.
Muhammad Salah ne ya raba gardama a wasan da kwallon da ya ci a minti na 81, da wannan sakamako haka Liverpool ta koma matsayi na biyu a teburin gasar da maki 22 Arsenal ta tsaya a matsayi na uku da maki 18.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp