Da sannu a hankali fasahar zamani na Artificial Interligent na neman mamaye yadda bankuna da cibiyoyin kudi ke gudanar da harkokinsu, a kan haka ‘yan Nijeriya da masana ke bayyana tsoron su na yiwuwar karuwar harkokin ‘yan damfara da cuwacuwa saboda dogaro da wannan fasahar, masu hulda da bankuna da bankunan su kansu za su ci gaba da tafka asarar makudan kudade kamar yadda binciken jaridar LEADERSHIP ya nuna.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke asarar dala miliyan 500 sakamakonm sata ta intanet, wanda hakan ke nuna kudin ya kai Naira biliyan 675 a duk shekara inda ka yi amfani da canjin naira 1,350 a kan dala 1.
- Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN Ya Dakatar Da Harajin Tsaron Yanar Gizo
- Da Ɗumi-ɗumi: EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Da ‘Yarsa A Gobe Alhamis
Kididdga daga hukumar sadarwar Nijeriya NCC ya nuna cewa, Nijeriya na asarar kudaden da aka ambata ne a bangarori daban-daban yayin da bangaren bankunan Nijeriya ya yi asarar fiye da Dala biliyan 8 ga ayyukan masu zamba ta intane a shekarar 2022 kawai.
Hukumar sadarwar ta bayyana cewa, kashi 71 kawai ne bankuna ke bayar da rahoton harin da ake kai musu ta intanet, amma hukumar kula da harkokin bankuna a Nijeriya ‘Nigeria Interbank Bank Settlement System (NIBSS), ta sanar da cewa, bangaren bankuna a Nijeriya sun yi asarar fiye da naira biliyan 50.5 ga masu zamba ta intanet a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.
Fasahar zamani na musamman da ake kira da ‘Artificial Intelligence (AI)’ fasaha ce da ake tafiyar da harkoki tamkar irin na dan adam, an shirya na’ura ta yadda za ta rinka aikin yau da kullum na banki tamkar dan adam kuma a cikin sauri.
Duk da cewa, wannan fasahar ta AI abu ne mai kyau ga bangaren bankuna, inshora da sauran harkokin kudi amma matsalar ita ce yadda za a kare bayanai da kuma sirrukan masu hulda.
Babban damuwar al’umma anan shi ne yadda wasu bayanai na sirri na al’umma da za a iya sanya wa fasahar AI za su iya fadawa hannun bata gari ta yadda za su iya amfani da su wajen damfarar masu hulda da wadnnan cibiyoyin kudi, ba tare da sun sani ba.
A kan haka aka gargadi ‘yan Nijeriya da su yi hattara da irin manhajojin AI da suke saukewa a wayoyinsu don su kan kasance wasu kafa na lekan asiri da bata gari ke amfani da su wajen satar bayanai masu muhimmanci daga wayoyin mutane domin aikata muggan ayyukansu na damfara.
Hukumar Lamuni ta Duniya IMF, ta bayyana cewa, cibiyoyin kudi sun sanar da asarar kudaden da ya kai dala biliyan 12 tun daga shekarar 2004 da kuma asarar dala biliyan 2.5 tun daga shekarar 2020.
A rahotonta na halin da bangaren harkar kudi na duniya yake tafiya na shekarar 2024, IMF ta bayyana cewa, hare-hare ta intanet ga bankuna yana kara karuwa a kullum, inda ake asarar kudade masu dimbin yawa.
Masana sun bayyana cewa, masu aikata laifi ta inatne sun rungumi tsarin AI, inda suka fito da sabbin dabaru na rudar da mutane inda suke amfani da jimloli masu tsawo waje aikata damfara musamman ga bankuna a fadin duniya.
A yayin da ake ci gaba sauraron aukuwar karin hare-haren na ‘yan damfara masu amfani da AI, masana sun bayar da shawarar, a karfafa dabarun kariya ga manhajojin bankuna masu AI tare da kuma sabunta su aka-akai.
Rahoto na baya-bayan nan daga cibiyar binciken laifukkan da ake aikatawa da kwamfuta, ‘Computer Crime Research Centre (CCRC)’ ta yi lura da cewa, damfara ta intanet ya haura zuwa akalla dala tiriliyan 12 a shekrar 2024 saboda amfani da fasahar AI, rahoton ya kara da cewa, “A shekarun 2024 da 2025, za mu fuskanci karuwar ayyukan ‘yan damfara ta intanet masu kai hari ga bankuna, za kuma mu ga karuwar amfani da fasahar AI wajen aitaka wadanna ayyukan rashin gaskiyar.
“Fasahar Deepfake zai mamaye tsofaffin hanyoyin da ‘yan damfara ke amfani dasu. Yayin da harkokin kasuwanci da dama za su rungumi fasahar AI, za kuma su fuskanci gaggarumar barazana daga masu aikata laifukka ta intanet musamman amfani da fasahar AI, wadanda za su bullo da sabbin fasahohi da za su karya duk wata kariya da cibiyoyin kudin ke samarwa.
“Bangaren da za su fi fadawa wannan hadarin sun hada da masu kananan kasuwanci da cibiyoyin kudi da basu da manyan jari wadanda ba za su iya saye tare da samar wa kan su manhajoji masu karfi da za su bayar da kariyar da ake bukata ba,” in ji rahoton.
Da yake tabbatar da sakamakon wannan rahoton, wani tsohon darakta a hukumar NDIC, Dakta Jacob Afolabi, ya lura da cewa, an samu karuwar hare-hare ga cibiyoyin kudi ta hanyar fasahar AI a shekarar 2023, sun kuma aukar da gaggarumin asara ga cibiyoyi da hukumomin gwamnati.
Afolabi ya kuma yi bayanin cewa, fasahar AI na iya sarrafa bayanai masu yawan gaske a lokaci daya, abin da yake kara tsoron kariya ga sirrin wadanan bayanai da kuma tsaronsu.
“Fasahar Al na kara karuwa tare da sarkakiya, haka kuma kare masu amfani da su yake kara wahala ga kuma yiwuwar an yi amfani da su ta barauniyar hanya yana kara karuwa. Masu aikata laifukka ta intanet na kara fito da sabbin hanyoyin da za su karya duk wata kariya da aka yi wa fasahar AI don su cutar da masu amfani da ita musamman a bangaren cibiyoyin kudi da sauransu,” in ji shi.
Domin samar da kariya ga bayanan al’umma, Afolabi ya bayar da shawarar a samar da dokoki na musamman domin kariya ga masu amfani da fasahar AI.
Dogaro kacikan ga fasahar AI yana kaiwa ga rasa zimma daga nutane, tunani mai amfani da kuma rasa hannun dan adama abin da ake yi, a kan haka tsohon daraktan ya bayar da shawarar cewa, ya kamata a samar da daidaito a tsakanin amfani da fasahar AI da kuma amfani da dan adama a harkokin bankuna da wuraren da ake amfani da fasahar AI saboda samar da kariya da kuma sanya ido na dan adam a harkokin yau da kullum.
Ya kuma kara da cewa, “rungumar fasahar AI na iya haifar da rasa ayyukan yi ga al’umma a ma’aikatu musamman ga ma’aikatan da basu da kwarewa na musamman, dole ma’aikata su rungumi ilimin fasahar zamani in har suna son kasancewa a fagen ayyuka a wannan zamani,”.
Haka kuma darakta mai kula harkokin gwamnati a kamfanin Microsoft Africa, Akua Gyekye, ya ce in har ana son amfani da fasahar AI a cikin nasara dole hukumomin gwamnati su rungumi tsarin tare da samar da tsarin gudanar da ayyukan a hukumance.
Ya bayyana cewa, kasashen Afrika da dama sun fara samar da dokoki da tsare-tsare a hukumance a kan tafiyar da fasahar AI, hakan ya kuma kai ga shirye-shiryen samar da wani tsari da zai tafiyar da hanyoyin kariya ga fasahar AI a duniya gaba daya.
Ta kuma kara da cewa, Kungiyar Tarayyar Afrika ta kira taron masana kimiyyar sadarwa a wannan shekarar inda suka samar da daftarin dokoki na yadda za a tafiyar da harkokin fasahar AI a tsakanin kasashen Afrika.
Wani jami’i a hukumar sadarwa ta Nijeriya NCC, Kelechi Nwankwo, ya ce, duk da bunkasar harkokin sadarwar zamani a Nijeriya, ana fuskantar hare-hare na intanet abin kuma na iya karuwa a nan gaba.
Da yake nuna damuwarsa, shugaban kamfanin inshora na Guinea Insurance Plc, Ademola Abidogun, ya ce, duk da cewa, amfani da fasahar AI na da muhimmanci ga bangaren inshora amma matsalolin da ke tattare da hakan suna da yawan gaske, musamman a bangaren kariya ga bayanai na sirri na al’umma.
Tun da farko hukumar Lamuni ta Duniya IMF ta bayyana cewa, masu aikata laifi ta intanet sune babbar barazana ga harkokin cibiyoyin kudi inda suke dagula harkokin bankuna suna kuma sanya tsoro ga masu hulda da cibiyoyin kudin gaba daya.
Domin karfafa bangaren bankuna da cibiyoyin kudin, IMF ta bayar da shawara ga manyan bankuna kasa na su samar da tsarin kasa na yaki da masu zamba ta intanet tare da sanya ido da kuma aiwatar da dukkan dokokin da aka samar na kariya daga sharrin masu aikata zamba ta intanet.
Haka kuma, a nasa tsokacin, shgaban kungiyar jami’an kula da tsaron bankuna a Nijeriya (CCISONFI), Mr. Festus Amede, ya bayyana bukatar samar da tsarin kariya ga bayanan sirri a cibiyoyin kudin kasar nan musamman daga barazanar masu aikata laifi ta intanet.