A ranar 27 ga wannan Agustan 2022 ne karamar ministar Babban Birnin Tarayya, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta mika wa Sarkin Gwari, Alhaji Awwal Musa Ijakoro sandar girma na 11.
Wasu daga cikin sarakunan arewa sun nuna wa matashin basaraken kara na bayar da lokacinsu zuwa ta ya shi murna a wannan rana.
- Muna Zargin Masallatai Da Coci-coci Da Hannu A Satar Mai –Kyari
- …Dalla-dallar Yadda Aka Kashe Kudin Tallafin Mai
Da take mika masa sandar, minisarar ta roki al’umar Bwari da su bai wa sarkin goyan baya. Sannan ta yaba da kokarin sarkin wajen hada kan al’ummarsa da shugabanci nagari.
Hajiya Ramatu ta yi kira da sarkin da ya yi riko da alkur’ani a wajen shugabatar al’umarsa tare da kauce wa duk wani kabilanci da son zuciya kamar yadda Allah ya umurni.
Mai Martaba, Alhaji Awwal Musa Ijakoro ya gaji wannan sarauta ce a gurin mahaifisa, Alhaji Musa Muhammad Ijakoro, wanda a hannunsa masarautar ta zama mai daraja ta biyu a 12 ga watan Yunin 1997.
A shekarun da Mai Martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro ya yi a kan karagar mulki ya sami nasarar hada kan al’umarsa waje guda, wanda hakan ya kawo masa daukaka a masarautarsa baki daya.
Da yake amsar sandar, Mai Martaba Alhaji Awwal Musa Ijakoro ya nuna godiyasa ga Allah Madaukakin Sarki da ya nuna masa wannan rana, sannan ya godi wa dinbin mutanen da suka zo don nuna masa kauna da kuma al’ummar Bwari baki daya.
Ya kuma mika godiya ga gwamnatin tarayya da ministan Abuja da sauran dukkan ma’aikan da ke karkashin minisatan Abujan baki daya.
Ya yi kuma jinjina ga majalisarsa bisa ba shi goyan baya wajen samun nasarar yin wannan taro.