• English
  • Business News
Friday, June 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Gwamnonin Nijeriya Suka Butulce Wa Shugaba Buhari Bayan Ya Fitar Da Su Kunya

Jerin Tallafin Ceto Da Ya Ba Su Baya Ga Kuɗaɗen Paris Club

by Bashir Ahmad
2 years ago
in Makala
0
Yadda Gwamnonin Nijeriya Suka Butulce Wa Shugaba Buhari Bayan Ya Fitar Da Su Kunya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ceto gwamnonin Nijeriya daga halin ni-`ya-su na matsin tattalin arziki a yayin da jihohinsu suka shaƙi ƙamshin mutuwa ta hanyar bijiro da tallafin Gwamnatin tarayya ba ɓoyayyen abu ba ne a ƙasar nan, kowa ya sani.

Shakka babu jama’a na ankare da yadda gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari, ta samu Nijeriya a cikin wani mayuwacin hali a shekarar 2015, baya ga fama da matsaloli masu nasaba da rashin tsaro da ayyukan tada ƙayar baya na Boko Haram, akwai kuma matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da suka tilasta wa ƙasar tsayawa cak a wancan lokaci. Wanda hakan ya sanya tunani a zukatun wasu daga cikin ƙungiyoyin da ke ciki da wajen ƙasar nan tare da amanna da cewa ban da zuwan Buhari, da irin kishin ƙudirinsa na alkhairi da yake da shi ga ƙasar, da tuni magana ake ta yadda ƙasar ta tsinci kanta cikin yanayi na tsananin rikicin da zai sa ta zama labari.

Tsananin da ya sanya masu ƙaramin ƙarfin har ma da masu hanu da shuni cikin wani yanayi na ƙunci a wasu daga cikin jihohin da ke faɗin ƙasar nan ko da kuwa ba a ce dukkansu ba, tsananin matsin tattalin arzikin da aka tsinci kai a ciki ya sanya wasu daga cikin gwamnonin ƙasar nan kasa biyan albashin ma’aikata a jihohinsu tare da ciyo bashi daga wasu wuraren, baya ga irin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya take turo wa jihohin domin yin wasu ayyuka da biyan albashi da ya zamana tilas a wuyan gwamnati.

  • Buhari Da Tsofaffin Shugabannin Kasa Sun Bukaci ‘Yan Takara Su Karbi Sakamakon Zabe

Hakan dai ya bayu ne zuwa wani yanayi da gwamnonin ke fakewa a bayansa na ƙarancin kuɗaɗe da rashin samar da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’ummar da suke shugabanta.

To, sai dai a iya cewa zuwan Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa, ya yi tasiri ƙwarai da gaske wajen ceto waɗannan jihohi daga halin ƙamshin mutuwar da suka shaƙa ta hanyar karɓar tallafi daga gwamnatin Buhari, ba tare da la’akari da jam’iyya ko addini ba.

Labarai Masu Nasaba

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

Ranar Jin Kai Ta Duniya (2024): Kiran Gaggawa A Kan Ceton Rayuka

Tallafin kuɗaɗen ‘Bailout’, Paris Club har ma da na Cutar Korona (COVID-19).

Tallafin Kuɗi Na ‘Bailout’
Tun bayan rantsar da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bijiro da tsarin bayar da tallafin kuɗi na ceto jihohi daga ƙaƙa-ni-ka-yi da ake kira da ‘Bailout’, inda aka fitar da tsabar kuɗi har Naira Biliyan 477 domin farfaɗowa tare da inganta rayuwar wasu daga cikin jihohin Nijeriya, ƙari da wasu kuɗaɗen da gwamnonin jam’iyyar APC suka nema na ƙarashen kuɗaɗen ayyukan manyan titunan da suka ƙarasa mallakin gwamnatin tarayya a jihohinsu.

Wanda bincike ya gano cewa ba wannanne karon farko da gwamnonin ke neman ƙuɗi da nufin ƙarasa ayyukan gwamnatin tarayya ba, inda ko a gwamnatocin baya an samu irin wannan iƙirarin daga wajen gwamnonin.
Sai dai ba wai iya tallafin kuɗin biyan albashi gwamnatin Buhari ta agaza wa da gwamnonin ba har da kuɗaɗen da za su biya Ariyas ga ma’aikata.

Tallafin Paris Club
A magana ta gaskiya da zahirin abin da ya bayyana a lokacin da jihohi suka tsinci kansu a halin ƙamfar kuɗi da rashin fara gudanar da ayyukan raya ƙasa da walwalar al’umma, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bai wa gwamnatin tarayya umarni da a bai wa dukkanin wata jiha zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 10 na tsawon watanni 8, a dai dai lokacin da farashin gangar ɗanyen man fetur ya faɗi a kasuwar duniya.
Idan `yan Nijeriya za su iya tunawa an yi wani lokaci da jihohi ke kokawa kan rashin amfana da bashin Paris Club, wanda hakan ya tilasta wa gwamnatin tarayya ware musu nasu kason. Mun kuma san cewa ban da jin ƙai irin na Shugaba Buhari da wasu gwamnonin da jihohinsu babu inda za su je.

Buhari

Tallafin Korona (COVID-19) Ga Jihohi
A shekarun baya, a daidai lokacin da ƙasar nan ta shiga wani yanayi na halin matsin tattalin arziki sakamakon ɓullar cutar Korona (COVID-19) wanda ba wai Nijeriya lamarin ya shafa ba kaɗai, a’a duniya ce baki ɗaya, amma cikin adalcinsa, Shugaba Buhari ya ɓullo da wasu hanyoyin tallafa wa gwamnoni da nufin tallafa wa talakawan da ke zaune a gida, wanda har aka zargi wasu daga cikin gwamnonin da karkatar da kayan tallafin domin amfanin kansu, wasu kuwa ajiye kayan suka yi har sai da ruwa ya lalata su aka yi ba-wan-ba-ƙanin.

Mu Kalli Wani Abu ta Mahangar Siyasa
Idan muka ajiye maganar ceton jihohi da gwamnoni da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta yi a ƙasar nan ta hanyar tallafa musu ta hanyoyi daban-daban, na tabbatar da cewa `yan Nijeriya sun aminta da cewa wasu daga cikin gwamnonin musamman na jam’iyar APC sun shiga rigar mutunci da alfarmar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ta silar haka suka lashe zaɓukansu a jihohinsu, na san ba za a taɓa mantawa da abin da aka yi wa take da “Guguwar Buhari” ba.
To amma abin takaici shi ne yadda wasu daga cikin su har yanzu jahilci ya hana su fahimtar ba domin shi ba da tuni da dama daga cikinsu na gidan Yari, wasu kuwa suna can an manta da babinsu a duniya.
Haka kuma shugaban ya tsaya kai da fata wajen ƙarfafawa talakawan ƙasar nan ƙwarin gwiwar zaɓensu domin ba su dama su jagorance su tare da tunanin cewa su ma suna ƙaunarsa tsakani da Allah, wanda a zahiri Musa ne a baki Fir’auna a zuciya, wasu kuwa raɓuwa suke da hotunansa a yayin gangamin yaƙin neman zaɓensu domin kuwa sun yarda da cewa Buhari, ya zo da manufofin da za su ceto wannan ƙasa daga halin da ta tsinci kanta a wancan lokaci.
To, sai dai cikin mamaki wai a ce waɗannan gwamnonin da suka shiga rigar alfarmar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ne a gaba-gaba wajen cin amanarsa da faɗa masa maganganun da ko ƙuda ba zai kalla ba ballantana ya ci, kuma ba don komai ba, sai don yinƙurin shugaban ƙasan wajen tabbatar da cewa an samar da sahihin zaɓe ga `yan ƙasa da za su aminta da shi.
Ashe ba a banza ba masu zalaƙar iya harshe ke faɗar “siyasa ba ta da gwani”.

 Me Ya Kamata `Yan Nijeriya Su Sani?
Ya kamata al’umma su sani cewa tsarin sauya fasalin takardun kuɗi da gwamnati ta bijiro da shi an yi shi ne da kyakkyawan ƙudiri domin ci gaban Nijeriya da kuma samar wa da ƙasar kyakkyawar gobe.
Haka kuma ƙudirin da ake sa ran zai daƙile matsalolin cin hanci da rashawa da inganta tattalin arziƙin ƙasa har ma da sauran wasu abubuwan da ka iya kawo naƙasu ga ci gaban wannan ƙasa.
Baya ga wannan halin matsi da wannan doka ta zo da ita wanda masana da dama suka yi amanna gaba za ta yi kyau, ya kamata `yan Nijeriya, su sani cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ba mai satar kuɗin ƙasa ba ne, haka kuma ba mayaudari ba ne, hasalima ba zai taɓa yin abin da zai sanya rayukan talakawa cikin hatsari ba.
Har ila yau, ya kamata mu tambayi kanmu, me ya sa gwamnonin suke ƙalubalantarsa kan wannan doka? Me ya sa ba su yi haka a kan sauran ƙudirorin da suka shafi talaka kai tsaye ba? Me ya sa ba su ƙalubalanci wasu dokokin da aka yi a baya ba wanda wasu ma ba su da masaniyar yin su, amma me ya sa sai wannan?
A ƙarshe zan ƙarƙare da ba da shawarar cewa, idan har yanzu kana ko kina ajiye da tsoffin takarardun kuɗi to, a yi ƙoƙari a kai su Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin a canza su, duk yawansu, matuƙar ka kasan halak malak ɗinka ne, domin ciki da gaskiya, wuƙa ba ta huda shi…

Bashir Ahmad, shi ne Mai Taimaka Wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na Musamman A Kan Shafukan Sadarwa na Zamani.

  • https://leadership.ng/buhari-wife-close-aides-arrive-daura-for-presidential-nass-elections/

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BuhariGwamnoniJihohiNijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Warware Rikici Cikin Lumana Ta Hanyarta

Next Post

Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

Related

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya
Makala

Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Wata Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Tsarin Shugabancin Duniya

9 months ago
Ranar Jin Kai Ta Duniya (2024): Kiran Gaggawa A Kan Ceton Rayuka
Makala

Ranar Jin Kai Ta Duniya (2024): Kiran Gaggawa A Kan Ceton Rayuka

10 months ago
Hukuma Ta Koka Da Yadda Masu Mulki Ke Tauye Hakkin Al’umma
Labarai

Hukuma Ta Koka Da Yadda Masu Mulki Ke Tauye Hakkin Al’umma

12 months ago
Hadiza Bala Usman Ta Gargadi Masu Gangamin Bata Mata Suna
Makala

Hadiza Bala Usman Ta Gargadi Masu Gangamin Bata Mata Suna

2 years ago
Sam Nda-Isaiah
Makala

Shekara 61 Da Haihuwar Sam Nda-Isaiah: Waiwayen Mukarrabai Kan Mashahuran Hikimominsa

2 years ago
Next Post
Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

Bukatar Samar Da Cikkakken Tsaro Ga Hukumar Zabe

LABARAI MASU NASABA

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)

June 13, 2025
Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka

Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka

June 13, 2025
nijeriya

Yadda Badakalar Tallafin Man Fetur Ta Zame Wa Nijeriya Alakakai

June 13, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Cimma Daidaito Da Sin Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya

June 12, 2025
Ba Zan Bar Nijeriya Ta Zama Kasa Mai Jam’iyya Daya Ba – Tinubu

Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025

June 12, 2025
Sin Na Fatan Amurka Ta Yi Hadin Gwiwa Da Ita Don Tabbatar Da Matsayar Da Shugabannin Kasashen Biyu Suka Cimma

Sin Na Fatan Amurka Ta Yi Hadin Gwiwa Da Ita Don Tabbatar Da Matsayar Da Shugabannin Kasashen Biyu Suka Cimma

June 12, 2025
Sin Ta sanya Indonesiya Cikin Tsarin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Na Sa’o’i 240 Da Kara Yawan Kasashen Tsarin Zuwa 55

Sin Ta sanya Indonesiya Cikin Tsarin Shiga Kasar Ba Tare Da Biza Ba Na Sa’o’i 240 Da Kara Yawan Kasashen Tsarin Zuwa 55

June 12, 2025
Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka

Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka

June 12, 2025
Zambar Naira Miliyan 55: ICPC Ta Fara Bin Diddigin Dan Kwangilar Dam Din Jihar Filato

ICPC Ta Gurfanar Da Ma’aikacin Kotu Bisa Badakalar Naira Miliyan 9.2

June 12, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

Fahimtar Sabon Tunani: Raya Kimiyya Da Fasaha Da Dogaro Da Karfi Na Kashin Kai Sun Ingiza Ci Gaban Kasar Sin 

June 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.