ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Smishing Wajen Yin Kutse

by Ibrahim Sabo
3 years ago
Smishing

A kullum madatsa ‘Hackers’ suna bin hanyoyi daban-daban wajen ganin sun yi kutse a mutane.

Kutsen kuwa ya hada da shafukan sada zumunta kuma har da asusun ajiya na Banki. Wata hikimar da suke yi wajen yin datsa (Hacking) wadda ta yi Kaurin suna a wannan lokacin da ake Kira smishing ta sanya mutane da dama a halin ha’ula’i, duba da yadda ake yaudararsu don cutar da su.

  • Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Ita? (Kimiyya)

Smishing wata dabarar kutse ce da ‘yan madatsa, wadanda aka fi sani da hackers su ke amfani da ita wajen yaudarar mutane.

ADVERTISEMENT

Suna amfani da wannan dabarar ne wajen yaudarar mutane ta hanyar tura musu saKonni ana tambayarsu game da wadansu bayanansu na sirri.

Irin wannan kutsen yana daga cikin ire-iren kutsen Social Engineering da ya addabi mutane. Don haka mutane da dama suna yawan Korafe-Korafe a kan yadda ake musu kutse ta hanyar shiga asusansu ba tare da saninsu ba.
Sai dai duk da haka, abin da ba a sani ba shi ne, mutanen ne da kansu ke bayar da bayanansu da hanunsu.

LABARAI MASU NASABA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Hanya mafi sauKi da madatsan kan bi wajen rudar mutane ita ce tura musu saKonni, musamman zuwa asusun saKonninsu (inbod) na waya da ke nuna kamar saKon yana da inganci, misali; saƙo daga 500, ko 424 ko makamancin haka. Wato dai wani code, wanda ke nuna cewa ba daga lambar waya bane, don kar a gane su.

Irin wadannan saKonnin suna tunzura mutum ya bayar da bayanansa na sirri, musamman idan aka dubi lambobin da aka yi amfani da su wajen tura saKonnin. Ta wannan hanyar mutum zai yi tunanin daga wani kamfani ne ake neman bayanansa.

Akwai wasu kalmomi da suke kamanceceniya da smishing, wadanda duk suka kasance ire-iren dabarar kutse Social Engineering kamar haka:

1. Smishing — Tura saKonni zuwa asusun saKonnin waya don rudar da mutane tura bayanansu na sirri zuwa ga madațsa.
2. Phishing — Tura wa mutane liKau, manhajoji ko saKonnin email don karbar wasu muhimman bayanansu na sirri.
3. Bishing — Ƙiran mutane a waya ta hanyar bi da lallami da kalaman yaudara don damfararsu, musamman don samu bayanansu na sirri.

Ta Yaya Mutum Zai Kare Kansa?
1. Kada a danna liKau ko shafin yanar gizon da ba a yarda da su ba.
2. Kada a mayar da martani ga saƙon imel ɗin da ba a yarda da shi kuma ba a san wanda ya turo shi ba.
3. Kada a kula da Kiraye-Kirayen wayoyin da ba a san su ba.
4. A rinKa kula da shafukan da ake ziyarta da tabbatar da sahihancinsu.
5. Kada a sanya manhajar da ba a tabbatar da sahihancinta cikin na’ura ba.
6. A kula da saKonni a cikin waya kuma kada a mayar da martani gare su.
Tabbas ya zama wajibi a kula da wadannan shawarwari don kada a yi nadama nan gaba, domin yanzu kutse ya zama ruwan dare a wannan zamanin.
Bugu da Kari, a rinKa kula da saKonnin da ake samu daga banki haKiKa ba kowane saKo ba ne daga asusun banki, sau tari ana iya amfani da wasu dabaru don kutse cikin na’urori don tura wa mutane saKonnin bogi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje
Rahotonni

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba
Manyan Labarai

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Next Post
Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Fasa Bututun Mai

Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Fasa Bututun Mai

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba 

November 17, 2025
Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

November 17, 2025
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing

November 17, 2025
NBS

Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%

November 17, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO

November 17, 2025
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

November 17, 2025
Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

Kudaden Kasafin Kudin Sin Sun Karu Da Kashi 0.8 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana

November 17, 2025
Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi

November 17, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin

November 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.