• English
  • Business News
Sunday, July 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

by Rabi'at Sidi Bala
5 hours ago
in Taskira
0
Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu ‘yan matan ke daukar lambar motar duk namijin da suka ga ya yi musu, musamman idan motar me tsada ce su kai wa malami domin a janyo musu hankalinsa. Haka kuma wasu daga cikin iyaye mata na zuwa wajen malami domin a gwada musu taurarin ‘ya’yansu Domin a janyo musu mijin aure, musamman wanda tauraronsa zai yi daidai da na ‘yarsu (namiji mai kudi), za a janyo shi ko a ina yake, zai taho da gaggawa domin auren ‘yarsu.

  • Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • “Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; “Shin me yake janyo hakan, kuma dama ana iya janyo hankalin namiji ta lambar mota, shin hakan abu ne me kyau ko kuwa kuskure ne, mene ne ribar yin hakan, kuma me yake janyo hakan, ko akwai wasu matsaloli da hakan zai iya haifarwa?”.

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Fatima Rabiu Janyau daga Gusau:

Labarai Masu Nasaba

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo

Eh, wasu mata suna daukar lambar motar duk wanda ya yi musu kyau ko ya zo da motar alfarma, su kai wa malami ko boka domin a janyo hankalinsa ya zo neman aurensu. Hakan kuskure ne babba, ba daidai ba ne a nemi aure ta hanyar sihiri ko dabara marar tsarki. Duk wata riba da ke tattare da hakan ba ta da karko, kuma tana iya dawo da akasin abin da aka nema, kamar rashin samun auren kwarai da tsayayye, zama da mutumin da ba da gaske yake ba, daukewar albarka daga rayuwa, fushin Allah da rushewar aure cikin lokaci. Shawara ga masu haka; ku dogara da addu’a, tarbiyya da hakuri, idan aure naku ne, zai zo da sauki cikin halal. Kada ku cuci kanku don burin duniya, ku tsaya akan gaskiya da dabi’a ta gari. A guji bin hanyar da ba ta dace ba domin cimma buri, duk mai hakuri sai ya ci riba.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, Dan Jarida kuma Marubuci daga Jos:

Mata ku ji tsoron Allah, kuma ku nemi yardarsa

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un! Wannan labari ne mai daga hankali da firgitarwa. Son auren miji mai kudi ko samun mijin aure mai rufin asiri ya rufe wa wasu mata ido, suna rasa imaninsu, don biye wa son zuciya. Lallai tsafi gaskiyar me shi ne, kuma abu ne mai yiwuwa a yi wa mutum asiri daga lambar waya ko wani abu mai nasaba da shi. Mutanen da suke shiga malamai don su jawo ra’ayin namiji da karfin asiri ba da addu’a ba, suna jefa kansu ne cikin tarkon shirka. Sannan ko da bukatar su ta biya ba lallai ne auren mutumin ya zama alheri ga rayuwarsu ba. Shawarata ita ce, duk abin da muke neman mallaka a rayuwarmu, mu yi addu’a mu nemi yardar Allah da zabinsa, domin idan Allah Ya kaddara za ki yi rayuwa da mutumin da kike so, zaman ya yi albarka, kuma ku ji dadin rayuwa da juna. Muna neman tsarin ubangiji daga sharrin malaman tsibbu, bokaye da matsafa dake rinjayar zuciyoyin mata marasa tsoron Allah. Su kuma masu yi Allah Ya shirye su. Amin

 

Sunana Balkisu Galadanchi Sokoto:

To da farko dai abin da zan ce shi ne; Ni ban yadda da boka ko malam ba, abin da kawai na sani kudirar Allah ce kadai za ta iya kawo wannan mutumin. Idan ya kasance motar ta aro ce kuma fa? Wannan babban kuskure ne, duba da cewar a Musulunci ma shirka ce, kuma tsaf za ki gayyato dan shan jini. Hakan sam ba riba, mugun kwadayi ne da zai iya janyo wa mutum halaka kai tsaye. Matsalolin da wannan abin zai iya haifarwa suna da dama musamman rashin tabbas, duk ranar da tsafi ya bar jikinsa da kan mutum zai yi bayani ai. Iyaye da ‘yan mata ku kama mutuncin kanku, ku sani hakan yi wa Allah shisshigi ne kuma shirka ce babba, Allah ta’ala ya sa mu dace.

 

Sunana Ibrahim Garba Bizi, Damaturu Jihar Yobe:

Wannan toshewar basira ce babba wanda mutum zai yi, ba ka san ta hanyar da ya samu motar ba, ko ta yankan kai ne ba ka sani ba. A’a kuskure ne gaskiya, ba ta da wani riba ko kadan a rayuwa. Zai Haifar da rashin imani, Allah ne ke azurtawa. Shawara su daina tun kafin mutuwa ta riske su saboda shirka ne, kar rayuwar duniya ta rude su, su nemi na kansu.

 

Sunana Princess Fatimah Mazadu daga Jihar Gomben Najeriya:

Subhanallahi Wa Azubillahi Minash-shaidanir Rajeem! cab-di-jam, wannan ai babbar shirka ce fakewa da aure ta hanyar yaudara da tilastawa, kuma mafi kuna ta sabon Allah ba ta hanyar addu’ar; ubangiji ya hadaka da naka rabon ba, ko da bai kai wanda ka gani din ba, Allah ya kiyaye mana imanin mu. Eh! gaskiya ana yi saboda mata da yawa suna fariya sun auri mazajensu ta wannan hanyar ‘more especially’ akan ‘plat forms’ na Instagram, snap chat, tiktok da sauransu, gaskiya ana yi duk da ni na fi yarda don Allah ne ya bar su da dabararsu. Abu ne mara kyau a zahiri da badini, babu wata riba ko kadan sai tarin nadama da da-na-sani, ‘yes’ ka cika burinka ka auri abin da ka ke so ta karfi, amma kwanciyar hankali fah? babu shi don Allah shi ke azurtawa kuma ke ba da duk wani abu da bawa ke nema da bukata kan ya roke shi ma. Akwai matsaloli masu tarin yawa, kamar rasa Imani, taurin zuciya, buri da kwadayi, da-na-sani da zubar mutunci ranar da duk asiri ya tonu, asara biyu ga mari ga tsinka jaka, biyu babu, ba mutunci, babu masoyin. Saboda duk tsayi da tasirin asiri ba ya ‘lasting’ wata rana abin zai warware a bazata ke kare shekarun duniyar ki kina nadama ke da iyayen naki. Mata ko tsoro ba sa yi don ka kansa da mota ka san halayensa ne? watakila dan yawo ne, ko dan daba, ko mazinaci, ko mashayin giya, wanda jurarsa zai rika baki wahala, kin ga farin ciki ya zamo bakin ciki.

 

Sunana Labaran Jibrin Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Batu na farko hakan na nuna san zuciya karara a fili kenan, sai kuma ta fuskar addini hakan babban kuskure ne, domin rashin bar wa Allah zabi akan abu mafi alkhairi. Kuma mene ne hukunci mai duba taurari a Musulunci? Saboda haka duba taurari ai kamar bugun kasa ne, dame bugun kasa da wanda ake bugawa mu kalli hukuncin su a addinance. Abu na biyu babu wata riba ga mai hankali, kuma ko hausawa kan ce kowa ya hau motar kwadayi ya zama dole a sauke shi a tashar wulakanci. Abu na uku dole akwai matsaloli sosai domin ba za ma mu ce matsala ba misali kin ga mutum da babbar mota ba bincike shin wane ne shi ya halayyarsa kuma mece ce sana’arsa da sauransu, daga karshe ma wata kila ‘yahoo boys’ ne ko wani matsafi ko kawali da dai sauransu daga ranar da asirin hakan ya tashi tun a nan duniya riba aka ci ko faduwa, ba a zo kan maganar addini ba ma, shin mai duba taurari da kuma wanda za a duba masa haram za su ci ko halak, Manzon Allah (S.A.W). ya ce ku ciyar da iyalanku da halal, kuma ku shayar da kanku da iyalanku da halal, domin duk naman jikin dan’adam din da aka gina da halal ko wuta ba ta bukatar ci.

 

Sunana Fatima Nura Kila, A Jihar Jigawa:

Tabbas mu kan ji wannan labarin mu ma, amma zahiri akwai wadanda suke aikata wannnan dabi’ar kuma wasu su kan yi nasara, amma wasu su kan yi akasin haka. Tabbas babban kuskure ne a Musulunci ma, babu wata riba a ciki domin a karshe su kan yi da-na-sani, abin da yake janyo wa hakan kuma san duniya ne, da kuma dole wasu matan sai sun auri masu kudi saboda a ganinsu auren me kudi shi ne jin dadi bayan ba haka ba ne. Zai haifar da matsaloli wacce sai a gaba mace za ta gane abin da ta aikata babban laifi ne. Shawarar da zan bawa masu wannnan akida su sani duk inda arzikinka yake tabbas zai zo kawai lokaci ne, amma sun kasa ganewa, fatan mu Allah ya sa mu fi karfin zuciyar mu.

 

Sunana Khadija Auwal Koki, A Jihar Kano:

To gaskiya wannan babban kuskure ne ya kamata iyaye da ‘ya’yan su ji tsoran Allah, domin aure lokaci ne kuma su san hakan babbar illa ce, domin kuwa ba su san wanda za su janyo ba, watakila ya zame musu da-na-sani. Hakan ba, abu ne mai kyau ba, domin kuwa iyaye za su jefa ‘ya’yansu ne a kan turbar da-na-sani, kuma hakan ba zai haifar da da mai ido ba. kuma kwadayi ke jawo haka, kuma an ce kwadayi mabudin wahala. Hakan na iya janjo hulakanci da rashin ganin mutuncin juna da kuma rashin zaman lafiya, domin soyayyar ba ta Allah da Annabi ba ce. Shawara ita ce duk mai hali irin wannan ya yi gaggawar sauya halinsa kuma ya tuba ya mika lamarinsa zuwa ga Allah.

 

Sunana Hussy Saniey, daga Jihar Katsina:

Mutane sun zama abin da suka zama, sun mayar da kwadayi sana’arsu, shi ya sa har suka dauki wannan hanyar suke ganin ita ce mai billewa a gare su tare da taimakon wani mushirikin da ke irin wannan aikin. Za a iya dacewa domin an ce tsafi gaskiyar mai shi amma idan har mai motan ya rike azkar da hannu bibbiyu to ba za su ci nasara akan shi ba. Wannan abin babban kuskure ne suke aikatawa kuma babu wata riba da za su samu sai dai ma su tsinci larabarsu a talatarsu, domin za su janzo wa kansu nadama marar amfani. Babbar matsala kuwa hakan yake janyowa domin shi asiri tasirinsa na lokaci kadan ne daga ya karye kuma yarinya za ta tsinci kanta a duniyar zawarci bayan imaninta da ya raunana. Shawara ita ce su yi hakuri su daina suna zaune Ubangiji zai kawo masu namijin da yake daidai da rayuwarsu, wanda zai rike su fiye ma da yadda suke hari domin Allah ya fi su sanin abin da ya dace da rayuwarsu.

 

Sunana Hafsat Sa’eed daga Naija:

Yin hakan kuskure ne, domin ba a san me za a daukowa kai ba, dan shaye-shaye ne, ko dan daba ne, ko matsafi, ko me wata mummunar dabi’ar da ba a so, wanda zai addabi al’umma kuma a je a haifi ‘ya’ya cikin rashin sa’a a haifo me dabi’unsa, ya kamata a kula da irin wadannan abubuwa dan wannan sam! ba ci gaba bane, ci baya ne aka samu a daina kallon abubuwa komai ya zama wayewa ko zamani ana yi masa kallon ci gaba, a roki Allah zabi mafi alkhairi.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:

Gaskiya wannan abu bai dace ba sam! an kauce hanyar addini kuma an kama hanyar bata. Wai mai muke son zama ya Allah, babban burin mace ta yi addu’ar samun miji nagari ba mai kudi ba. sai ki ga Allah ya bar mutum da aniyarsa an samu mai kudin karshe a kare a wahala, Allah ya kyauta. Yo ai abu ne a bude babu wani kyau ko alfannu sai bata da tabewa, sannan abin duniya na wasu iyayen dan ba duka aka taru aka zama daya ba, Allah dai ya yi mana magani. Aure da aka gina shi da soyayya da kauna ma yanzu ya Allah ya cika bale auren asiri da zarar ya karye shikenan an tsinci kai a tashar wulakanci. Abin da zan ce Allah ya kyauta ya yi mana magani ya shiryi masu yi su gane gaskiya kawai.

 

Sunana Aisha Lawan Ya’u Momy, Jihar Kano Ado Bayero Layout:

Tabbas hakan yana faruwa ga wasu marasa ilimi, kuma sai an yi shirka sannan hakan ke tabbata. Kuma wannan ba abu ne me kyau ba, kwadayi da hangen wanda suka fika shi ke janyo hakan. Babbar matsalar sai ya tabbata an yi aure zama ya yi zama sannan za a fuskanci wulakanci saboda ba a gina shi akan sunna ba. Shawara ga masu aikata hakan su yi hakuri wallahi duk yadda ki ke mijinki yana nan ubangiji ya zaba miki.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: IyayeMata
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

Next Post

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Related

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu
Taskira

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

1 week ago
Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo
Taskira

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo

1 month ago
Taskira

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

2 months ago
Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
Taskira

Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba

2 months ago
Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu
Taskira

Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu

2 months ago
Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?
Taskira

Shin Ziyarar Bazata Zuwa Gidan Budurwa Daga Saurayi Na Bata Wa ‘Yanmatan Rai?

3 months ago
Next Post
Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

LABARAI MASU NASABA

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

July 12, 2025
Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

July 12, 2025
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

July 12, 2025
Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

July 12, 2025
Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

July 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

July 12, 2025
Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

July 12, 2025
Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista

Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista

July 12, 2025
Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi

Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi

July 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.