- Sana’ar Na Karfafa Ayyukan Bata-gari –Hukuma
- Wannan Shirin Zai Tsaftace Sana’armu –Shugaban Kungiyar
Hukumomin tsaro a Babban Birnin Tarayya Abuja sun fara farautar ‘yan kasuwar Jari Bola (dillalan shara).
Ko’odinetan Hukumar Kula Da Harkokin Birnin Tarayya Abuja (AMMC), Cif Felid Obuah, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da jami’an kasuwar fanteka a Abuja.
- Sam Ba Ni Da Labari Kan Abin Da Ya Faru A Unguwar Rimin Zakara – Abba Gida-Gida
- Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna
Obuah ya bayyana cewa an fara wannan shiri ne don inganta sa ido da ka’idojin ayyuka a duk kasuwannin pantaker da ke fadin FCT.
A cewarsa, aikin ya biyo bayan matakin da kwamitin tsaro na Babban Birnin Tarayya Abuja ya dauka ne a ranar 13 ga watan Janairu na dakatar da ayyukan duk kasuwannin Jari Bola na tsawon makwanni biyu.
“Kalmar ‘pantaker’ tana nufin kasuwannin da suka kware wajen sayar da kayayyaki na hannu da kayan tarkace, gami da kayan daki da kayan gida,” in ji shi.
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu barna a yankin.
Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya.
“Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu.
“Haka zalika za a bukaci masu gudanar da aikin su rike rajistar masu saye da masu kaya. Muna bukatar mu san su wanene masu samar muku da kaya kuma wa kuke sayarwa. Samun wannan bayanin zai taimaka a kokarinmu na tsaro,” Obuah ya kara da cewa.
Ya shawarci masu sana’ar pantaker da su guji yin mu’amala da wasu mutane ba bisa ka’ida ba ko sayen kayan sata, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da irin wannan kayan zai fuskanci kamawa tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
Obuah ya kuma kara karfafa gwiwar ma’aikatan da su hada kai a karkashin wata kungiya domin samar da ingantaccen hadin gwiwa da gwamnati da hukumomin tsaro.
Daraktan Sashen Tsaro na Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, Adamu Gwary, ya jaddada cewa masu sana’ar sayar Jari Bola ne kawai da aka sani za a yi musu bayani kuma a ba su izinin sake bude kasuwancinsu.
Ya umurci duk ma’aikatan da ba su yi rijista ba da su bi tsarin tantancewa kafin su ci gaba da aiki.
Da yake mayar da martani, Shugaban Masu Sana’ar Pantaker Operators na Kasa, Alhaji Abbas Bello, ya bayyana kudirin ma’aikatan na tallafa wa kokarin da suke yi na inganta sana’o’insu.
Ya yarda cewa akwai masu aikata laifuka a cikinsu kuma ya yi maraba da shirin a matsayin hanyar kawar da su.
Sakataren Kungiyar Malam Salisu Abubakar ya tabbatar da shirinsu na hada kai da jami’an tsaro domin yakar wannan barna a Babban Birnin Tarayya Abuja