Janye tallafi man fetur da aka yi a kwanan nan da kuma karya darajar naira sun shafi manya da kananan masana’atu da dama a Nijeriya, wanda hakan ya kai ga raguwar kudaden shiga da kuma matsalolin da suka shafi kudade gudanarwa.
Tunda aka janye tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu a shekarar 2023, farashin man fetur ta tashi kashi fiye da 193 abin da ya hargitsa tare da haifar da rudani a bangaren.
- Sin Ta Kulla Yarjejeniyar Tsarin Kafa Huldar Abota Ta Raya Tattalin Arziki Cikin Hadin Gwiwa Tsakaninta Da Kasashen Afirka 22.
- Hukumar Zaɓe Ta Jihar Kano Ta Rage Farashin Takardar Tsayawa t Takara
Lamarin ya fi shafar masu masana’antu ne saboda karuwar farashi man fetur da karuwar farashi kayan da ake sarrafawa ya haifar da tsadar kayan aiki gaba daya.
Rahaoto ya nuna cewa, kudaden haraji daga bangaren masana’antu ya yi kasa da fiye da kashi 70 a zangon farko na shekarar 2024, wanda ke nuna irin matsalar da bangaren masana’antun ke fuskanta.
Haka kuma karyewar darajar naira ya sanya shigo da yayakin daga kasashen waje ya kara tsada, abin da ya kara hauhawar farashi da nakasa abin da yake hannun masu saye da sayarwa.
Wannan ya kuma rage bukatar da al’umma ke yi wa kayyakin da aka sarrafa a masana’antu, hakan ya kuma kara karya bangare gaba daya. Masu fashin baki sun bayyana cewa, wadanan tsare-tsaren tattalin arzikin, wanda zai hana masu masana’antu samun riba a harkokinsu.
Ana matukar sukar gwamnatin Nijeriya a kan yadda ta aiwatar da wadannan tsare- tsaren ba tare da cikakken tattaunawa tare da nema jin ra’ayin al’umma ba, ba kuma tare da ta samar da wasu hayoyin rage wa masu masana’antu radadin da za su shiga ba sakamakon wadannan tsare-tsare na gwamnati ba, haka ya sa ake ganin rashin kwarewar mukarraban gwamanatin da kuma kwarwarsu a bangaren farfado da tattalin arziki.
A tsokacinsa, shugaban kamfanin Coleman Wires and Cables Industries Limited, George Onafowokan, ya kwatanta shekarar 2024 a matsayin shekarar da ba ta yi wa masu masaa’antu dadi ba, ya bayar da misali karyewar darajar naira, jaye tallafin mai da kuma rashin tabbas a bangare tattali arzikin kasa a mastayin matsaloli da za su ci gaba da cutar da masana’atu a kasar nan.
A tattaunawar da aka yi da shi, ya ce, wadannan tsare-tsare sun yi matukar shafar bangaren masu masana’antu a sassan Nijeriya tun a watan Mayu na shekarar 2023, ya ce, zuwa yanzu ana ci gaba da karya darajar Naira, yayin da janye talafin mai ya haifar da karuwar kudin sufuri ya kuma shafi dukkan bangarorin tattalin arzikin kasa.
A cewarsa babu wani da bai dandana sakamakon matsalar tattalin arzikin nan ba domin shekarar gaba daya ta zo a hagunce ga dukkan bangarorin tattalin arziki Nijeriya musamman bangaren masana’antu.
“Ci gaban harkokin kasuwanci a yau na bukatar jajircewa mai yawa saboda rashin tabbas a bangarorin tattalin arziki da dama,” in ji Onafowokan, ya kuma ce, rashin tabbas a farashin naira ya sa ba zai yiwu mutum ya yi tsare-tsare da hasashen ko kuma tsara harkokin kaswuancinsa ba.
Ya kuma karfafa masu masaa’antua kan karfafa fata dukda mastralo,I da ake fuskanta, y ace, in har aka ki karfafa fata to daga karshe za a kai ga rufe masana’antun ke nan.
Onafowokan ya kuma ce, ya kamata gwamnati ta bayar da umarni samar da bashi ga ,masu masana’antu ta hanyar Bakin Masana’anatu, ya ce wanann mataki ne da zai farfado da masana’antu da dama a fadin kasar nan.
Ya kuma nemi a rage wa masu masaa’atu harajin da suke biya akan kayan da suke shigo da shi wadanda suke sarrafawa don tabbbatar da masana’antu na ci ga da rayuwa duk da matsalar tattali arzikj da ake fuskanta.