A ranar Lahadi 11 ga watan Disamba 2022 ne Kungiyar Tuntuba ta yankin Funtua wadda aka fi sani da (Futua Consultative Forum) da ke Jihar Katsina ta gudanar da taronta na shekara-shekara inda ta karrama wasu fittatun ‘yan asalin jihar tare da kaddamar da Mujallar kungiyar mai suna ‘The Trumpet Magazine’, taron ya gudana ne a karkashin jagorancin Farfesa Abdulmunin Ibrahim.
A jawabinsa, shugaban kungiyar Dakta Zaharadeen Idris ya bayyana cewa, an kafa kungiyar ne a shekara 13 da suka gabata kuma cikin ayyukan da kungiyar ta fi ba karfi sun hada da bunkasa harkar ilimi, tattalin arzikin al’umma, kiwon lafiya, da horar da mata matasa sana’oin dogaro da kai, suna kuma cimma manufofin ne ta hanyar gudanar da gangamin fadakarwa inda suke gayyatar masana a bangarori daban-daban don su gabatar da mukaloli, suna kuma jagorantar nema wa matasa ayyukan yi a gwamatocin tarayya dana jihohi da ma kamfanoni masu zaman kansu.
Dakta Zaharadeen Idris ya kuma kara da cewa, a wannan shekarar sun samar da Mujalla wadda ta bayar da karfi wajen bayar da rahottanin irin cigaban da aka samu Jihar Katsina musamman ma a yankin Funtuwa, akwai kuma mukaloli na yadda al’umma za su bunkasa harkar kiwon lafiyarsu a dukkan matakai.
Taken taron na wannan shekarar ya yi bayani ne a kan yadda gwamnati za ta bunkasa harkar samar da kiwon lafiya musamman ga mata a ‘yankunan karkara.
Shugaban kungiyar ya kuma bayyana cewa, sun gayyaci tsohuwar shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya, NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman ne don ta jagoranci kaddamar da Mujallar su saboda yadda ta nuna kishin Jihar Katsina a lokacin da take a kan karagar shugabancin NPA.
Ya ce, ta samar da ayyukan cigaba da bunkasa rayuwar al’umma da dama a yankuna mazabun majalisar dattawa uku da ke a Jihar Katsina, ayyukan kuma sun hada da horar da matasa sana’oin dogaro da kai a garin Dangani na karamar hukumar Musawa, horar da mata hanyoyin tsaftace mjuhalli a garin Daura, samar da fittilun kan titi masu amfani da hasken rana a yankuna kananan hukumomin Musawa, Mutazu, Malumfashi, Kafur da Bakori haka an samar da irin wannan fitillun kan titi masu amfani da hasken rana na kananan hukumkomin Danja, Funtua, Kankara, Sabuwa da kuma Faskari.
Bayani ya kuma nuna cewa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta dauki nauyin horas da mata da matasa sana’oin dogaro da kai a kan Anan Dandume da Funtua.
A bangaren ilimi kuwa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta gina tare da yi wa wasu makarantu a sassan jihar kwaskwarima, wananna aiki ya shafi kusan dukkan kananan hukumomin Jihar gaba daya da kuma gyara asibitin masu fama da cutar yoyon fitsari da ke garin Babban Ruga ta Jihar Katsina.
Dakta Zaharadee Idris ya kuma tabbatar da cewa, Hadiza Bala Usman ta yi wadannan ayyuka kuma ga wannan yake son ganinsu yana iya zuwa garuruwan da aka zayyana don ya gane wa kansa, a kan nr kuma ya yi kra ga ‘yan asalin Jihar Katsina da suke rike da madafun iko a hukumomi da kamfanonin gwamnati a fadin tarayyar Nijeriya su jajirce wajen koyi da Hajiya Hadiza ta hayar samar da ayyukan cigaban ga al’umma Jihar.
A nata jawabin, Hajiya Hadiza Bala Usman, wanda ta samu wakilcin Tsohon Kwamishinan Fili da Safiyo na Jihar Katsina, Alhaji Abubakar Sada, ta nuna jin dadinta ne a kan ayyukan kungiyar, tana mai cewa, dole ta alakanta kanta da ayyukan kungiyar saboda yadda suka yi daidai da ra’ayoyinta na bunkasa rayuwar al’umma musamman mazauna yankunan karkara, ta ce, matasa na da matuka muhimmanci a kokarin bunkasa rayuwar al’umma musamman a wannan lokacin da ake fuskantar harkokin siyasa da zabubbukan 2023, a kan haka ta nemi Matasa su jajirce wajen ganin an gudanar da sahihin zabe su kuma gujewa shiga harkokin bangar siyasa da duk abin da zai kawo cikas ga zaman lafiya a jihar Katsina dama Nijeriya gaba daya.
Wadanda suka samu halartar taron sun hada da Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Malam Lawal Sani Matazu, Farfesa Abdulmumi A Ibrahim da Babban Sakatare a ma’aikatar kudi da tsare-tsare na Jihar Katsina, Alhaji Hassan Musa da mataimakan shugabannin kananan hukumomin Faskari, Funtuwa, Kafur, Bakori, Malumfashi, Musawa, Matazu, da Kankara sauran sun hada da shugabannin sassa na kananam hukumomin Kafur, Funtuwa, Bakori, Danja, Matazu, haka kuma taron ya samu halartar Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtuwa Alhaji Sambo Idris Sambo wanda magajin Makera ya wakilta da sauran manyan malaman addini da ‘yan kasuwa da manyan malaman jami’oi daban-daban.
A yayin kaddamar da mujjalar kungiyar mai suna ‘The Trumpet, Hajiya Hadiza Bala Usman ta kaddamar da mujallar a kan kudi Naira Miliyan daya, ta kuma nemi manyan ma’aikatan gwamnati da manya ‘yankasuwa su tallafa wa kungiyar musamman ganin akidunta da ayyukanta sun shafi tallafa wa al’umma ne.
Bincike ya nuna cewa, Hajiya Hadiza Bala Usman ta gabatar ire-iren wadanan ayyukan bunkasa rayuwar al’umma a sassan jihohin tarayyar Nijeriya, wanda hakan ke kara tabbatar da tsananin kishin kasarta.