A wani yunkuri da Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta bujiro da shi domin sake farfado da martabar aikin gwamnati, a ranar Litinin da ta gabata ne, Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abukar Labaran Yusuf ya girke kujerar a kofar shiga ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano domin shaida lokacin da kowa ke zuwa aiki.
Kwamishinan wanda daman an san shi wajen kokarin ganin kowa na yin aiki bisa gaskiya, ya bayyana cewa sake dawo da kima da kuma darajar aikin gwamnati na cikin kyakkyawan manufofin Gwamnatin Abba, don ya zama wajibi kowane ma’aikaci ya sake shiri, saboda gwamnatin ba za ta lamunci yin rikon sakainar Kashi da aiki ba.
- Ribadu Zai Shugabanci Taron LEADERSHIP Da NDLEA Kan Yaki Da Miyagun Kwayoyi
- Yanzu-yanzu: Everton Ta Dauki Ashley Young Daga Aston Villa
“Dole kowa ya sani alkawari ya dauka a lokacin da za a dauke sa aiki, bisa alkawarin yin aiki ba tare da yin kwange ba, ko makara a lokacin gudanar da aiki. Matukar mutun yana son cin halak dinsa, to ya zama wajibi ya tabbatar da zuwa aiki a kan lokaci, kuma kowa ya tabbatar da ganin sai lokacin tashi ya yi sannan zai tashi.”
Ya bukaci ma’aikatar ba tare da la’akari girman mukami ba da kowa ya yi wa kansa kiyamul laili wajen ci gaba da zuwa aiki a kan lokaci, sannan kuma kowa ya himmatu a kan aikinsa. A cewarsa, wannan gwamnatin ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.
Idan za a iya tuna Gwamna Abba a lokacin rantsar da sabbin kwamishinonin ya bayyana cewa zai sa ido kan kokarin kowane kwamishina tun daga lokacin da aka rantsar da su har zuwa watanni shida. Ya ce duk kwamishinan da ya gaza yin abin da ake bukata zai sauke shi.