Jama’a barkanmu da shigowa cikin wannan wata mai alfarma, wata mai girma, watan ibada, yadda muka fara azumi lafiya, Allah ubangiji ya sa mu kammala shi lafiya, Allah ya yafe mana kurakuranmu, Allah ya karbi ibadunmu, Allah ya sa muna daga cikin ‘yantattun bayinsa,amin.
Kamar kodayaushe shafin TASKIRA shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamntakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda azumin bana ya zo cikin tsadar rayuwa, ta yadda sauran al’umma ke kokawa game da wannan hali na kunci da tsananin rayuwa.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko ta yaya ya dace mutane su daidaita rayuwarsu da yadda azumin bana ya zo cikin tsadar rayuwa?, Wacce shawara ya kamata a bawa maigidanta, matan aure, samari da ‘yan mata?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hassana Muhammad, A Jihar Jigawa:
Da farko dai mutane su dora doron rayuwar su bisa karantar war addinin islama wajen ciyar da iyalansu, tufatar dasu, da sauran su, kamar yadda Allah (SWT) yace.
Mutane su cire duka abin da ba dole bane a cikin kasafin ƙudinsu na yau da kullum, su kuma gina rayuwa bisa gaskiya. Mutane su nisanci duka abin da zai gurgunta masu azumi ko kuma ya bata shi gabaki daya, su kauracewa yawan kallace-kallace, musamman ta kafofin sada zumunta, ba ko ina za su ke lekawa ba, domin ji, gani da zukata ababan tambaya ne, su lazamci karanta littafin Allah, zikiri, umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki da tausayawa talakawa, sai rahamar Allah ta yalwaci al’umma baki daya.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori A Jahar Jigawa:
To magana ta gaskiya dole al’umma su yi karatun-ta-nutsu a irin wannan lokaci na azumi duba da yadda tsadar rayuwa dama tsananin talauci ya addabi al’umma, dole al’umma a rage kashe-kashen kudi mara amfani domin ganin an yi azumin cikin nutsu da kwanciyar hankali, kuma ya kamata al’umma su daure suke taimakon masu karamin karfi a irin wannan lokaci da’ake ciki, domin hakan zai taimaka wajen a gudu tare a tsira tare. To shawara ta ga magidanta ya kamata a rage kashe-kashen kudi mara amfani domin kaucewa kure tanadin azumin da aka yi kafin azumin ya kare, don haka ya kamata abi a hankali, amma idan Allah ya kawo wadata to a iya yin komai har ma a taimakawa mabukata na kusa dana nesa, sai kuma matan aure su kuma ya kamata su yi hakuri da kadan idan aka kawo kuma su yi tattali da tsumi domin hakan zai taimaka wajen ganin an samawa magidanta sauki, sai kuma samari da ‘yan mata su kuma ya kamata a tashi tsaye a taimakawa iyaye da ‘yan uwa irin wannan lokaci da ake neman lada a wata mai alfarma, samari a taimakawa iyaye da daukar dawainiyar gida. Su kuma ‘yan mata a taimakawa iyaye mata da aikace-aikacen cikin gida.
Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Naija:
Mutane su daidaita rayuwarsu akan azumin daya zo cikin tsadar rayuwa, gaskiya abun zai dan yi wuya sabida ana cikin wani yanayi, wasu dan ‘ya’ya, idan kai ka yi hakuri ka daidaita rayuwarka, ‘ya’ya su ba su san haka ba, yaya za ka yi da su?, za su iya shiga wani hali, a wannan halin da ake ci ya kamata gwamnati ta taimaka saboda akwai mabukata da yawa, fiye da yadda ba a tunani. Shawarata ga maza da mata da matan aure da magidanta shi ne; Su yi hakuri a duk in da ka tsinci kanka, ka yawaita istigfari da hailala da sauran addu’o’i zuwa ga mahaliccinka, shi da ya halicce ka shi zai ba ka mafita in Allah ya yarda, kana zaune sai ka ga wata hanya ta zo maka ta in da ba ka tunani, fatanmu Allah ya sa a gama azumi kafiya.
Sunana Abubakar Usman Malam Madori A Jihar Jigawa:
Abubuwan daya kamata mutane su duba a wannan lokaci musamman yanzu da azumin watan Ramadan mai alfarma ya gabato mu, ya zama wajibi mu sassauta kashe kudi da duk abubuwan da basu zama dole a gare mu ba, da kuma tattala duk dan abun da muka samu wajen sarrafa shi da yin abun da ya dace. Ya kamata iyayenmu mata su dinga karbar dan abun da suka samu daga wajen magidantansu suna saka mai albarka duk kankantarsa kuma su samu wata ‘yar sana’a su dan gudanarwa domin a gudu tare a tsira tare, domin hannu daya ba ya daukar jinka, sai ka ga an wuce wurin da taimakon. Su kuma ‘yan uwana matasa su yi karatun-ta-nutsu wajen tallafawa iyayensa, ta hanyar samun sana’a duk kankantarta, kuma yana taimakawa iyayensa da duk dan abun da ya samu, sai Allah ya sanyawa abun albarka, maimakon ya je yana kashewa ‘yanmata kudi ko kuma dauko rayuwar da ta fi karfi sa, ta fi karfin samunsa, ko kuma kallon abubuwan da abokansa suke kashewa ya ce lallai shi ma sai ya yi irin wannan rayuwar wannan ba hanya ba ce mai billewa domin Hausawa suna cewa; “idan ba ki da gashin wacce, kar ki ce sai ki yi kitson wacce” domin yin hakan babu abun da ya ke haifarwa face dana-sani, haka idan ka dauko rayuwar ‘yan matan ma a halin yanzu hakan abun yake su ma mafi yawancinsu ba sana’a suna zama nauyi ga iyayensu kuma suna daukowa kansu abun da ya fi karfinsu musamman ta fuskar sutura da sauran abubuwan more rayuwa.
Sunana Hassana Sulaiman Hadejia A Jihar Jigawa:
To gaskiyar lamarin nan dai gameda yadda al’umma za su dai-dai ta rayuwar su, musamman cikin watan nan na ramadana da muka fara yinsa cikin ikon Allah da amincewar sa, da kuma yardarsa shi ne akwai wasu abubuwan kan da ya kamata ace duk wani wanda ya riske shi zai yi kama daga ibadar ita kanta, taimakawa juna da ‘yan’uwa da duk wasu mabukata ma. Kuma dai yanayin da mutane za su iya yinsa dan daidaita rayuwar su wajan samarwa da kansu nustuwa da walwala da kuma yin ibada yadda ya dace, shi ne mutum da farko ya fara tsarkakewa niyyarsa da zuciyarsa da komawa zuwa ga ubangiji sai kuma yin kokarin nisantar yin sabo cikin yanayin azmumin, dan gudun kada ka yi kishin ruwan banza ta hanyar sabawa ubangiji dan ka tsinci kanka cikin yanayin damuwa da kunci, talauci, matsin rayuwa. Mutane kada ku yi amfani da wannan yanayi wajan cutar da juna, karku fake da yanayin nan na tsadar rayuwar da ake ciki ku jefa kanku ga halaka, yayi ba, ya kamata yayi ko kuma wajan ubangiji ku roke shi ya yaye muku. Shawara zuwa ga ‘yan’uwa magidanta, matan aure, samari da ‘yan matan, anan shi ne matsayinka na magidanci dole ne tun farko ka zama tsayayye cikin gidanka, kuma ka zamo mai nuna musu samunka da rashinsa, su kuma matan aure su yi hakuri da yanayin nan suna yi wa mazajensu addu’a da hakuri da kadan, samari ku zama masu taimakawa iyayenku idan kuna da shi, ‘yan mata ku daina dorawa samarinku bukatar da tafi karfinsu,
Allah ya kawo mana saukin rayuwar nan.
Sunana Babangida Danmama Malam Madori Jihar Jigawa:
Yanada kyau iyaye mata su rika hakuri da duk abun da magidanci ya kawo gida a matsayin kayan buda baki, duba da yadda aka tsinci kai cikin yanayi na tsadar rayuwa. Sannan yana da kyau iyaye mata su kara zage damtse wajen tattalin abun da miji ke kawowa, idan suka yi la’akari da faman da maza ke sha wajen ci da gida a yanzu. A wannan wata na azumin Ramadan da za a shiga yana da kyau magidanta ko ya yake su dage da ciyarwa, domin neman samun sauki kan wannan hali da aka tsinci kai daga wurin Allah.
Sunana Asma’u El-kabeer (Husna) daga Jihar Kaduna:
Yadda mutane ya kamata su daidaita rayuwarsu musamman yadda azumin bana ya zo cikin tsadar rayuwa shi ne; maigidanta su daina takura kansu kan abin da ba su da shi su ceallai sai sun yi. Su ma ‘yan mata ya kamata su san cewa rayuwa ta canja kar su rinka ganin kamar rayuwar daya take da ta baya, idan sun ga abin da ba a yi musu shi a wadace ba, to su yi hakuri kuma kar su kai kansu in da Allah bai kaisu ba, kar su bata rayuwarsu dan biyan bukatunsu, musamman wajen tafiya sallar ashaan ya kamata mutum ya san me ya dace da shi, ya kuma san ibada ya je. Kn kowa ya san tsadar rayuwa, kyautatawa ce kawai tsakanin masoya, amma bai zama dole ba sai mutum yayi ba. Allah ya sa mu dace amin. Shawarar da zan bawa magidanta, samari da ‘yan mata shi ne; kada su ce sai sun yi abun da gidan wane da wance suka yi in sun saba a baya yanzu ba fa daya bane, domin wallahi komai ya canza misali; in kun saba yin sadaka shekarun baya da suka wuce wannan shekarar in ta zo a lokacin da iya rufin asiri ne da ku kar ku ce lallai sai kun yi.
Sunana Usman Adamu Malam Madori A Jihar Jigawa:
Shawara ga magidanta, matan aura, samari da ‘yan mata, wannan shawara ce ga dukkan wani musulmi domin mun shigo watan alfarma da neman kusanci ga Allah (swt), to ta ya ya za mu samu kusanci da Allah (swt) shi ne, yin biyayya ga dukkanin abin da ya ce a yi, sannan da kin yin abin da ya yi hani da shi, Allah ya ba mu damar yin biyayyar, amiin. Sannan ina ba mu shawara game da yin sallar tarawee wato (asham), falalar sallar tarawee (asham) daga Aliyu dan abidalib R.A cewa shi ya ce; an tambayi Annabi (saw) dangane da falalolin sallar tarawee a cikin watan ramadan sai ya ce; mumini yana fita daga zunubansa a farkon daren kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi, a dare na biyu za a gafarta masa da iyayansa in sun kasance muminai.