Bayan an samu tsaikon jinkirta wa’adi har sau bakwai, a karshe dai matatar man Fatakwal ta fara aikin tace danyan mai kamar yadda LEADERSHIP ta ruwaito Bincike ya nuna cewa matatar mai ta Fatakwal ta rasa wa’adin har sau bakwai na fara aikinta a zuwa watan Oktoban 2024.
Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya sanya ranakun fara aikin matatar, ciki har da alkawuran da aka yi a watan Maris, Agusta, da Satumbar 2024, wadanda duk sun wuce ba tare da cika wannan alƙawari ba.
- Man Fetur Da Ake Shigowa Ya Ragu Da Kashi 35 – CBN
- Dangote Ya Rage Wa ‘Yan Kasuwa Farashin Man Fetur
Sai dai a wani sako daga wata majiya mai tushe, wadda LEADERSHIP ta ci karo da shi, NNPC ya ce, “A yau (Talata) babbar nasara ce ga Nijeriya yayin da matatar man Fatakwal ta fara aikin sarrafa ɗanyen mai a hukumance.
Wannan gagarumin ci gaba ne na bude sabon babi na samun ‘yancin kai a vangaren makamashi da ci gaban tattalin arzikin al’ummarmu.
“Ina taya Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da hukumar gudanarwa ta NNPC karkashin shugabancin, Mele Kyari bisa jajircewar da suka yi wajen wannan aikin na kawo sauyi.
Sannu a hankali muna sake fasalin makomar makamashin Nijeriya.” An fara gyaran matatar mai ta Fatakwal ne tun a shekarar 2021. Dan kwangilar da ke kula da aikin, Maire Tecnimont SpA, ya kasance yana aiki a wurin tun lokacin da aka sanya hannu kan kwangilar na dala biliyan 1.5 a cikin watan Afrilu 2021.
Duk da sanarwar kammala aikin a watan Disamba na 2023, matatar ba ta fara aikin tace mai ba, saboda abin da NNPCL ta kira, “ci gaba da binciken tsaro da jinkirtawa wani matakin ƙarshe na gyaran.”