Wasu matuka jirgin saman kamfanin Ehiopian Airlines biyu sun yi sabi-zarce har zuwa koluluwar da aka daina jin duriyarsu bayan bacci ya kwashe su.
Rahotanni sun ce masu kula da jiragen sama a filin jirgin saman da ke Habasha sun yi ta kokarin kiransu a waya to amma ina sun ringa sun kai kololuwar da ba za a iya samun su ba.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 69 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Bauchi
- Kotu Ta Garkame Maigadi Kan Zargin Sace Kadarorin Miliyan 1.8 Na Jami’a
Bayan da kararrawar jirgi ta tashe su, sai suka yi kokari suka sauka a yunkuri na biyu.
Jirgin dai ya tashi ne daga filin jirgin saman Khartoum a Sudan.
Jirgin samfurin Boeing 737, mai daukar fasinjoji 154, na shafe kasa da sa’oi biyu ne idan zai je kasashe makwabta.
Mutane da dama ne dai suka bayyana mabambantan ra’ayoyi a kan barcin matuka jirgin a yayin aiki in da wasu suka tausaya musu tare da cewa aiki ne ke musu yawa shi ya sa barci ya kwashe su, wasu kuma sun mayar da abin raha har suna wallafa wa a shafukansu na tiwita cewa barci a yayin aiki ya kai matuka jirgi kuloluwa.
Masu sharhi kan al’amuran da suka shafi zirga-zirgar jirage sun bayyana matukar damuwarsu kan afkuwar lamarin a shafukansu na tiwita.
Bai dai aji ta bakin kamfanin jirgin ba har yanzu.