Baban mai taimaka wa shugaban ƙasa a kan harkokin siyasa, Hon. Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana dalilan da ya sa suka shiga suka fita shi da gwamna Dikko Raɗɗa aka soke aikin sake gina hanyar kankara zuwa Katsina daga hannun ɗan kwangilar.
Masari, ya yi wannan kalamai ne a Katsina a lokacin bikin raba shinkafar da gwamnatin tarayya ta bai wa Jihar Katsina domin raba wa al’umma su rage raɗaɗin rayuwa da ake fama da shi.
- Ya Kamata Wike Ya Kyale Ribas Ta Zauna Lafiya – Fubara
- An Kashe Dorinar Ruwa A Jihar Kebbi Bayan Ta Kashe Mai-Gadin Lambun Basarake
Wannan aikin hanyar mai tsawon kilo mita 170 da ta taso daga marabar kankara zuwa Katsina ta haɗa ƙananan hukumomi bakwai da yawansu manoma ne sannan suna fuskantar matsalar tsaro daga ‘yan bindiga
Kamar yadda alkaluma suka nuna aikin wannan hanya zai ratsa kananan hukumomi guda 7 da suka haɗa da Malumfashi da Kankara da Ɗanmusa da Safana da Dutsinma da Kurfi da kuma Ɓatagarawa a Jihar Katsina.
Lokaci da aka ba da aikin wannan hanya al’umma da dama sun nuna farin cikinsu da samun wannan aiki wanda suka bayyana cewa zai taimaka wa al’umma musamman manoma sannan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen kai ɗauki a yayin da aka kai hari wuce gona da iri.
Sai dai kwatsam aka ji labarin ministan ayyuka na Nijeriya ya soke wannan kwangila daga hannun kamfanin da aka bai wa ita daga farko duk da cewa an fara aikin.
Shi ma a nasa jawabin babban mai taimaka wa shugaban kasa a harkokin siyasa Hon Ibrahim Masari ya bayyana wasu hanyoyi da gwamnatin tarayya ta bada aikinsu, sai dai ya ce hanyar kankara zuwa Katsina ba a ɗora ƙwarya a gurbinta ba shi ya sa suka je wajen shugaban ƙasa domin ya soke ta.
Ana dai zargin cewa wani jigo ne a jam’iyar PDP a Katsina kuma ɗaya daga cikin yaran Ministan Abuja, Nyesom Wike aka bai wa kwangilar aikin hanyar tun farko, lamarin da bai yi masu daɗi ba, inda suka shiga suka fita aka dakatar da aikin, wanda yanzu ba a san matsayin da aikin hanyar yake ciki ba.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko shugaban ƙasa zai sake ba da aikin hanyar a wani kamfanin da gwamna Dikko Raɗɗa da Hon. Ibrahim Kabir Masari suke so ko kuwa shike nan ruwa ta sha?