Wani sabon salo da bindiga ke amfani da shi wajen tursasawa, gallazawa da kuma bautarwa shi ne, yadda a halin yanzu suke mamaye kauyuka tare da mallake a’ummar yanki gami da duk abin da suka mallaka.
Duk kauyen da suka mamaye to zai zamo duk abin da jama’ar wannan gari suka mallaka ya zama nasu daga kan dabbobi, gidaje abinci, abin hawa kai har ma da matayensu na aure da ‘ya’yansu mata.
- Matar Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar Da Bada Tallafin N50,000 Ga Mata Dubu 4 A Gusau
- Majalisar Wakilai Ta Nemi A Cefanar Da Sufurin Jirgin Kasa
Mazauna yankin Karamar Hukumar Faskari da ke Jihar Katsina sun ce ‘yan bindigar sun kwace gonakin jama’a, tare da tilasta wa mutanen garuruwan yi masu shuka da huda da ma sauran ayyukan gona.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaida wa BBC Hausa cewa ‘yan bindigar suna shiga kauyuka kuma su yi abin da suke so, kuma a lokacin da suke so.
Ya ce ‘‘A yanzu maganar da ake a cikin firamare din Kogo ‘yan bindiga ne a ciki zaune, in an yi abinci a kai masu, in suka ga yarinya su dauka, in kuma ka yi magana su kashe ka.’’
Mutumin ya ce mazauna yankin suna biyayya ne ga ‘yan bindigar saboda ba su da wani zabi na daban.
‘‘Tashin farko dai suka sa aka hada masu kudi cikin yarjejeniyar da aka yi, da kuma gonakin da suka ware wadanda ba za a noma ba, su za a nomawa. Duk lokacin noma za mu je can, mu yi masu noma, mu yi masu huda, su fada mana abin da za a noma, mu yi noma kuma idan lokacin girbi ya yi mu kwashe mu ba su.
Sun maida mu tamkar bayi a cikin wannan yanki, idan ka yi kaifi a hukunta ka’’
Ya ce kauyukan yankin da suka hada da Birnin Kogo da Yar-tsamiya da Kahi da Fankama da Hayin Dungu da kuma Gobirawa duk karkashin ikon ‘yan bindigar suke, wadanda ke ci gaba da muzgunawa jama’a.
Dakta Nasir Mu’azu, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Katsina ya ce gwamnatin jihar ta farga da wannan lamari.
‘‘Mutane a irin wadannan kauyuka sun je sansanin ‘yan gudun hijira, to kuma wasu da yawa ba za su iya hakuri da zaman sansanin ba don haka sai suka koma kauyukansu, suna ci gaba da zama bisa ga yadda ‘yan bindigar suke ta gallaza masu’’
Dakta Nasir ya ce gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda yana aiki tukuru don kula da mutanen da matsalar tsaron ta tilasta masu yin hijira da kuma tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Gwamnatin Jihar Katsina dai ta lashi takobin magance matsalar tsaro da ta dabaibaye garuruwa da kauyuka da dama na jihar. Kuma ko a kwanan nan sai da ta kaddamar da rundunar sintiri ta farar hula don taimaka wa wajen tabbatar da tsaro.