Sallah karama, ibada ce da Musulmi ke gabatar da ita bayan kammala Azumin Ramadana, Sallar da wasu kuma ke kiranta Sallar ado, ta yadda za a ga kowane magidanci ya yi iya bakin kokarinsa na ganin ya faranta wa iyalansa ta hanyar yi musu dinkin kayan sawa domin fita kunya, da kuma shirya kayan abinci na musamman wanda sai a irin wannan rana ake sayensu.
To sai dai a wannan shekarar duk wanda ka kusanta sai ka ji yana kukan halin kuncin rayuwa da yadda al’amura suka lalace ta fuskar tattalin arziki, abin da mutum ya saya a shekarar da ta gabata a yanzu a kasuwa ya ninka sau uku. Wasu duk da halin da ake ciki sun yi iya kokarinsu wajen ganin sun yi wa ‘ya’yansu abin da ba a rasa ba. kafi a zo wannan yanayin magidanci yakan hakura da yi wa kansa dinki ya yi wa ‘ya’ya da matarsa, amma a wannan yanayin iyayen ne gaba daya suke hakuri da dinka kaya a yi wa yara, maganar abinci kuwa sai abin da aka gani.
- Azumi Lokaci Zafi: Yadda ‘Yan Kasuwar Kankara Ke Camamarsu A Yobe Da Zamfara
- Tsaraba Ga Amaren Bayan Sallah Da Masu Niyyar Aure
Wannan ta sa LEADERSHIP HAUSA ta zagaya wasa sassa na Abuja domin jin ta bakin wasu daga cikin mutane inda suka fadi albarkacin bakinsu. Muhammad Banufe wani mazaunin garin Mararraba ne da ke Jihar Nasarawa, cewa ya yi shi a yanzu, ba ya tunanin yin abinci da nama domin a yanzu kazar gidan gona kwaya daya ana sayar da ita Naira dubu 13, don haka shi ya hakura da yin abincin Sallah da nama.
“Yanzu fa kudin Zobo shi ne ya zama kudin shinkafa, kawai ka je ka sa a yi maka tuwon shinkafa miyar wake ka ci kawai ka hakura lamarin ya fi karfin tunaninka,” in ji shi.
Haka shima malam Haruna wani mazaunin cikin Abuja cewa ya yi a halinzu da rayuwa ta yi tsada ana kokarin abin da za a ci ne kawai dinki kuwa sai dai a yi wa yara su sa shi ma don kada yaro ya yi ta yi maka kuka ne. “Yanzu an samu canji sosai abubuwa sun ninka sau uku, abin da Naira dubu 10 za ta yi maka a shekarar da ta gabata yanzu sai ka sa Naira dubu 30, yadin da talaka zai saya wa dansa Naira 700, yanzu fa Naira 3000, to haka na 10,000 shi ne ya koma 30,000,” in ji shi.
Haka nan wani matukin KEKE NAPEP da bai bayyana sunansa ba cewa ya yi, a shekarar da ta gabata Naira dubu 13 ne suka isa ya sayi yadin da ya dinka wa ‘ya’yansa kayan Sallah su uku, amma a wannan shekarar dan karanin dansa ne ya cinye Naira dubu sha ukun shi kadai a dinkin ban da maganar takalmi da hula.
Wani matashi kuwa da ko aure bai yi ba cewa ya yi, dyk ba shi da aure amma yana tausayin masu iyali, saboda duk da ba shi da ‘ya’ya ya san masu ‘ya’ya suna fuskantar kalubale. “To ai gani na yi daga ni sai cikina amma ka duba yadda nake fama, koda yake na yi wa Allah godiya ina da iyaye kuma ina taimaka musu, amma da na duba kudin da na kashe wajen yi wa kannena kayan Sallah da abin da na saya na abin da za a ci sai na ga lallai magidanta suna cikin halin ni ‘ya su. tunanin da na yi shi ne da kuma a ce ba ni da shi fa yaya zan yi, sannan kuma magidantan da basu da shi kuma yaya za su yi?” in ji shi.
Sau da dama Sallah karama ko babba ta kan samu al’umma musamman talakawa a irin wannan yanayi amma ba a taba shiga halin matsin rayuwa kamar wannan lokacin ba, rayuwar talaka dai a wannan lokaci sai dai addu’ar Allah ya kawo dauki.