Mutuwar tsohon kwaminisan yada labarai na Jihar Neja, Danladi Ndayebo da mashawarcin shugaban majalisar dattawa, Mohammed Isa ta fallasa lalacin kayayyakin lafiya a fadin jihar.
Abokan guda biyu sun samu mammunan hatsarin mota a kan hanyar Minna zuwa Suleja na Jihar Neja.
- INEC Ta Roki ‘Yan Jarida Da Su Kauce Wa Labarai Da Dumi-Dumi Da Zafafan Kanun Labarai Don Jawo Hankali
- Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin Kungiyar APEC Karo Na 29
Rahotonni sun bayyana cewa sun mutu ne sakamakon sakacin jami’an lafiya da karacin kayayyakin aiki na bayar da agajin gaggawa da wadanda suka raunata.
Danladi ya mutu ne a ranar Litinin, yayin da Mohammed ya mutu a ranar Juma’a a cikin mako guda.
Kanin Danladi mai suna Usman Mohammed Ndayebo ya bayyana wa jaridar Daily Trust cewa dan’uwansa tare da Mohammed ba a ba su kulawa yadda ya kamata ba lokacin da suke asibitin koyarwa na IBB da ke Minna har na tsawon awanni 13 da faruwar hatsarin. Ya ce allura kadai aka yi musu domin kashe zafin ciwon jikinsu bayan awanni hudu da suka isa asibitin.
Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da samun rahoton cewa mamatan guda biyu ba a ba su kulawar da ya kamata ba lokacin da aka kawo su asibitin.
“Na samu kiran waya da safe, inda aka shaida mun cewa Marigayi Ndayebo da wani majinyaci an garzaya da su asibitin koyarwa na IBB a cikin dare, amma abun takaici har zuwa da safe da aka kira ni babu wani likita da ya duba majinyatan.
“Babban abun takaicin shi ne, washagarin da safe lokacin da aka zo duba shi aka tarar ya mutu,” in ji Matane.
Ya ci gaba da cewa gwamnati ta damu da abun da ya faru na sakaci a asibitin gwamnati wanda bai kamata a samu irin hakan ba. Ya ce gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya bayar da umurnin gudanar da sahihin bincike game da musabbabin mutuwar Ndayebo, a ga ko sakacin ne na jami’an asibitin koyarwa na IBB ko kuma rashin kwarewa ne.
A cewar bincike, mafi yawancin majinyata ciki har da mata masu juna biyu sun mutu a asibitin sakamakon karancin ma’aikata da za su gudanar da ayyuka, musamman ma ga wadanda suke bakatar kulawar gaggawa.
An dai bayyana cewa a wasu asibitocin, nas guda daya ke duba mara lafiya sama da 20 a cikin dare lokacin da karancin likitocin suka tashi daga aiki.
Idris Mohammed, wani majinyaci da aka kai shi babban asibitin Minni bayan samun hatsari ya ce ya fuskanci irin wannan lamari a can.
“Ina iya tuwa cewa an bukaci mu sayi safar hannu, amma muka ki wanda ya sa ma’aikatan jinyar suka dauki tsawon lokaci ba su duba ni ba. An dauki kwanaki biyu kafin likita ya duba ni. A duk lokacin da dan’uwana ya bukaci ganin likita, sai a ce masa lambarsa ba ya shiga,” in ji shi.
Binciken Daily Trust ya gano cewa likitoci guda hudu ne ke aiki a asibitin Jummai Babangida Maternal and Neonatal Hospital. Binciken ya bayyana cewa likitoci 500 ne a fadin jihar, amma likitoci guda 39 da ma’aikatan lafiya 800 sun gudu gaba jihar a cikin shekaru biyu.
Haka kuma binciken ya gano cewa a yanzu haka likitoci guda biyu ne kacal a babban asibitin Mokwa, yayin da a babban asibitin Bida akwai likitoci hudu, sannan a babban asibitin Kutigi akwai likita daya, a babban asibitin Agaie akwai likitoci uku, inda a babban asibitin Lapai akwai likitoci biyu, haka kuma a babban asibitin Kuta akwai likitoci biyu.
Haka kuma a babban asibitin Kafin-Koro da babban asibitin Tunga-Magajiya da babban asibitin Bangi da kuma babban asibitin Nasko dukkansu likita daya kowannansu yake da shi, yayin da a Auna da Gulu suke da likitoci biyu-biyu.