Da yawan wasu mutanen sun iya sana’o’i daban-daban, sai dai akan same su da rashin maida hankali, kiwa, rashin iya tafiyar da kasuwanci da raina sana’a, ke sa su faduwa a cikin al’amuran sana’o’insu.
Wanda a ganinsu yin karamar sana’a ba tasu ba ce, domin sun wuce ajin yin karamar sana’a kaskanci ne a gare su, sun fi son manyan sana’o’i, ko da kuwa sun kware da kananun sana’o’in, sun gwammace su yi ta zaman jiran babbar sana’a, wanda hakan ke sa su yin da sun sani watan watarana.
Sabanin wadanda ba su iya sana’a ba, masu kokarin koya ta kowacce hanya, sukan maida hankali su koya ko da kuwa wasu nasu ba su taba yin irin sana’ar ba, wanda kuma hakan yakan zamo musu babbar riba a gaba.
Kwararriyar bakuwarmu wadda ta kware a fannin zanen fulawa na jan lalle (Jan kunshi) FATIMA YA’U ADO ta bayyana wa masu karatu irin gwagwarmayar da ta sha wajen ganin ta koyi yadda ake yin sana’ar kunshin. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA Kamar haka:
Ya sunan Malamar?
Sunana Fatima Ya’u Ado an fi kirana da Teemah.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Da farko dai kamar yadda na fada sunana Fatima Yau Ado, kuma an haife ni ne a garin Kano, Unguwar Kawon Mai Gari. Nayi Firamare dina a ‘EL- Litinin Learning Feals’ dake Giginyu, na yi Sakandare dina a makarantar ‘Yan Mata dake Giginyu, sannan na tafi ‘College of Health’
A yanzu kina ci gaba da karatu ne ko aiki ko kuma wata sana’a?
A’a! ban ci gaba da karatu ba, sai dai ina zuwa aiki matsayin ‘Temporary’, Sannan ina yin sana’a.
Kamar wacce irin sana’a kike yi?
Ina sana’ar lalle ne.
Kamar wanne irin lalle kenan?
Jan lalle nake yi, irin wanda za ki ga ana jera masa salatif.
Me ya ja hankalinki har kika karkata ga sana’ar Kunshi?
Kawai na tsinci kaina a ciki ne kuma abin na burge ni.
Lokacin da za ki fara sana’ar kunshi, kin nemi taimakon wani ko wata wajen koya, ko kuwa akwai wata makaranta da aka ware dan koyar da sana’ar, ko da kanki kawai kika ga kin iya, ya abin yake?
Ban nemi taimakon kowa ba, kawai na gwada sai na ga ina yi.
Farkon da za ki fara ya abin ya kasance?
Na fara shi ne a kafar kannena, tun ina yi musu ba ya yin kyau har na saba.
Ya farkon fara yin sana’ar ya kasance, kamar yi wa wasu na waje ba na gida da kika saba yi wa ba?
Da farko na fara ne da ‘yan gidanmu idan na yi musu, sai kawayensu suka fara zuwa nake yi musu har takai ta kawo yanzu ake zuwa daga ko ina ma na wasu unguwannin nake yi musu.
Za ki kamar shekara nawa kina wannan sana’a?
Zan yi kamar shekara uku ina yi.
Me ya fara ba ki wuya lokacin da za ki fara yin kunshin?
Abin da ya fara ba ni wuya shi ne; wajen yanka salatef da kuma fitar da fattan dizayan gaskiya kan na iya na sha wuya sosai.
Za ki ga wasu sun iya lallan amma za su ce su ba za su yi ba sabida bata waje da yake yi, me za ki ce akan hakan?
Eh! toh ni dai gaskiya idan na ce zan yi wa mutum lalle ina cika alkawari ina yi musu, sai dai idan na gaji shi ne. Kuma idan ka kwaba shi kafin kwastoma su zo za ka yi shi tsaf! ba tare da ka bata wajen ba.
Za ki ji wasu sun ce ba a kwaba lalle ya jima kafin a zo yinsa kamar yana sikewa, ko kuwa fadar mutane ce kawai?
Eh! ya danganta da wasu, amman baya komai sai dai idan ka kwaba ya dade sosai shi ne yake sikewa.
Kina iya yi wa mutane kunshi kamar mutum nawa a rana?
Ina iya yi wa mutane da yawa, ya danganta da samun lokacin da ba zan fita ba, tun da ina fita aiki, amma a rana ina yi wa kamar mutum takwas ko sama da haka.
Ya kika dauki kunshi a wajenki?
Na dauke shi sana’a mai kyau sosai.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta game da sana’ar kunshi?
Eh! lokacin dana fara kafin na iya na sami kalubale a wajen kwastoma, amman yanzu ya huce.
Ya batun nasarori fa?
Gaskiya na sami ci gaba mai yawa sosai, wanda ba sai na fada ba, sai dai na ce Alhamdilllah.
Ko akwai wadanda kike koyawa kunshi a yanzu, ko kuwa sai nan gaba kike da burin koyarwa?
A’a gaskiya, Ina da dai burin koyarwa a nan gaba.
Mene ne burinki na gaba game da sana’arki ta kunshi?
Burina na ga na bude babban ‘shop’ da zan rinka yi.
Idan mutum yana so ya zo ki yi masa kunshi a ina zai iya samunki?
Zai sameni ne a gidanmu dake kawon maigari, opposite ‘Aunty Merry College’ da ke garin Kano, duk wanda aka tambaya gidan mu za a kai shi, ko kuma a tuntube ni ta lambata.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi a rayuwrki ba?
Ba zan taba mantawa da wannan bakar nanar ba, ranar da mahaifina ya rasu na shiga bakin ciki sosai.
Shin Malama Fatima tana da aure ko babu?
A’a! ba ni da aure
Yaushe za ki aure?
Nan da wani lokaci kadan ba da dadewa ba In sha Allah.
Idan kika ga mata marasa sana’a ya kike ji cikin ranki?
Ina jin ba dadi, domin yanzu ba a zama ba tare da sana’a ba.
Wacce shawara za ki bawa sauran mata na gida masu jiran miji?
Shawarar da zan ba su shi ne idan sun sami mai sonsu tsakani ga Allah to su yi saurin dai-daitawa da su, soyayya babu inda za ta je musu duk kyawun mace gidan mijinta.
Wanne kira za ki ga sauran mata na gida marasa sana’a?
Su tashi su nemi sana’a domin rufin asirinsu ba sai abin da mijinsu yayi musu ba, ku taimaka musu dan rayuwar ‘ya’yanku ta inganta.
Wanne kira za ki ga sauran Mata masu zuwa yin kunshi?
Toh! dai shi wannan kunshin Ado ne ga Mace, kuma an san mace tana yawaita ado a gidanta ne ko a gidansu dan yawancin maza suna son mace ‘Yar kwalliya.
Me za ki ce ga makaranta wannan shafi na Ado da Kwalliya?
Ina yi musu fatan alkhairi, su ci gaba da bin wannan shafi da kuma daukar darasin da ke cikinsa musamman na koyar sana’a domin a gudu tare a tsira tare.
Me za ki ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa?
Ina yi wa wannan gidan Jarida fatan alkhairi, Allah ya kara daukakata, ya kara basira ga ma’aikatan gidan Jaridar.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina mika godiyata ga Allah da yayi min baiwa, Alhamdillah, ina mika godiyata ga iyayanena da suka taimaka min har na kai wannan mataki, da ‘yan uwana ‘Brothers & sisters’ da ‘Friends’ dina.
Muna godiya Malama Fatima
Ni ma na gode.