A yau shafin ya yi tozali da wata matashiyar marubuciya mai suna MARDIYYA LAWAN wadda a kafi sani da AUTAR GOGGO, inda ta bayyana wa masu karatu batutuwa masu yawan gaske da suka shafi farkon fara rubutunta har ma da irin gwagwarmayar da ta sha bayan ta tsinci kanta cikin marubutan littafan Hausa na yanar gizo, da ma sauran batutuwa masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da RABI’AT SBS (BIG GAL) Kamar haka:
Ya sunan marubuciyar?
Sunana Mardiya Lawan, amma da yawan mutane sun fi sanina da Preety Mardy wasu kuma Autar Goggo.
Ko za ki iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Kamar yadda na fada a baya sunana Mardiya Lawan, ni haifaffiyar garin Lagos ce a nan na taso nayi rayuwata har zuwa yanzu. Nayi karatun ‘Nursery’ da ‘Primary’ har ‘Secondary School’ a nan Lagos sannan na tafi Sokoto inda nayi NCE dina a ‘Shehu Shagari College Of Education’.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutce-rubuce?
Tun ina firamare ina da son karance-karance sosai, daga wannan lokacin sai na ji ina ma a ce ni ma zan iya rubuta nawa littafin? Daga wannan lokacin ne kuma dana dan samu lokaci sai na fara tsara labari. Haka dai nake yi kodayaushe in na samu dama zan fara rubutawa, kuma hakan bai hanani karance-karance ba duk da inada karancin shekaru. A haka bayan na gama makarantar sakandare sai yayata ke cewa “Mardiya ya kamata ki rubuta mana labari”, sai nake ce mata gaskiya ba zan iya ba rubutun labarin online ba kamar wanda mutum zai rubuta a littafi bane, sai take cewa “ai ba lokaci daya za ki saki ba ‘Page By Page’ za ki rika yi kamar yadda ake yi muke karantawa” ita ce wadda ta karfafa min gwiwa na fara rubutun online.
Kamar wane irin labari ki ka fi mayar da hankali a kai wajen rubutawa?
Na fi mayar da hankali a kan soyarya, tausayi da zalunci, kusan duka labarin nawa idan aka karanta sai ka samu kusan duka a ciki.
Za ki yi shekara nawa da fara rubutu?
Eh! to, a kalla shekara biyar kenan zuwa shida.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Ban fuskanci wani wahala ba, farawa kawai nayi na fara turawa group-group din littattafai da nake ciki. Ana haka wata marubuciya mai suna Maryam Al-Hassan Obam ta yi min magana ta ‘Pribate’ a kan ya kamata na shiga group din marubuta, na ce mata babu damuwa ta bada lambata aka saka ni cikin ‘Kainuwa Writers Association’ ta hakan na kara samun taimako sosai da sosai, a gaskiya ba ni da abin da zan ce mata sai fatan Allah ya kara daukaka.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka nuna musu kina sha’awar fara rubutu, shin kin samu wani kalubale daga gare su ko kuwa?
A gaskiya ban samu ba saboda mahaifiyata mace ce me fahimta, sannan kuma a lokacin da muke maganar da yayata tana wajan, fadan data yi mun shi ne kada na yarda ya taba karatuna.
Kin rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?
Na rubuta labarai sun kai 8 amma guda uku kawai na fitar da su.
Idan na fahimce ki kina so ki ce kin buga guda uku kenan ko ya ki ke nufi?
Na saki guda uku a online ragowar kuma ban sake su ba sakamakon sace min waya da aka yi komai yana ciki ga karatu da nake yi hakan ya sa na ji ba zan iya sake rubutasu ba.
Ko za ki fada wa masu karatu sunayen labaran da ki ka rubuta dan su kara fahimtar wadda muke tare da ita?
Na farko Kowa Da Ranarsa, na biyu Rikicin Tagwaye, na uku Dana sanin Rayuwata.
Wane labari ne ya zamo bakandamiyarki cikin wadanda ki ka rubuta?
A gaskiya na fi son Kowa Da Ranarsa, kuma shi ne bakandamiyata.
Cikin labaran da ki ka rubuta akwai wanda ki ka buga ko ki ke saka ran bugawa?
Ban buga ko daya ba, amma ina fatan na buga Kowa Da Ranarsa in sha Allahu.
Wanne irin Nasarori ki ka samu game da rubutu?
A gaskiya na samu sosai saboda na sha kira ta waya wasu hadda kati wasu data wasu ma idan suka ga hoto na sai su yi ta mamakin yadda na hada wannan labarin na rubuta, gashi da tsawo ba zan manta lokacin da labarin ya kai tsakiya ba, sai na dakata saboda na fahimci yanayin karbuwar labarin. Washegari na sha kira da Tedt Message, ta Whatsapp ma haka ga ‘boice note’ hakan sai ya karamin kwarin gwiwa ya sani farinciki na ci gaba da yi.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da rubutu ko ta bangaren masu karatu?
Eh! to, babu abin da za ka yi a rayuwa da za ka kai wani mataki ba tare da kalubale ba, wasu sun nuna min bakin cikinsu kiri-kiri kafin na hadu da Aunty Maryam Obam, akwai wata marubuciya da na taba yi wa maganar ina so in shiga kungiyarsu ta marubuta sai ta nuna min ai sai na rubuta littafi da yawa kuma sai na yi wasu cike-cike cikin hakan, Allah ya hada ni da Aunty Maryam Obam.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Babban burina shi ne na ci gaba da rubuta littafi masu ma’ana da darasi, na kai matakin da har za a iya fim da labarina.
Ko akwai abin da ya taba bata miki rai ko faranta miki game da rubutu?
Eh! Abu daya ne ya bata min rai shi ne yadda na tsinci littafi na ana siyarwa.
Wane abu ne idan ki ka tuna shi ki ke jin dadinsa game da rubutu?
Yadda nake iya aika sako ta hanyar rubuta labari, a gaskiya yana saka ni nishadi sosai da kuma yadda mutane ke nishadantuwa da labarin har suke min ‘comment’ masu dadi.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Na dauki rubutu wata hanya ta fadakarwa da tunatarwa tare da saka nishadi a zukatan masu karantawa.
Bayan rubutu kina yin wata sana’ar ne?
Ina ‘Business’ siye da siyarwa, daga baya kuma na fara koyarwa.
Ya kike iya hada aiki da kuma rubutu?
A gaskiya ba abu me sauki bane, amma in na tuna yadda mutane ke bibiyar labarin sai ya bani kwarin gwiwa.
Kamar wane lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Lokacin da bana komai na samu wajen da babu hayaniya na zauna ko kuma da daddare.
Me za ki ce da makaranta labaranki?
Babu abin da zan ce musu sai sakallahu khairan, saboda soyayyar da suka nuna min da kuma fatan su dauki darasin dake cikin labarin.
Gaishe da mutum biyar
Da farko zan fara gaida mahaifiyata, sannan yayata Hijjaziya wadda ta bani kwarin gwiwar fara rubutu, sai Aunty Maryam Obam, sai Hassan Atk sai kuma masoyan littattafai na.
Muna godiya, ki huta lafiya
Ni ma na gode, Allah kara daukaka gidan jaridar Leadership Hausa, tare da ma’aikatanta.