Tun daga shekarar 2021, Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya (NPA), ta kara yawan gudummawar da take bayarwa ga asusun tattara kudaden shiga (CRF) tare da saukaka fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje.
Tattalin arzikin Nijeriya ya fuskanci Kalubale da dama a cikin ‘yan shekarun da suka gabata inda masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu ke fafutukar ganin sun rayu. Kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin sun hada da hauhawar basussukan da ake ciyowa, hauhawar farashin kayayyaki, rashin daidaiton musayar kudaden kasashen waje, raguwar samar da kudaden shiga, da dai sauransu.
- Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
- Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe
Masana tattalin arziki sun yi nuni da cewa idan gwamnati tana son dakile wadannan kalubale, to akwai bukatar ta samar da karin kudaden shiga, rage hauhawar farashin kayayyaki tare da kuma daidaita darajar Naira ta hanyar saukaka fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
Nijeriya ta samu karuwar kudaden shiga daga Naira biliyan 317 a shekarar 2020, zuwa Naira biliyan 333.5 a shekarar 2021, har zuwa Naira biliyan 361 a shekarar 2022; sannan kuma kudaden da ake turawa suna ci gaba da karuwa daga Naira biliyan 80 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 93.4 a karshen shekarar 2022, wanda hukumar ke shirin zarce hakan a shekarar 2023 bisa jimillar kusan Naira biliyan 90 da aka riga ma aka shigar a asusun CRF na watan Janairu zuwa Agustan 2023 wanda wannan amsa ce ta gaggawa domin cimma bukatun habbaka tattalin arzikin al’umma.
Masana harkokin tasoshin ruwa, sun bayyana cewa babban jami’i kuma shugaban hukumar ta NPA, Mohammed Bello-Koko, shi ne ya bunkasa kudaden shigar hukumar da ake samu zuwa wani matakin da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan da aka nada shi shugabancin hukumar a shekarar 2021.
A cewarsu, ya fito da dabaru uku masu dorewa wanda ya hada da kirkirar fasahar al’umma, fasahar zamani, tare da samar da ababen more rayuwa da kuma kayan aiki.
A cewar wani mai jigilar kayayyaki, Ikechukwu Chima, ya ce hukumar a wani yunkuri na dakile tashe-tashen farashi da ake samu a bangaren kudaden waje, ta sake gina makarantar horar da tashar jiragen ruwa, tare da fadada na’urar lura dake cibiyar horarwa ta tashar jiragen ruwa da kuma inganta ta domin ta dace da ka’idojin bayar da takardar shedar kasa da kasa wanda hakan ya sanya ya zama ba dole ba ne a yanzu a rika aika ma’aikata zuwa kasashen waje domin samun horo, ta hakan kawai, an ceto kasar daga kashe makudan kudaden waje domin horaswa a waje.
Alakar da take akwai ba tare da rabuwa ba wajen gudanar da aikin al’umma, shi ne fahimtar da ba a saba gani ba na gwamnati cewa akwai asarar da ake yi a kowanne sa a da aka rasa na rage kayan aiki, wannan dalilin ya sa ta ci gaba da kulla alaka da manyan ma’aikatan kungiyar kamfanoni masu zaman kansu da kuma kamfanoni mallakar Gwamnati (SSASCGOC: TUC), da kuma Kungiyar Ma’aikatan tasoshin jiragen ruwa (MWUN: NLC) tare da sauran kungiyoyi masu tallafa wa wanda ake ganin alfanun hakan a bangaren walwala da jindadin ma’aikatan da ake gani. Dangane da yarjejeniyar ruwa ta kasa da kasa a bakin Teku ga masu amfani da Tekun, kwanan nan Hukumar ta sake ginawa tare da samar da kayayyakin aiki a ofishin masu aiki a Teku (MTS) a Legas zuwa mafi kyawun irin sa a yankin. MTS shi ne ma’auni na duniya wajen kwatanta kimar tashar jiragen ruwa da kuma samar da kyakkyawan suna ga kasa.
Har ila yau, tare da cewa fasaha ta kasance ginshikin samar da ingantaccen tashar jiragen ruwa, hukumar ta inganta tare da sabunta tsarin tashar jiragen ruwa ta hanyar hadin gwiwa tare da IMO domin bunkasa ‘Port Community System (PCS)’ wanda hakan ke nuni da muhimmancin masu gudanarwa na hukumar na yanzu suka nuna domin ciyar da kasuwancin Nijeriya gaba.
PCS wanda ya kafa harsashin samar da ‘National Single Window (NSW)’ wato- ma’auni na duniya na ingancin tashar jiragen ruwa, wanda yake tsari ne na musamman wanda ke saukaka musayar bayanai tsakanin duk bangarorin da ke ayyukan da suka shafi tashar jiragen ruwa. Hukumar Tashoshin Ruwa ta Nijeriya (NPA) ta kasance a gaba-gaba wajen daukar matakan aunawa domin aiwatar da tsarin na PCS.
Duk da cewa a tsarin aikin PCS yana da bukatar ayyukan hukumomi da yawa, wanda hakan ke daukar lokaci mai tsawo, hukumar NPA a matsayinta na babban dandali dake saukake hanyoyin kasuwanci a Nijeriya ta hanyar ba da shawara da hadin gwiwa ta saukaka hanyoyi kasuwanci kuma yadda ya zuwa yanzu ta kammala kashi na biyu na shawarwarin cinikayya a karkashin Jagorancin Hukumar Kula da Tasoshin jiragen ruwa ta Duniya (IMO).
Domin tabbatar da gaskiya tare da kuma kawar da rashin fahimta, Hukumar ta kammala aikin sarrafa kayan liyafar tashar jiragen ruwa da biyan kudi tare da tsarin tattara kudaden shiga da tsarin gudanarwa (RIMS), da kuma kaddamar da hanyar samun bayanai cikin sauki da kuma shaidar biyan shiga jirgin ruwa (ESEN), da kuma tsarin sarrafa zirga-zirgar lantarki (e-Call Up), a halin yanzu kuma tana gudanar da ‘Oracle Financials’ da ‘Oracle HR’ kuma hukumar na kan hanyar siyan manhaja da za ta taimaka wajen sarrafa tashar jiragen ruwa da kuma aiwatar da ingantaccen kayayyakin aikin da za su karfafa siginal din samun bayanai na tashoshin jiragen ruwan.
Domin tabbatar da an wayar da kai domin bai wa hukumomi iko tare da kuma samar da bayanan da suke da aminci ga hanyoyin da ke cikin tasoshinsa daidai da tsarin tsaro na rayuwa a Teku (SOLAS), Hukumar gudanarwar a yanzu ta hada hannu da hukumar zirga-zirgar jiragen ruwa na ‘NLNG Ship Management Ltd (NSML)’ domin tura sabis din zirga-zirga a matakin karshe.
Dorewar tashoshin jiragen ruwa ya dogara ne da ingantattun kayan more rayuwa da na aiki. A yayin da ake jiran amincewar da suka wajaba domin samar da kudade wajen sake gina katafaren tashar jiragen ruwa na ‘Tin Can Island’ da suka tsufa da kuma gyara abubuwan da suke fuskantar kalubale a dukkan wuraren tashar jiragen ruwa, tawagar gudanarwa ta yanzu a cikin lokacin da ake wannan bitar ta dauki matakan da suka dace wanda ya cancanci a yaba mata kamar haka:
– Samar da irin sa na farko a cikin harkokin cinikayya ta ruwa na Afirka inda a kwanan nan aka kaddamar da ‘Azimuth Stern Dribe (ASD) 8213 model 80’ da kuma ‘Ton Bollard Pull Tugboats’ domin ba da damar jigilar manyan jiragen ruwa na mita 300 LOA ko ma fiye.
– Ingantawa tare da gudanar da na’urorin sarrafawa na zamani na Legas da na tashar ruwa na ‘Tin Can Island Port’.
– Saye tare da tura jiragen ruwa na tsaro da aka fi sani da ‘Security Patrol Boats’ (SPBs) a dukkanin tasoshin ruwa domin samar da ingantaccen tsaro tare da kuma magance hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a hanyoyin tashoshin wanda hakan ke haifar da cunkuson da ba a taba gani ba wajen zirga-zirgar kayayyaki a Tashoshin dake Gabas musamman tashar Onne. -Samun karin kayayyaki na saukaka aiki kamar (Tugboats, Pilot Cutters) domin kawar da jinkirin da ke tattare da tura jiragen ruwa da kuma tukin jiragen ruwa tare da bunkasa ayyuka a Tashoshin.
Saye tare da sanya na’urorin taimako na ‘Aids’ da kuma masu kewayawa da aka fi sani da ‘Buoys’ a Warri da kuma gundumar ‘Calabar Pilotage’, domin daidaita alamar tashoshi da taswirar hanya; kammala hanyar da ta hada ‘Berth 9,10, &11’ a mahadar Tashar Tekun Tarayya, Tashar Onne da kuma sanya mashigar Tsaro ta ‘Marine Fenders Authority Wide’. Wannan baki daya an yi ne domin habaka amincin kayayyakin aiki tare da kuma zama ma’auni na riga-kafi domin hana duk wani nau’i na hadari da zai taso daga tunkarar jirgin ruwan kai tsaye a kan jikin jirgin ruwa.
Bisa la’akari da muhimmancin da ma’auni na kasuwanci ke da shi wajen karfafa darajar Naira, hukumar NPA a karkashin agogo sarkin aiki wato Bello Koko ta ba da shaida tare da ba da lasisin har guda 10 ga tasoshin da suke fitar da kayayyaki wato ‘Edport Processing Terminals (EPTs)’ a turance a jihohin Legas da Ogun a tashin farko. An tsara wannan tsarin na EPTS ne domin kawar da duk wasu kulla-kullar da yake akwai a cikin tsarin fitar da kaya daga Nijeriya zuwa kasuwannin kasashen duniya wanda hakan ke sanya rashin gasa a tsakani.
Hukumar ya zuwa wannan lokacin da ake bitar nan ta kuma yi nasarar aiwatar da ka’idojin saukewa da daukar kaya, wanda baya ga zurfafa hanyar kwarewa da kuma bin tsarin da ya dace na duniya a fannin teku, ta samar da ayyukan yi da kuma samar da makudan kudaden shiga daga Kamfanonin mai na kasa da kasa (IOCs) wanda ake yin asararsu.
Samar da sabbin sana’o’i da guraben ayyukan yi kamar a bangaren gudanarwa na ‘Barge Operations’ wanda baya ga rage matsi a kan tituna ya kuma kara abin da ake samu zuwa samar da Naira biliyan 2 a duk shekara ta hanyar zuba hannun jari kai tsaye da kuma na waje. Hukumar ta NPA ta kuma fara ba da karin lasisin tanadin wuraren manyan motoci domin kara karfin wuraren manyan motocin da ke kula da tashoshin jiragen ruwa na Legas. Haka nan, an sami raguwar faduwar manyan motoci saboda nasarar aiwatar da tsarin kira na ‘E-Call Up’.
Hukumar ta NPA ta kuma tabbatar da aiwatar da mafi karancin ka’idojin tsaro a kan manyan motoci, wanda ya nuna cewa, duk manyan motocin da ke shiga tashar jiragen ruwa ana duba su, a kuma ba su takardar shaidar tabbatar da tsaro. Sauran sune: kashi 65% na raguwar adadin hatsarori, wanda ya samo asali daga inganta matakan manyan motocin da ke aiki a cikin harabar tashar jiragen ruwa da daidaita tsarin aikinsu domin gudanar da ayyuka daban-daban daga jiragen ruwa, jirage masu zaman kansu, matukin jirgi, jirgin ruwa / tukin jirgin ruwa da dai sauransu.
A yunkurin sanya Nijeriya a turbar gudanar da ingantaccen tsarin aiki a fannin albarkatun ruwa na kasar a matsayinta na kasa mai zaman kanta, Hukumar ta ba da shawarwarin amfani da fasaha tare da bin diddigin matakan amincewa cikin hanzari domin gudanar da ayyukan tashar ruwa mai zurfi ta farko a Nijeriya; tashar ruwa ta Lekki wanda ya ninka matsayin tashar jirgin ruwa ta farko mai sarrafa kanta a Nijeriya.
Tashar ruwa ta ‘Lekki Deep Sea’ ta aza harsashi wajen amincewar da majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi a kwanan nan wajen samar da tashar jiragen ruwa ta Badagry, tashar ruwa ta Ondo, ‘Snake Island’ da tashar Koko a Jihar Delta.
Idan aka yi la’akari da abubuwan da suka gabata, ya tabbata cewa hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Nijeriya tana kan turba mai inganci domin tabbatar da ci gabanta, sanya gasa, tare da kuma bunkasa shirye-shiryenta na nan gaba domin kara bayar da damammalin da ke tattare da yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).