Yanzu matafiya daga wannan jiha zuwa waccan suna cikin halin ni ‘yasu musamman ma sun kwan da sani irin yadda halin hanyoyin Nijeriya suke ciki, abinda ke kara jagule lamura shine lokacin damina. Daga Abuja zuwa Kaduna, Umuahia-Ikot Ekpene, Calabar-Itu, Ado Ekiti-Ikere-Akure, hakanan Makurdi zuwa Enugu abin ya zama kamar tarkon mutuwa domin ganin yadda yanayin hanyoyin suke, shi yasa ma mazauna wuraren suka bukaci a kammala hanyar Lakwaja zuwa Benin.
Da yake yanzu ana cikin halin damina lokaci ne da za aiya gane lalle Nijeriya na fama da karancin hanyoyi masu kayau.
- Yawan Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajoji Da Bayar Da Hidimomi Ya Karu Da Kaso 4% A Agusta
- Sama Da ‘Yan Nijeriya Miliyan 4 Suka Yi Zaman Kashe Wando A 2023 –NBS
Abubuwan da ka iya faruwa sanadiyar rashin hanyoyi masu kyau suna da yawa, suna kuma taimakawa wajen matsalolin da ake fuskanta, da suka hada da tattalin arziki, zamantakewa, da kuma muhalli.
A Katari kan hanyaer Kaduna zuwa Abuja za‘a iya ganin irin yadda matsalolin wani abu daga cikin sinadaran more rayuwa suke.
Duk da yake ma’aikatar ayyuka ta kasa bada dadewa bane ta kawo kamfanin Julius Berger, aka kira dan kwangilar da aka ba kwangilar tun farko ya dawo bakin aiki, duk da hakan hanyar zuwa yanzu ta zama alakakai.Matafiya lokutta da dama suna shan wahala idan suna kan hanyar, yayin da wani lokaci tafiyar ta kan karu da awa uku zuwa hudu wani lokaci ma kilomita biyu ne na waurin da ya lalace,bama kamar lokacin damina.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da labaran irin rasher ashen rayukan da aka yi saboda yawan hadurran da suke aukuwa akan hanyar.
Mark Shima,wanda shi direba ne a tashar mota ta mahadar Command dake Kaduna ya nuna bukatar d ake da ita ta daukar matakin gaggawa wajen gyare- gyaren hanyoyi,inda yace rashin kyan hanya ya sa an yi asarar rayuka musamman ma, a wani wuri da yake a gaban Jere.
A Jihar Sakkwato hanya daga Sakkwato zuwa Kebbi duk da yake dai ba mai tagwayen hanyoyi bane,ba a samun matsala sosai.Sai dai kuma hanyar Sakkwato zuwa Gusau ita ma tana bada matsaloli.Wasu ayyukan gyare da hukumomin gwamnati suka yi ya kara inganta wuraren , amma akwai wuraren da suke bukatar daukar mataki. Akwai wuraren da ake fuskantar matsaloli da suka hada da Tureta,Dange-Shuni, and Talata Mafara.HanyarThe Dange-Shuni ana maida ta tagwayen hanyoyi wadda aka faro daga Sakkwato amma sai dai aikin yana tafiyar Hawainiya.Wani dierba mai suna Sani Auwalu ya bayyana yadda yake fama da gyaran motar shi saboda rashin kyau na hanyar, saboda duk lokacin da aka ce ya dawo daga tafiya dole ne sai ya yi bincike saboda ko akwai noti ko kusa da ta bata.
A Jihar Kano lamarin bai canza ba domin kuwa hanyar Sabon Titi da take babbar hanya ce da ta hada manyan garuruwa kamar Gwarzo Madobi da Dorayi, ta kasance wata hanya c eke taimakawa ta wuraren da suke da rami, sai dai maganar neman a bada nagoro da matasa ke yi. Mustapha Niga, da yake direba wanda yake zama kusa da wuraren, ya yi kira da gwamnati ta dauki matakin da ya dace saboda kada ta kara lalacewa fiye da yadda take yanzu.
Jihar Zamfara ma tana da matsalolin saboda yanayin daminar da ake ciki ga kuma hanyoyin gwamnatin tarayya da ake aikin gina su da gyara.Funtua zuwa Gusau (kilomita 97ne), Gusau zuwa Sakkwato ( kilomita 225 km), yayin da Gusau zuwa Magami da Dansadau (kilomita 105) hanyoyin basu da kyau.Ayyukan da ake cikin yi sun kara sa ana shan wahala lokacin tafiye – tafiye.
Hanyoyin Jihar Katsina kamar ta Gidan Mutun daya da zata kai mutum zuwa babban birnin Jihar tana bukatar gyara ita ma.Mallam Zuberu Sani,da yake mazaunin wurin yace da farko an yi niyyar tagwayen hanyoyi amma daga baya sai aka bar aikin bayan an fara, hakan na samar da matsalaoli ga matafiya.
Jihar Borno abin can ma akwai ban takaici kan lamarin hanyoyi wadanda sun lalace da maganar ambaliyar ruwa. Wannan shi yasa ake samun yawan harin’yan B OKO Haram da garkuwa da jama’a.
A Jihar Neja kusan dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya basu da dadin bi ayitafiya da mota lokacin damina.Hanyar Suleja zuwaMinna, Agaie-Baddegi-Bida,Kontagora-Rijau-Zuru, Kontagora-Bangi, Minna-Tegina, da Tegina-Bokani-Mokwa, da kuma Tegina zuwa Kalgara har da Birni Gwari duk basu da kyau. Mista Samson Alfa ya ce saboda rashin kyau na hanyoyin yasa yasa kudin tafiya ya karu, ga kuma ambaliyar ruwa da zaizayar kasa.
A Jihar Kwara hanyoyin Ilorin-Omu-Aran-Egbe-Kabba da Share zuwa Patigi manyan matsaloli ne ga matafiya cewar Malam Ganiyu Adigbongbo,shugaban kungiyar direbobi ta kasa NURTW na reshen Gambari zuwa Ilorin, ya bayyana irin matsalolin da matafiya suke fuskanta.
Jihar Imo, hanyoyin Owerri zuwa Umuahia sune wadanda suka fi damuwar matafiya.Hanyar kuros riba ta Kudu maso gabas, da suka hada hanyoyin mazabun ‘yan majalisar dattawa uku na Jihar da kuma bangaren Neja Delta, suna da wurare biyu da basu da kyau.
Jihar Abia State hanyoyi kamar Umuahia-Ikot Ekpene da Aba-Ikot Ekpene sun dade da baci saboda yadda suke wahalar da matafiya.