ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ruwan Sama Ya Kara Dagula Hanyoyin Mota A Daminar Bana

by Idris Aliyu Daudawa and Sulaiman
2 years ago
Ruwan sama

Yanzu matafiya daga wannan jiha zuwa waccan suna cikin halin ni ‘yasu musamman ma sun kwan da sani irin yadda halin hanyoyin Nijeriya suke ciki, abinda ke kara jagule lamura shine lokacin damina. Daga Abuja zuwa Kaduna, Umuahia-Ikot Ekpene, Calabar-Itu, Ado Ekiti-Ikere-Akure, hakanan  Makurdi zuwa Enugu  abin ya zama kamar tarkon mutuwa  domin ganin yadda yanayin hanyoyin suke, shi yasa ma mazauna wuraren suka bukaci  a kammala hanyar  Lakwaja zuwa Benin.

 

Da yake yanzu ana cikin halin damina lokaci ne da za aiya gane lalle Nijeriya na fama da karancin hanyoyi masu kayau.

ADVERTISEMENT
  • Yawan Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajoji Da Bayar Da Hidimomi Ya Karu Da Kaso 4% A Agusta
  • Sama Da ‘Yan Nijeriya Miliyan 4 Suka Yi Zaman Kashe Wando A 2023 –NBS

Abubuwan da ka iya faruwa sanadiyar rashin hanyoyi masu kyau suna da yawa, suna kuma taimakawa wajen matsalolin da ake fuskanta, da suka hada da tattalin arziki, zamantakewa, da kuma muhalli.

 

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

A Katari kan hanyaer Kaduna zuwa Abuja za‘a iya ganin irin yadda matsalolin wani abu daga cikin sinadaran more rayuwa suke.

 

Duk da yake ma’aikatar ayyuka ta kasa bada dadewa bane ta kawo kamfanin Julius Berger, aka kira dan kwangilar da aka ba kwangilar tun farko ya dawo bakin aiki, duk da hakan hanyar zuwa yanzu ta zama alakakai.Matafiya lokutta da dama suna shan wahala idan suna kan hanyar, yayin da wani lokaci tafiyar ta kan karu da awa uku zuwa hudu wani lokaci ma kilomita biyu ne na waurin da ya lalace,bama kamar lokacin damina.

 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da labaran irin rasher ashen rayukan da aka yi saboda yawan hadurran da suke aukuwa akan hanyar.

 

Mark Shima,wanda shi direba ne a tashar mota ta  mahadar Command dake Kaduna ya nuna bukatar d ake da ita ta daukar matakin gaggawa wajen gyare- gyaren hanyoyi,inda yace rashin kyan hanya ya sa an yi  asarar rayuka musamman ma, a wani wuri da yake a gaban Jere.

 

A Jihar Sakkwato hanya daga Sakkwato zuwa Kebbi duk da yake dai ba mai tagwayen hanyoyi bane,ba a samun matsala sosai.Sai dai kuma hanyar Sakkwato zuwa Gusau ita ma tana bada matsaloli.Wasu ayyukan gyare da hukumomin gwamnati suka yi ya kara inganta wuraren , amma akwai wuraren da suke bukatar daukar mataki. Akwai wuraren da ake fuskantar matsaloli da suka hada da Tureta,Dange-Shuni, and Talata Mafara.HanyarThe Dange-Shuni  ana maida ta tagwayen hanyoyi wadda aka faro daga Sakkwato amma sai dai aikin yana tafiyar Hawainiya.Wani dierba mai suna Sani Auwalu ya bayyana yadda yake fama da gyaran motar shi saboda rashin kyau na hanyar, saboda duk lokacin da aka ce ya dawo daga tafiya dole ne sai ya yi bincike saboda ko akwai noti ko kusa da ta bata.

 

A Jihar Kano lamarin bai canza ba domin kuwa hanyar Sabon Titi da take babbar hanya ce da ta hada manyan garuruwa kamar Gwarzo Madobi da Dorayi, ta kasance wata hanya c eke taimakawa ta wuraren da suke da rami, sai dai maganar neman a bada nagoro da matasa ke yi. Mustapha Niga, da yake direba  wanda yake zama kusa da wuraren, ya yi kira da gwamnati ta dauki matakin da ya dace saboda kada ta kara lalacewa fiye da yadda take yanzu.

 

Jihar Zamfara ma tana da matsalolin saboda yanayin daminar da ake ciki ga kuma hanyoyin gwamnatin tarayya da ake aikin gina su da gyara.Funtua  zuwa Gusau (kilomita  97ne), Gusau  zuwa Sakkwato ( kilomita 225 km), yayin da Gusau zuwa Magami da Dansadau (kilomita 105) hanyoyin basu da kyau.Ayyukan da ake cikin yi sun kara sa ana shan wahala lokacin tafiye – tafiye.

 

Hanyoyin Jihar Katsina kamar ta Gidan Mutun daya da zata kai mutum zuwa babban birnin Jihar tana bukatar gyara ita ma.Mallam Zuberu Sani,da yake mazaunin wurin yace da farko an yi niyyar tagwayen hanyoyi amma daga baya sai aka bar aikin bayan an fara, hakan na samar da matsalaoli ga matafiya.

 

Jihar Borno abin can ma akwai ban takaici kan lamarin hanyoyi wadanda sun lalace da maganar ambaliyar ruwa. Wannan shi yasa ake samun yawan harin’yan B  OKO Haram da garkuwa da jama’a.

 

A Jihar Neja kusan dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya basu da dadin bi ayitafiya da mota lokacin damina.Hanyar Suleja zuwaMinna, Agaie-Baddegi-Bida,Kontagora-Rijau-Zuru, Kontagora-Bangi, Minna-Tegina, da Tegina-Bokani-Mokwa, da kuma Tegina zuwa Kalgara har da Birni Gwari  duk basu da kyau. Mista Samson Alfa ya ce saboda rashin kyau na hanyoyin yasa yasa kudin tafiya ya karu, ga kuma ambaliyar ruwa da zaizayar kasa.

 

A Jihar Kwara hanyoyin Ilorin-Omu-Aran-Egbe-Kabba da Share zuwa Patigi manyan matsaloli ne ga matafiya cewar Malam Ganiyu Adigbongbo,shugaban kungiyar direbobi ta kasa NURTW na reshen Gambari zuwa Ilorin, ya bayyana irin matsalolin da matafiya suke fuskanta.

 

Jihar Imo, hanyoyin Owerri zuwa Umuahia sune wadanda suka fi damuwar matafiya.Hanyar kuros riba ta Kudu maso gabas, da suka hada hanyoyin mazabun ‘yan majalisar dattawa uku na Jihar da kuma bangaren Neja Delta, suna da wurare biyu da basu da kyau.

 

Jihar Abia State hanyoyi kamar Umuahia-Ikot Ekpene da Aba-Ikot Ekpene sun dade da baci saboda yadda suke wahalar da matafiya.

Ruwan sama
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi
Ruwan sama
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
katsina

Gwamna Ya Bukaci Sojoji Su Rika Amsa Kiran Gaggawa A Katsina

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.