Nijeriya na iya asarar gudummawar wasu kasashe 12 a bangaren a banbharen samar da tsaro ga al’ummata za kuma ta iyan yin gaggarumin asara a tattalin arzikin kasa sakamakon ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar kasashen yankin Afirka ta Yamma, kamar yadda masana da al’ummar da suke zaune a yankuna suka bayyana wa jaridar Daily Trust.
Masanan sun kuma yi hayanin cewa, ficewar wadanan kasashe uku za iya tarnaki ga tattaunawar da ake yi don samar da hadewar yankin da kuma aiwatar da yarjejeniyar da aka yi na cinikayya a tsakanin yankunan Afirka (AfCFTA).
- Nijeriya Ta Yi Allah-Wadai Da Ficewar Nijar, Mali Da Burkina Faso Daga ECOWAS
- ECOWAS Ta Shimfida Sabbin Ka’idoji Domin Janye Wa Nijar Takunkumi
An samar da shirin AfCFTA ne don gagguta hada harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka kamar yadda dokokin majalisar dinkin duniya ta tanada.
Idan za iya tuna a ranar Lahadi ne sojojin da ke mulki a kasashen uku suka sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS da gaggawa. Hakan kuma ya faru ne sakamakon takunkumin da kungiyar ta sanya musu baayn juyin mulkin da aka yi a kasashen. A shekarar 2021 aka dakatar da kasa Mali bayan juyin mulki har sau biyu an kuma dakatar da kasar Burkina Faso ne a shekarar 2022, yayin da aka dakatar da kasar Nijar a shekarar 2023.
Ba kamar yadda abin da ya faru ba a lokacin da aka dakatar da kasashen Mali da Burkina Faso, dakatar da Nijar ya jawo kace-nace musamman daga al’ummar yankin arewacin Njijeriya wanda suke da dangatakar tarhi da an kasuwanci a tsakaninsu da Nijar.
Al’ummar kasashen biyu suna da tarihin auratayya, harkokin kasuwanci suna kuma fuskantar matsalolin da ke auko masu tare a dukkan matakai na mulki. Suna kuma da iyakokin da suke tare da kilomita fiye da 1,608 (mil 999) wanda ya taso daga Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa, Yobe da jihar Borno.
Duk da cewa, kasar Nijar ta dogara da Nijeriya a bangaren samar da hatsi, tufafi da kayan giine-gine, ita ma Nijeriya ta dogara da Nijar don samun dabbobi kamar rakuma shanu tumakai, dabino da asauran kayyakin amfani nay au da kullum.
Tabbas juyin mulkin da aka yi a Nijar da kuma matakan da kungiyar ECOWAS ta dauka wadda Nijeriya ta jagoranta sun shafi gangamin yaki da ta’addanci da hadakar sojoji daga yankin suke yi, sojojin da ke aikin tabbatar da zaman lafiya suna iya tabbatar da wannan ikirarin.
‘Yan Gudun Hijrar Yankin Borno Na Fuskatar Matsaloli
Shugaban dattawan yankin Borno, Dr Bulama Mali Gubio, ya bayyana cewa, ficewar kasar Nijar daga kungiyar ECOWAAS za iyi matuka shafar rayuwar ‘yan gudun hijira daga jihar Borno ya kuma shafi harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen wanda aka yi shekara da shekaru ana yi ba tare da wata mastala ba.
Lamarin Ya Shafi Hadin Kan Kasashen Yankin —
Malami a bangaren tattalihn arziki a Jami’ar Usmanu dafodiyo Sakkwato, Farfesa Tanko Baba, ya bayyana cewa, matsalar wadannan kasashe da kungiyar ECOWAs zai shafi Nijeriya ta bangarori da dama.
Matsalolin da za a fuskanta sun hada da raguwar kasuwanci a tsakanin Nijeriya da kasashen wanda hakan zai shafi al’ummar Nijetiya da dama wadanda suka diogara da wadanna kasuwan ci wajen rayuwar yau da kullum. Za kuma a samu mastalar tsaro. Wannan na nufin ‘yan ta’adda za su iya shogowa Nijeriya ba tare da wata mastala ba.
Dole Nijeriya ta sake nazarin wadannan lamarin don kada a kara jefa al’umma cikin matsalar tattalin arziki dana tsaro.