An sake samun girbi mai albarka a kasar Sin! Inda alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar a kwanan nan ta nuna cewa, a karon farko, kasar Sin ta kai ga cimma nasarar samun yawan hatsi da ya haura tan miliyan 700. Kafin hakan, cikin shekaru 9 a jere, kasar Sin na samun hatsin da ya haura tan miliyan 650 a duk shekara.
Bayan da muka watsa wannan labari ta shafinmu na Facebook, masu bibbiyarmu da dama sun taya kasar Sin murnar cimma wannan nasara. Hakika, har kullum masu bibbiyarmu na mai da hankali sosai a kan harkokin da suka shafi ci gaban noma a kasar Sin, musamman ma yadda kasar Sin ke zamanantar da ayyukan noma, wadanda kuma suke fatan ganin Sin da kasashen Afirka sun karfafa hadin gwiwarsu a wannan fanni.
- Xi Ya Halarci Bikin Dawowar Yankin Musamman Na Macao Kasar Sin Da Rantsar Da Sabuwar Gwamnati
- Dakarun MNJTF Sun Daƙile Harin Da Aka Kai Sansanin Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10 A Kamaru
Hasali ma dai, ci gaban ayyukan noma sun tabbata ne sakamakon yadda kasar Sin ke ba da muhimmanci matuka a kan ayyukan da suka shafi noma da yankunan karkara da ma manoma. Kasar Sin kasa ce da yawan al’ummarta ya kai biliyan 1.4, haka kuma kasa ce da yawan manomanta ya kai kimanin miliyan 700. Don haka, batutuwa masu nasaba da noma da yankunan karkara da kuma manoma na shafar samar da abinci ga ‘yan kasar biliyan 1.4 da ma ci gaban kasar, kuma tunanin ta yaya za a daidaita batutuwan muhimmin aiki ne da har kullum jam’iyyar da ke kan karagar mulki da ma gwamnatin kasar ke sanyawa a gabansu. A sabili da haka, a karshen kowace shekara, jam’iyyar Kwaminis da ke kan karagar mulkin kasar ta kan kira babban taro kan ayyukan raya yankunan karkara, inda a kan yi nazarin yanayin da ake ciki ta fannonin da suka shafi noma da yankunan karkara da ma manoma, tare da tsara ayyukan da za a gudanar a shekara mai zuwa.
Daga ranar 17 zuwa 18 ga wata, an gudanar da taron na bana a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya umarci a gaggauta zamanantar da ayyukan noma da yankunan karkara, da karfafa tushen ayyukan noma, da kara samar da ci gaba mai albarka a yankunan karkara, da kuma kara inganta walwalar manoma, don a cimma burin raya kasar ta zama gagarabadau a fannin ayyukan noma.
Noma tushen arzki, kamar dai yadda Hausawa kan ce. Abin hakan yake. A nahiyar Afirka, musamman kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, ayyukan noma kan dauki sama da kaso 30% daga cikin jimillar karfin tattalin arziki ta GDP, yayin da sama da kaso 70% na al’ummomin da suke da ayyukan yi suna gudanar da sana’o’i ne da suka shafi noma. Don haka ma, batutuwa masu nasaba da noma da yankunan karkara da kuma manoma su ma suna taka muhimmiyar rawa wurin daidaita matsalolin da kasashen suke fuskanta ta fannonin abinci da saukaka fatara da ma zamanantar da kansu.
Kasancewarta kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kullum kasar Sin na kallon kanta da kasashen Afirka a matsayin al’ummu mai makoma ta bai-daya, abin da ya sa take kokarin raba dabarunta da ma damammakinta ga kasashen Afirka a lokacin da take bunkasa kanta ta fannonin noma da yankunan karkara da ma manoma. A ‘yan shekarun baya, hadin gwiwar ayyukan noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya inganta bisa shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da ma tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, tuni har kasar Sin ta kafa cibiyoyin nune-nunen fasahohin noma 24 a kasashen Afirka, tare da yayata fasahohin noma na zamanin fiye da 300, matakan da suka sa amfanin gonar da aka samar a yankunan da abin ya shafa suka karu da kaso 30% zuwa 60%, wadanda kuma suka samar da alfanu ga manoma sama da miliyan a Afirka. “Kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a yunkurin kasashen Afirka na zamanantar da ayyukan noma”, in ji Rahamtalla M. Osman, babban wakilin kungiyar tarayyar Afirka a kasar Sin, wanda ya ce, fasahohin da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka sun taimaka wajen tabbatar da dauwamammen ci gaban ayyukan noma a kasashen Afirka, a yayin da kuma suka taimaka ga kara kudin shigar manoma.
A gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a watan Satumban bana a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu matakai 10 na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wajen zamanantar da kansu, ciki har da matakin da ya shafi bunkasa ayyukan noma, wato za a samar da gudummawar hatsi na kimanin kudin Sin yuan biliyan daya ga kasashen Afirka cikin gaggawa, da kafa yankunan nune-nunen fasahohin noma da tura masanan ayyukan noma 500 zuwa kasashen Afirka da kafa kawancen kirkire-kirkiren fasahohin noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka da dai sauransu.
Kasancewarsu kawayen juna, kasar Sin za ta rika raba cin gajiyar nasarorinta ga aminanta na Afirka wajen zamanantar da ayyukan noma, don su cimma burinsu na zamanantar da kansu. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp