Har kullum zaman lafiya shi ne burin bai daya na dukkan bil Adam, dama masu hikimar magana na cewa, “zaman lafiya ya fi zama dan sarki.” Wasu ma suka ce, “ya fi zama sarki.” Ko shakka babu, zaman lafiya shi ne jigo, kana kashin bayan dukkan wani cigaba na rayuwar bil adama. “Zama lafiya” “zaman lafiya” “zaman lafiya.” Wannan daya ne daga cikin manyan manufofin da mahukunta kasar Sin ke yawan ambatawa tare da dora muhimmanci kansa, kasancewar babu wata al’umma ko kasa, ko yanki, ko shiyya da za ta samu ci gaba ba tare da samun dawwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro ba.
Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya kasar Sin take kara bada gudunmawarta ta hanyar shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, kuma sau da dama, shugabannin kasar suna yiwa sojoji Sinawa huduba tare da kara musu kaimi wajen hada kan bangarori daban daban na duniya, domin dunkulewa wuri guda don tinkarar ayyukan kiyaye zaman lafiya, tare da tabbatar da tsaro, yayin da ake kokarin samun bunkasuwa a yanayin zamantakewar al’ummar ‘yan Adam baki daya.
Shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da sojojin kasar Sin ke yi ya shaida cewa, Sin ta tsaya tsayin daka, kan tsarin kasa da kasa, bisa manufofin MDD, da bin ka’idojin kundin tsarin mulkin MDD da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Har kullum Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen tabbatar da ra’ayin bangarori daban daban, da tabbatar da adalci, da more zaman lafiya, da kuma sa kaimi wajen shimfida zaman lafiya da samun wadata tare. A yayin da ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara ta 2022 ta kasance a matsayin ranar tunawa da ma’aikatan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a karo na 30, alkaluman da ma’aikatar tsaron kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, sojojin kasar Sin kusan dubu 50 sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a karo daban daban har 25.
Wannan shi ke nunawa a fili cewa, kasar Sin ta dauki hakikanan matakai a ayyukan kiyaye zaman lafiyar duniya, ta zama kasa ta farko wadda ta fi tura sojojin wanzar zaman lafiya daga cikin kasashe biyar masu wakilcin kujerun dindindin na kwamitin sulhu na MDD. Cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, rundunar sojan kasar Sin ta tura yawan sojoji masu ayyuka daban daban, wadanda suka gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiyar a kasashen duniya da dama, daga ciki, akwai kasashen Afrika, da suka hada da Kongo (Kinshasa), Liberia, Sudan, Sudan ta Kudu, Mali, Afirka ta Tsakiya, Saliyo, da sauran kasashe irinsu Cambodia, Lebanon, Cyprus da makamantansu, inda suka ba da muhimmiyar gudummawa wajen daidaita rikici cikin ruwan sanyi, da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankuna da shiyyoyi, da kara azama kan bunkasar tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummar kasashen.
Yayin da sojojin kasar Sin ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, har kullum suna mayar da hankali ne wajen sauke muhimmin nauyin dake bisa wuyansu, na kiyaye zaman lafiyar duniya, da raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam, a matsayin burinsu da aikinsu, sannan ayyukan nasu sun yi matukar bada tagomashi kuma sun zama ginshikan ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.
Hakika yadda jamhuriyar jama’ar kasar Sin ke jajurcewa wajen bayar da gagarumar gudunawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ma sauran batutuwan dake shafar cigaban kasa da kasa yana kara samun yabo a duniya, koda yake, wasu kasashen yammaci da ba su fiya son fadar alherin wasu kasashe ba, suna kawar da kansu daga nuna fatan alheri ga irin wadannan muhimman ayyukan kasa da kasa, da ma an ce, “idan ana son ganin laifinka ko ruwa kake tafiya sai a ce ka tada.” Wannan ba sabon abu ba ne. Sai dai ita gaskiya har kullum ba ta bukatar ado.
Idan za mu iya tunawa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne aka gudanar da bikin cika shekaru 50 da dawowar halastacciyar kujerar wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD, shugabannin kasashen duniya da jami’an diflomasiyya gami da shugabannin kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa sun gabatar da tsokaci da yin Allah sam barka bisa ga irin nasarorin da kasar ta cimma da kuma gagarumar gudunmawar da ta samarwa duniya a dukkan fannoni, wanda ya kunshi har da batun kiyaye zaman lafiya.
A wani jawabin da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar a lokacin bikin ya ce, a cikin shekaru 50 da suka gabata, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta samu dawowar wakilcinta a MDD. Guterres ya ce, cikin wadannan shekarun da suka gabata, ci gaban kasar Sin ya samar da damammaki ga duniya. “Muna godiya ga kasar Sin bisa yadda ta jajurce wajen kiyaye huldar bangarori daban daban, da taimakon da take bayarwa ga ayyukan MDD, da kuma muhimmiyar rawar da take takawa, da gudunmawarta ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa da kasa.”
Ya ce hakika MDD tana matukar nuna godiya ga kasar Sin bisa rawar da ta taka wajen kawar da kangin talauci, da jure matsalolin sauyin yanayin duniya, da kiyaye mabanbantan halittu, da daga matsayin aikin samar da riga-kafin cutar Covid-19. Shi ma shugaban babban taron MDD (UNGA) karo na 76 Abdullah Shahid, yabawa kasar Sin ya yi game da gagarumar gudunmawar da ta baiwa duniya tun bayan maido mata da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD.
Ya ce Sin ta taka rawar gani a hadin gwiwar bangarori daban daban, domin a halin yanzu, ita ce kasa ta biyu a duniya mafi bayar da gudunmawa na kasafin kudin ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDD. Sannan tana jagorantar ayyukan wanzar da zaman lafiya kimanin 30, bugu da kari, ta bayar da gudunmawar dakarun aikin wanzar da zaman lafiya sama da 50,000. Shahid ya ce, yana matukar farin ciki da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron mahawara karo na 76 na babban taron MDD, wanda ya tabo batun cewa, kasarsa za ta kara fadada tallafinta zuwa ga sauran kasashe masu tasowa domin bunkasa samar da makamashi mai tsafta wanda ba zai gurbata muhalli ba.
Game da annobar COVID-19, kasar Sin ta taka rawar gani inda ta lashi takobin samar da alluran riga-kafin COVID-19 biliyan 2 ga duniya zuwa karshen shekarar da ta gabata. Shi ma tsohon wakilin kasar Zambiya a MDD Vernon Mwaanga, ya ce babu tantama, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a tsarin ayyukan MDD a shekaru 50 da suka gabata a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Ya kuma yi waiwaye game da yadda kasashen Afrika suka goyi bayan jamhuriyar jama’ar kasar Sin don maido da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD. Ya ce, wakilan kasashen Afrika sun yi matukar nuna jajurcewarsu tare da yin amanna cewa ba za su taba lamintar yankin Taiwan, wanda bangare ne na kasar Sin, ya zama shi ne ke wakiltar kasar Sin ba. Ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Afika tana da kyakkyawar makoma, duba da yadda ake kara samun gagarumin ci gaban hulda a tsakanin bangarorin, kana dangantakar bangarorin biyu ta kara karfafa ta hanyar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, da shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Har kullum, gwamnatin kasar Sin da jama’arta, suna mayar da aikin kiyaye zaman lafiyar duniya a matsayin wani muhimmin nauyin dake bisa wuyansu. Ban da aikin sa ido kan tsagaita bude wuta, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun bada tabbaci ga manyan ayyuka, da jigilar kayayyaki, da kuma ayyukan likitanci na MDD, hakan sun samar da goyon baya ga tawagogin musamman na kiyaye zaman lafiya na MDD, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen sake gina kasar da suke gudanar da ayyukan da kyautata zaman rayuwar kasar baki daya.
Sin ta kara ayyukan da dakarunta na kiyaye zaman lafiyar ke gudanarwar wanda ya kunshi ayyukan taimakawa kiyaye zaman lafiya, da bada kariya ga fararen hula, da kiyaye tsaro da dai sauransu, haka kuma sun samar da babbar gudummawa wajen magance rikice-rikice, da daidaita matsaloli, da tabbatar da tsaron fararen hula da ma’aikatan tawagogin musamman na MDD da kuma ayyukan more rayuwa da sauransu. Dama dai mahukuntan kasar Sin sun sha nanata cewa, kasar ta sha alwashin tallafawa dukkanin wasu matakai, wadanda za su kai ga wanzuwar zaman lafiya da lumana, tare da ci gaban duniya, da daidaito tsakanin kasa da kasa. Game da hakan, wani jami’in jakadancin na Sin ya taba bayyana cewa, zaman lafiya da samar da ci gaba, su ne muhimman manufofin da duniya ta sanya gaba a halin yanzu. Kuma duk wani yunkurin kaucewa hakan zai zamo abun kyama, kuma ba zai kai ga nasara ba.
(Ahmad Fagam daga Beijing, China)