• Leadership Hausa
Sunday, October 1, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Sin Ta Baiwa Afrika Da Duniya Gagarumar Gudunmawar Wanzar Da Zaman Lafiya

by Sulaiman
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Yadda Sin Ta Baiwa Afrika Da Duniya Gagarumar Gudunmawar Wanzar Da Zaman Lafiya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Har kullum zaman lafiya shi ne burin bai daya na dukkan bil Adam, dama masu hikimar magana na cewa, “zaman lafiya ya fi zama dan sarki.” Wasu ma suka ce, “ya fi zama sarki.” Ko shakka babu, zaman lafiya shi ne jigo, kana kashin bayan dukkan wani cigaba na rayuwar bil adama. “Zama lafiya” “zaman lafiya” “zaman lafiya.” Wannan daya ne daga cikin manyan manufofin da mahukunta kasar Sin ke yawan ambatawa tare da dora muhimmanci kansa, kasancewar babu wata al’umma ko kasa, ko yanki, ko shiyya da za ta samu ci gaba ba tare da samun dawwamamman zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro ba.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya kasar Sin take kara bada gudunmawarta ta hanyar shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, kuma sau da dama, shugabannin kasar suna yiwa sojoji Sinawa huduba tare da kara musu kaimi wajen hada kan bangarori daban daban na duniya, domin dunkulewa wuri guda don tinkarar ayyukan kiyaye zaman lafiya, tare da tabbatar da tsaro, yayin da ake kokarin samun bunkasuwa a yanayin zamantakewar al’ummar ‘yan Adam baki daya.

Sin
A cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, sojojin kasar Sin kusan dubu 50 sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.

Shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da sojojin kasar Sin ke yi ya shaida cewa, Sin ta tsaya tsayin daka, kan tsarin kasa da kasa, bisa manufofin MDD, da bin ka’idojin kundin tsarin mulkin MDD da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Har kullum Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen tabbatar da ra’ayin bangarori daban daban, da tabbatar da adalci, da more zaman lafiya, da kuma sa kaimi wajen shimfida zaman lafiya da samun wadata tare. A yayin da ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara ta 2022 ta kasance a matsayin ranar tunawa da ma’aikatan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a karo na 30, alkaluman da ma’aikatar tsaron kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, sojojin kasar Sin kusan dubu 50 sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a karo daban daban har 25.

Wannan shi ke nunawa a fili cewa, kasar Sin ta dauki hakikanan matakai a ayyukan kiyaye zaman lafiyar duniya, ta zama kasa ta farko wadda ta fi tura sojojin wanzar zaman lafiya daga cikin kasashe biyar masu wakilcin kujerun dindindin na kwamitin sulhu na MDD. Cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, rundunar sojan kasar Sin ta tura yawan sojoji masu ayyuka daban daban, wadanda suka gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiyar a kasashen duniya da dama, daga ciki, akwai kasashen Afrika, da suka hada da Kongo (Kinshasa), Liberia, Sudan, Sudan ta Kudu, Mali, Afirka ta Tsakiya, Saliyo, da sauran kasashe irinsu Cambodia, Lebanon, Cyprus da makamantansu, inda suka ba da muhimmiyar gudummawa wajen daidaita rikici cikin ruwan sanyi, da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankuna da shiyyoyi, da kara azama kan bunkasar tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummar kasashen.

Sin
Kasar Sin takan shirya atisaye da bada horo ga dakarun kiyaye zaman lafiyar gabanin tura su fagen daga.

Yayin da sojojin kasar Sin ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, har kullum suna mayar da hankali ne wajen sauke muhimmin nauyin dake bisa wuyansu, na kiyaye zaman lafiyar duniya, da raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam, a matsayin burinsu da aikinsu, sannan ayyukan nasu sun yi matukar bada tagomashi kuma sun zama ginshikan ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.

Labarai Masu Nasaba

’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 

Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

Hakika yadda jamhuriyar jama’ar kasar Sin ke jajurcewa wajen bayar da gagarumar gudunawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ma sauran batutuwan dake shafar cigaban kasa da kasa yana kara samun yabo a duniya, koda yake, wasu kasashen yammaci da ba su fiya son fadar alherin wasu kasashe ba, suna kawar da kansu daga nuna fatan alheri ga irin wadannan muhimman ayyukan kasa da kasa, da ma an ce, “idan ana son ganin laifinka ko ruwa kake tafiya sai a ce ka tada.” Wannan ba sabon abu ba ne. Sai dai ita gaskiya har kullum ba ta bukatar ado.
Idan za mu iya tunawa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ne aka gudanar da bikin cika shekaru 50 da dawowar halastacciyar kujerar wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD, shugabannin kasashen duniya da jami’an diflomasiyya gami da shugabannin kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa sun gabatar da tsokaci da yin Allah sam barka bisa ga irin nasarorin da kasar ta cimma da kuma gagarumar gudunmawar da ta samarwa duniya a dukkan fannoni, wanda ya kunshi har da batun kiyaye zaman lafiya.

A wani jawabin da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya gabatar a lokacin bikin ya ce, a cikin shekaru 50 da suka gabata, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta samu dawowar wakilcinta a MDD. Guterres ya ce, cikin wadannan shekarun da suka gabata, ci gaban kasar Sin ya samar da damammaki ga duniya. “Muna godiya ga kasar Sin bisa yadda ta jajurce wajen kiyaye huldar bangarori daban daban, da taimakon da take bayarwa ga ayyukan MDD, da kuma muhimmiyar rawar da take takawa, da gudunmawarta ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa da kasa.”
Ya ce hakika MDD tana matukar nuna godiya ga kasar Sin bisa rawar da ta taka wajen kawar da kangin talauci, da jure matsalolin sauyin yanayin duniya, da kiyaye mabanbantan halittu, da daga matsayin aikin samar da riga-kafin cutar Covid-19. Shi ma shugaban babban taron MDD (UNGA) karo na 76 Abdullah Shahid, yabawa kasar Sin ya yi game da gagarumar gudunmawar da ta baiwa duniya tun bayan maido mata da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD.

Sin
•Sin ta tura tawagogin dakarun wanzar da zaman lafiya ga kasashen Afrika da dama da suka hada da Kongo (Kinshasa), Liberia, Sudan, Sudan ta Kudu, Mali da makamantansu.

Ya ce Sin ta taka rawar gani a hadin gwiwar bangarori daban daban, domin a halin yanzu, ita ce kasa ta biyu a duniya mafi bayar da gudunmawa na kasafin kudin ayyukan wanzar da zaman lafiyar MDD. Sannan tana jagorantar ayyukan wanzar da zaman lafiya kimanin 30, bugu da kari, ta bayar da gudunmawar dakarun aikin wanzar da zaman lafiya sama da 50,000. Shahid ya ce, yana matukar farin ciki da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron mahawara karo na 76 na babban taron MDD, wanda ya tabo batun cewa, kasarsa za ta kara fadada tallafinta zuwa ga sauran kasashe masu tasowa domin bunkasa samar da makamashi mai tsafta wanda ba zai gurbata muhalli ba.

Game da annobar COVID-19, kasar Sin ta taka rawar gani inda ta lashi takobin samar da alluran riga-kafin COVID-19 biliyan 2 ga duniya zuwa karshen shekarar da ta gabata. Shi ma tsohon wakilin kasar Zambiya a MDD Vernon Mwaanga, ya ce babu tantama, jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a tsarin ayyukan MDD a shekaru 50 da suka gabata a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Ya kuma yi waiwaye game da yadda kasashen Afrika suka goyi bayan jamhuriyar jama’ar kasar Sin don maido da halastacciyar kujerar wakilcinta a MDD. Ya ce, wakilan kasashen Afrika sun yi matukar nuna jajurcewarsu tare da yin amanna cewa ba za su taba lamintar yankin Taiwan, wanda bangare ne na kasar Sin, ya zama shi ne ke wakiltar kasar Sin ba. Ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Afika tana da kyakkyawar makoma, duba da yadda ake kara samun gagarumin ci gaban hulda a tsakanin bangarorin, kana dangantakar bangarorin biyu ta kara karfafa ta hanyar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, da shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Har kullum, gwamnatin kasar Sin da jama’arta, suna mayar da aikin kiyaye zaman lafiyar duniya a matsayin wani muhimmin nauyin dake bisa wuyansu. Ban da aikin sa ido kan tsagaita bude wuta, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sun bada tabbaci ga manyan ayyuka, da jigilar kayayyaki, da kuma ayyukan likitanci na MDD, hakan sun samar da goyon baya ga tawagogin musamman na kiyaye zaman lafiya na MDD, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen sake gina kasar da suke gudanar da ayyukan da kyautata zaman rayuwar kasar baki daya.

Sin
Kasar Sin ta bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a cikin gwamman shekaru.

Sin ta kara ayyukan da dakarunta na kiyaye zaman lafiyar ke gudanarwar wanda ya kunshi ayyukan taimakawa kiyaye zaman lafiya, da bada kariya ga fararen hula, da kiyaye tsaro da dai sauransu, haka kuma sun samar da babbar gudummawa wajen magance rikice-rikice, da daidaita matsaloli, da tabbatar da tsaron fararen hula da ma’aikatan tawagogin musamman na MDD da kuma ayyukan more rayuwa da sauransu. Dama dai mahukuntan kasar Sin sun sha nanata cewa, kasar ta sha alwashin tallafawa dukkanin wasu matakai, wadanda za su kai ga wanzuwar zaman lafiya da lumana, tare da ci gaban duniya, da daidaito tsakanin kasa da kasa. Game da hakan, wani jami’in jakadancin na Sin ya taba bayyana cewa, zaman lafiya da samar da ci gaba, su ne muhimman manufofin da duniya ta sanya gaba a halin yanzu. Kuma duk wani yunkurin kaucewa hakan zai zamo abun kyama, kuma ba zai kai ga nasara ba.
(Ahmad Fagam daga Beijing, China)

ShareTweetSendShare
Previous Post

Bayan Ya Janye Takarar Gwamna, Bala Kaura Ya Sake Nada Shi Sakataren Gwamnatin Bauchi

Next Post

Yadda Ango Ya Yi Shahada Wajen Kare Amaryarsa Daga ‘Yan Bindiga

Related

’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 
Daga Birnin Sin

’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 

6 hours ago
Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba
Daga Birnin Sin

Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

7 hours ago
AU Ta Yi Kira Da Kara Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Afirka Da Sin
Daga Birnin Sin

AU Ta Yi Kira Da Kara Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Afirka Da Sin

8 hours ago
Shugaba Xi Ya Jinjinawa Jaruman Kasar Da Suka Kwanta Dama A Ranar Shahidan Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Jinjinawa Jaruman Kasar Da Suka Kwanta Dama A Ranar Shahidan Kasar Sin

8 hours ago
Duniyar wata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Kaddamar Da Binciken Duniyar Wata Mai Zuwa A Tsakanin Shekarar 2024

11 hours ago
Kasar Sin Na Maraba Da Baki Kwararru Domin Su Bada Gudunmuwa Ga Ci Gabanta
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Na Maraba Da Baki Kwararru Domin Su Bada Gudunmuwa Ga Ci Gabanta

1 day ago
Next Post
Yadda Ango Ya Yi Shahada Wajen Kare Amaryarsa Daga ‘Yan Bindiga

Yadda Ango Ya Yi Shahada Wajen Kare Amaryarsa Daga ‘Yan Bindiga

LABARAI MASU NASABA

Somaliya Da ATMIS Sun Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Tsakiyar Kasar

Somaliya Da ATMIS Sun Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Tsakiyar Kasar

September 30, 2023
Yadda Aka Samu Jihohi 36 A Nijeriya

Yadda Aka Samu Jihohi 36 A Nijeriya

September 30, 2023
Kotu Ta Tabbatar Da Kefas A Matsayin Gwamnan Taraba

Kotu Ta Tabbatar Da Kefas A Matsayin Gwamnan Taraba

September 30, 2023
’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 

’Yan Wasan Kasar Sin Sun Zarce Tsammani A Hangzhou 

September 30, 2023

Abubuwan Da Ya Kamata A Sani Game Da Dannau

September 30, 2023
Kungiyar Kwadago Za Ta Shiga Yajin Aiki Kan Cire Tallafin Man Fetur

NLC Da TUC Na Hada Kan Ma’aikata Don Tafka Gagarumin Yajin Aiki

September 30, 2023
Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

Za A Wallafa Sharhin Xi Kan Ciyar Da Zamanantar Da Kasar Sin Gaba

September 30, 2023
Danbarwar Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ta Dawo

Danbarwar Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ta Dawo

September 30, 2023
Tinubu Ya Jaddada Aniyar Magance Rashin Tsaro Da Talauci A Nijeriya

Tinubu Ya Jaddada Aniyar Magance Rashin Tsaro Da Talauci A Nijeriya

September 30, 2023
AU Ta Yi Kira Da Kara Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Afirka Da Sin

AU Ta Yi Kira Da Kara Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Afirka Da Sin

September 30, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.