• Leadership Hausa
Saturday, December 2, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 months ago
in Dausayin Musulunci
0
Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa

Kayan Tarihi Na Manzon Allah S.A.W (II)

Masu karatu, assalamu alaikum wa rahmtullah. Har yanzu dai muna kan darasi a kan kyawawan dabi’un Annabinmu, Manzon Rahama (SAW).

A makon da ya gabata mun kawo muku darasi na biyu game da kankan da kai na Annabi (SAW) wanda a ciki muka yi bayanin cewa, wani mutum ya taba shigowa wurin Annabi (SAW), sabida kwarjini sai makerketa ta kama Mutumin, Annabi (SAW) ya ce masa “sauwaka wa kanka, ni ba sarki ba ne, ni dan wata Mace ne daga dangin Kuraishawa wacce take cin Kilishi.”

  • Dabi’un Kankan Da Kai Na Manzon Allah S.A.W, Darasi Na Biyu
  • Manzon Musamman Na Shugaban Sin Ya Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Najeriya

Haka nan, an karbo daga Abi Hurairah ya ce, wata rana na raka Annabi (SAW) Kasuwa, sai ya siya Wando, ya ce wa mai bayar da farashi, ya yi wa wandon farashi kuma ya kara dan wani abu a kai da za a bai wa mai sayar da Wandon, sabida farin ciki, ga riba ya samu mai yawa kuma an ce a kara masa wani kudi, kawai sai ya rugo ya cafke hannun Annabi (SAW) yana so ya sunbanci hannun, sai Annabi (SAW) ya janye hannunsa ya ce wannan baibayi ne ke wannan, n iba sarki ba ne, ni Mutum ne a cikinku. Sannan ya amsa wandon, na tafi in amsar masa, sai yace “mai kaya shi ya fi cancanta ya dauki kayansa.”

A nan darasi game da kankan da kai na Annabi (SAW) ya kammala. Yanzu kuma za mu duba: Adalci, Amana, Kamewa Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW).

Wato wannan babin zai yi magana kan Adalcin Annabi da Amanarsa da Kamewarsa da gaskiyar maganarsa (SAW). Ma’anar adalci shi ne rashin cutar da wani na tauye masa hakkinsa ko kuma adalci shi ne bawa mutum hakkinsa kai kuma ka karbi hakkinka ba tare da ka kara fiye da hakkinka ba.

Amana ita ce kiyaye kayan abin da aka ba ka ajiya, ko na magana ko na kudi ko na mukami ko na karatu.

Kamewa, ita ce kore sha’awa, duk abin da zuciya take so wanda zai zubar da mutunci, a barshi. Amma kamewa an fi fadar ta a wurin kiyaye farji, Mutum ya yi aure ya kiyaye al’aurarsa da mutuncinsa.

Adalcin Annabi (SAW) da Amanarsa da kamewarsa da gaskiyar harshensa, ya kasance shi ne mafi tsananin adalci da amanar mutane, shi ne mafi kamewar mutane, shi ne mafi gaskiyar mutane tun yana dan karaminsa, makiyansa suka tabbatar masa da duk wadannan siffofi, shi suke kawo wa amana, in ana so gaskiya ta bayyana shi ake nufa, tun kafin a aiko shi da Annabta ake kiransa da “Al’aminu – Amintacce”.

Ibn Ishak, Malamin Tarihi yana cewa, Annabi (SAW) ya kasance ana kiransa da Amintacce sabida kyawawn dabi’un da Allah ya sanya a jikinsa, Allah tabaraka wata’ala ya ce “Muda’in samma amin – ¬abin yiwa biyayya ne a Sama sannan kuma abin amincewa da Wahyi ne a Kasa” da yawan Malamai sun tafi cewa, wannan Ayar tana magana ne da Annabi (SAW), sai dai akwai wasu daga cikin masu fassara, sun tafi cewa, wannan Ayar tana magana ne a kan Mala’ikah Jibrilu.

Yayin da Kuraishawa suka samu sabani kan kabilar da za ta dora Hajril Aswad, suna kokarin buga yaki yayin da suka sabunta ginin Ka’abah, tsofaffi daga cikinsu suka ce ba rigima za a yi ba, mu kwana a cikin wancan masallacin kar mu gaya wa kowa bukatarmu, duk wanda ya fara shigowa, to shi zai yanke mana hukunci, kuma duk hukuncin da ya yanke shi kowa zai bi, duka suka amince da wannan shawara, sai gashi Annabi (SAW) ne ya fara shigowa yayin da yake dan shekara 35, shekara biyar kafin Annabta.

Ka’abah a ingantattun ruwayoyin Malamai, an gina ta sau 12:

  1. Mala’iku a dai-dai saitin Baitul Ma’amuri
  2. Annabi Adam (AS), shi ne wanda Allah ya saukar masa da Hajril aswadi da Makamu Ibrahim, Yakutu ne na Aljannah da suke haska masa garin Makkah in dare ya yi
  3. Annabi Shisu Dan Adamu
  4. Annabi Ibrahim da dansa Isma’ilu
  5. Larabawan Jurhum
  6. Amalikawa bayan rasuwar Annabi Isma’ila, su suka kwace garin, suka sake gina Ka’abah
  7. Kusayyu bin Kilab (Kuraishu)
  8. Kuraishawa – Annabi yana dan shekara 35 saura shekara biyar a aiko shi.
  9. Abdullahi bin Zubair – Dan Asma’u binti Abibakr
  10. Hajjaju bin Yusuf, bayan ya kashe Abdullahi bin Zubair
  11. Suldanul Maradiy – Gwamnan Daular Usmaniyya
  12. Sarki Fahad – wannan ginin da yake yanzun (2023) a Makkah.

An karba daga Rabi’u dan Husaini ya ce, Annabi (SAW) ya kasance ana kawo kara wurinsa a Jahiliyya.

Kuraishawa suna son shi, sun yarda da shi sabida amanarshi amma yana zuwa da Musulunci suka ce sam ba haka ba. Manzon Allah (SAW) ya ce, Wallahi ni amintacce ne a Sama kuma amintacce ne a kan Kasa.

An karbo Hadisi daga Sayyadina Aliyu cewa, Aba Jahlin ya ce wa Annabi (SAW) “Mu ba ma karyataka sai dai muna karyata abin da kazo da shi” sai Allah ya fada cewa “fa’innahum la yukazzibunaka, walakinnaz zalimina bi’ayatillahi yajhadun – lallai ya rasulallahi ba kai suke karyatawa ba, ayoyin Allah suke karyatawa.” kila an ce, Aknasu Ibn sharafin (shugaba ne a kabilarshi, sun fito su 200 amma da ya ji an ce, Abu Sufyan ya tsira da kayan kasuwancinsu sai ya noke ya gudu, ), ya hadu da Aba Jahlin da Daddare ranar Badr,  ya ce Ya Abal hakam (Abu Jahlin Annabi (SAW) ya ke kiranshi) babu wani a nan da yake jin maganarmu, da gani sai kai “Fada min gaskiya kan Muhammadu, Mai gaskiya ne ko mara gaskiya?” sai ya ce “Wallahi Muhammadu mai gaskiya ne kuma bai taba karya ba!” sabida jin wannan gaskiyar, ya shawarci Abu Jahlin da kar ya yi yaki amma ya yi girman kai shi kuma Aknasu ya juya da rundunarsa zuwa gida.

Sabida wannan Hikima da ya yi, ya tseratar da Kabilarsa daga hallaka, ba a kashe su a yakin Badr ba. Malamai sun rahoto cewa, Sarki Aknasu ya musulunta da kabilarsa daga baya.

Dauloli biyu manya masu karfin soji da tattalin arziki a wannan lokaci guda biyu ne, Farisa da Rum, kusan kowane lokaci cikin yaki suke, Farisa ta samu rinjaye bayan shekaru bakwai sai Rum ta samu rinjaye, Kaisarar Rum ya yi alkawarin zuwa dakin Allah da ke Baitul Makdisi a kafa don Godiya ga Ubangiji kan nasarar da yasamu a kan Farisa, a dai-dai wannan lokaci kuma Annabi (SAW) ya bayyana ya tura da wasika zuwa Sarkin Hira shi kuma ya kai ma Kaisara. Sai aka hadu da Sarkin Hira da Kaisara da dan aiken Annabi (SAW) (Duhyatul kalbi) a garin Baitul Makdisi.

Sarki Kaisara ya tura a nemo masa dangin Annabi (SAW) da suka zo Baitul makdisi kasuwanci, sai aka zo da su, Abu Sufyan yana jagorantar tawagar Kuraishawa, bayan shigarsu fadar Kaisara sai ya fara tambayar wanda shi ne makusancin Annabi (SAW) – Abu Sufyan.

Hiraklu – Sarkin Rum na wannan lokaci, ya tambayi Abu Sufyan da cewa, kun taba tuhumarsa da karya, Abu Sufyan ya ce, A’a, duk abin da ya tambaye ni ina ba shi amsa ta gaskiya sai abu daya da na yi zanba a ciki, Abu Sufyan ya ce wa sarki ba sa tuhumar Annabi (SAW) da laifin komai sai dai ya fada mana wata magana da mun rasa yadda za mu yi da ita. Sarki ya ce, wacce magana ce? Wata rana ya ce mana ya zo wannan gari kuma ya koma duk a dare daya. Kuma mun san wannan tafiyar wata biyu ce zuwa da komawa, Ikon Allah, mai gadin Masallacin yana kusa, sai ya gasgata maganar Annabi (SAW), ya ce “A wannan daren, na kulle duk kofofin Masallacin amma daya ta ki rufuwa, na kira Mutane su taya ni amma ta ki rufuwa, sai aka ce a bari da safe a kira magina su gyara kofar, da safe sai na ga alamar mutum ya shigo ya yi Sallah a ciki kuma na ga alamar huji a jikin bangon da Annabawa suke kulle abin hawansu in sun zo masallacin, sai na tabbatar cewa, lallai wani Annabi ya shigo masallacin”. Don haka, Rumawa babu abinda ba su sani ba game da Annabta.

Tags: AdalciAmanaHalayen KwaraiManzon Allah
ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Sin Ta Kubuta Daga “Kangin Talauci”

Next Post

Abubuwa Takwas Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Bai Wa Fifiko

Related

Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa
Dausayin Musulunci

Allah Ya Girmama Annabi (SAW) Cikin Fadi Da Aikatawa

1 day ago
Kayan Tarihi Na Manzon Allah S.A.W (II)
Dausayin Musulunci

Kayan Tarihi Na Manzon Allah S.A.W (II)

1 week ago
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Kayan Tarihi Na Manzon Allah (SAW)

2 weeks ago
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Kyawawan Halayen Annabawa Da Ke Nuni Da Cikarsu (AS)

3 weeks ago
Abubuwan Da Allah Ya Fada Cikin Siffanta Annabawa (AS)
Dausayin Musulunci

Abubuwan Da Allah Ya Fada Cikin Siffanta Annabawa (AS)

4 weeks ago
Kamannin Annabawa Suna Tukewa Ne A Siffofin Manzon Allah (SAW)
Dausayin Musulunci

Kamannin Annabawa Suna Tukewa Ne A Siffofin Manzon Allah (SAW)

1 month ago
Next Post
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu

Abubuwa Takwas Da Gwamnatin Tinubu Za Ta Bai Wa Fifiko

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar Sin 

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar Sin 

December 2, 2023
Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Tare Da Dukkan Bangarori Don Gina Duniya Mai Tsabta

Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Tare Da Dukkan Bangarori Don Gina Duniya Mai Tsabta

December 2, 2023
An Kori Jaruma Daga Fim Saboda Wallafa Sakon Goyon Bayan Falasdinawa

An Kori Jaruma Daga Fim Saboda Wallafa Sakon Goyon Bayan Falasdinawa

December 2, 2023
Dusar Kankara Ta Sa An Dage Wasan Bayern Munich Da Union Berlin

Dusar Kankara Ta Sa An Dage Wasan Bayern Munich Da Union Berlin

December 2, 2023
Nijeriya Na Fuskantar Karancin Kayan Noma

Nijeriya Na Fuskantar Karancin Kayan Noma

December 2, 2023
Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Kundin Tattara Bayanai Na Ilimi

Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Kundin Tattara Bayanai Na Ilimi

December 2, 2023
Na Fi Jin Dadin Rubutu Da Sassafe Ko Dare – Princess Mazadu

Na Fi Jin Dadin Rubutu Da Sassafe Ko Dare – Princess Mazadu

December 2, 2023
Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana

Bayan Sace Fiye Da Mutum 100 A Zamfara: Kauyukan Da ‘Yan Bindiga Suka Sanya Wa Haraji Na Fuskantar Barazana

December 2, 2023
Tsaka Mai Wuyar Da Masu Gidajen Burodi Ke Ciki A Kaduna – Yarima

Tsaka Mai Wuyar Da Masu Gidajen Burodi Ke Ciki A Kaduna – Yarima

December 2, 2023
Gwamnatin Legas Za Ta Yi Amfani Da Fasaha Don Magance Matsalolin Cikin Gida

Gwamnatin Legas Za Ta Yi Amfani Da Fasaha Don Magance Matsalolin Cikin Gida

December 2, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.