Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles ta doke abokiyar karawarta kasar Ghana a wani wasan sada zumunci da suka buga a kasar Moroco.
Cyril Dessers da Ademola Lookman ne suka jefa wa Nijeriya kwallayen, kafin Jordan Ayew na kasar Ghana ya farke wa Ghana kwallo daya a minti na 90 da fara wasan.
- Da Wuya Bankuna 17 Cikin 24 Su Mallaki Sabon Jari Da CBN Ya Tsara -Rahoto
- Tinubu, Ka Taka Wa Wike Birki Ko Ka Fadi Warwas A Abuja A 2027 – Shugabannin APC
Manyan ‘yan wasan Nijeriya da suka hada da Victor Osimhen,Troost Ekong da Ahmed Musa ba su samu goron gayyata daga kocin tawagar, Finidi George ba wanda yake rikon kwarya.
Amma kuma ‘yan wasan na Nijeriya sun zage damtse wajen ganin sun doke kasar Ghana, Super Eagles za su hadu da kasar Mali a mako mai zuwa a daya wasan sada zumuntar.