Gwamnatin Jihar Katsina tare da hadin gwiwar kamfanin tuntuba ta shirya taron ranar manoma a jihar.
Taron shi ne karo na farko ya gudana ne a Daura da ke Jihar Katsina karkashin jagorancin kamfanin kwararrun mai suna “Aliyos Consultancy Trade Promoters Cooperatibe Society”.
- Zaben 2023: Majalisar Dinkin Duniya Da ECOWAS Sun Yi Sabon Gargadi
- An Watsa Shirin Bidiyo Na Tallata Shagalin Murnar Bikin Bazara A Wurare Daban Daban Na Duniya
Taron ya hada dubun dubatar manoman rani da na damina daga kananan hukumomin jihar karkashin jagorancin daraktocin aikin gona na kananan hukumomin 34, ya kuma gayyato kwararru masana aikin gona da nufin tattaunawa domin kara wa juna sani a bangaren aikin gona wajen inganta harkokin noma.
An dai yi wa taron lakabi da “Bunkasa aikin gona domin dogaro da kai hadi da wadatar da kasa da abinci”, na da nufin baje kolin iri amfanin gona domin magance kowane kalubale ta hanyar tattaunawa da nufin kawo mafita a lokacin da wata matsala ta faru.
“Ana Iya wayuwar gari a yi hasashen damina da ake sa ran za ta kai wani lokaci, to amma sai ya kasance ruwa ya yanke, irin wannan taro za a tattauna a wayar wa manoma kai a kan yadda za su samu mafita.”
Haka kuma an tattauna yadda kamfanin zai iya tallata wa manoman da amfaninsu ga kamfanonin da ke sarrafawa da sauran masu bukatar amfanin da aka noma ga mabukata a fadin duniya.
Abubuwan da suka gudana a wajen taron sun hada da baje kolin iri amfanin gona daga kowane bangare na Jihar Katsina da wasu makwabtan jihohi da kasashe irinsu Jamhuriyar Nijar.