‘Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari garin Dan-Ali da ke karamar hukumar Danmusa ta Jihar Katsina, inda suka hana mutane gudanar da sallar Juma’a a wasu masallatai.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun je yankin dauke da muggan makamai, inda suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya tayar da hankalin masu ibada.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Kudin Sufuri Da Kashi 40 Ta Hanyar Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas
- Wakilin Sin: Ya Kamata A Kiyaye Da Karfafa Gudummawar MDD A Fannin Yaki Da Ta’addanci
Wani mazaunin garin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce harin na da nasaba da kama Aisha Bala, wata mata a garin, da jami’an tsaro suka yi bisa zargin cewa tana taimaka wa ‘yan bindiga da bayanai.
Sai dai majiyar ta jinjina wa jami’an tsaron Katsina na Security Watch Corps bisa jajircewarsu wajen korar ‘yan bindigar, tare da rokon gwamnati ta kara tura jami’an tsaro domin inganta tsaro a yankin.
“‘Yan bindigar sun kai hari lokacin sallar Juma’a, mutane suka tsere yayin da suka fara harbe-harbe.
“Mun gode wa jami’an tsaron da suka kore su, amma har yanzu muna bukatar karin jami’an tsaro a yankin nan. Al’amarin yana kara ta’azzara,” in ji majiyar.
Sama da mako guda, mazauna garin Dan-Ali da kauyukan da ke kusa da su kamar Gwarjo, Dangane, Tudun, Tasha Kadanya, da Tasha Biri ba sa iya zuwa gonakinsu saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga.
An ruwaito cewa an yi garkuwa da wasu manoma da dama, wanda hakan ya jefa al’umma yankin cikin firgici.
Hanyar Yantumaki-Kankara, tana fuskantar yawan hare-haren ‘yan bindiga.
Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.