Wata mai yi wa kasa hidima (NYSC) wacce take aikin hidimar kasa a karamar hukumar Gamawa da ke jihar Bauchi, Khadija Lukman ta gwangwaje mutane masu fama da lalura ta musamman a karamar hukumar da Kekunan Hawa guda 100 domin saukaka musu gudanar da harkokin rayuwa.
Khadija mai lambar shaidar hidimar kasa BA/23A/3158 ta bayyana a wajen bikin mika kekunan hawan a ranar Juma’a cewa, wannan wani mataki ne na cika alkawarin da ta yi na cewa za ta taimaka wa masu fama da bukata ta musamman tun lokacin da take makaranta.
- Jihar Kaduna Ta Fara Ƙwaƙƙwaran Bincike Kan Yadda Lassa Ta Kashe Mutane A Asibitin Sojoji
- Yadda Zaki Ya Halaka Mai Ba Shi Abinci Har Lahira
A cewar jarumar matashiyar, wannan tallafin nata ta bayar ne ba wai domin ta karfafa wa wadanda suka ci gajiyar kekunan cigaba da yin barace-barace ba, illa domin ta taimakesu da karfafa musu guiwa wajen zirga-zirgan neman inganta rayuwarsu.
Khadija ta jawo hankalin wadanda suka ci gajiyar da kar su yi kasa a guiwa ko cire tsammani wajen fafutukar cika burikan rayuwarsu a kowani lokaci.
Khadija ta ce ta samu tallafi wajen aiwatar da wannan kyakkyawar aikin nata ne da gudunmawar daraktan cibiyar Beautiful Gate Handicap da ke Jos ta jihar Filato, Barista Ayuba Gufwan.
A gefe guda, mambar hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima, ta kuma horas da matasa sama da 100 kan yadda za su hada sabulu, man shafawa, kamshin daki da dai sauransu.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar, Fatima Muhammad, ta gode wa ‘yar Hidimar kasar da wanda ya dauki nauyin tallafin bisa taimaka musu, ta musu addu’ar Allah saka musu da alkairi.
A bangarenta, ko’odinetar hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) a jihar Bauchi, Rifkatu Yakubu, ta jinjina wa matashiyar ne bisa gudanar aikin da kai tsaye zai kawo sauki ga mutane masu fama da bukata ta musamman.
Kan hakan ne ta yi kira ga masu hannu da shuni da gwamnatoci da su karfafawa matasa masu yi wa kasa hidima da ke da kyakkyawar niyya da tsarin da za su taimakawa al’umma a kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp