• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Yunwa Da Kunci Suka Karu Bayan Fara Azumin Ramadan A Gaza

by Sadiq
2 years ago
Yunwa

Al’ummar Falasdinu sun fara gudanar da azumin watan Ramadan cikin halin kunci, daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta, inda yunwa ke kara ta’azzara a yankin Zirin Gaza yayin da har yanzu aka kasa kawo karshen yakin da Isra’ila ta kwashe watanni biyar tana yi a kan fararen hula.

“Wannan wata na Ramadan ya sha bamban da dukkan Ramadan da suka gabata,” in ji Bilal abed Rabbo mazaunin Ramallah.

  • SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1
  • NEDC Ta Rarraba Kayayyakin Noman Rani A Jihar Yobe

A taron majalisar ministocin kasar na mako-mako, Firaministan Falasdinu Mohammed Shtayyeh, ya bayyana cewa, “Watan Ramadan ya zo a wannan shekara, yayin da al’ummarmu a Zirin Gaza ke fama da yunwa da kisa sakamakon laifukan kisan kiyashi da ake ci gaba da yi ba tare da kakkautawa ba, muna sa ran shiga tsakani.”

Ya ce suna jiran kotun duniya ta dakatar da wadannan munanan laifuka, sannan suna rokon Allah ya sanya ranakun watan nan mai alfarma ya kasance sassauci ga wadanda suke cikin ukuba, kuma a daina zubar da jini, yana mai kara cewa, Allah ne kadai yake da ikon ceto wadanda suke cikin yunwa da kuma rashin lafiya.

Falasdinawa dai na ganin cewa za a samu tashin hankali daga Yahudawan da ke kyamar Musulunci a cikin watan Ramadan.

LABARAI MASU NASABA

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

“Na yi imanin cewa ayyukan shahada za su karu kuma tsayin daka zai karu, musamman ta fuskar al’amarin Aqsa da hana masu ibada shiga masallacin domin yin addu’a, musamman matasa,” in ji Jamal mazaunin Ramallah.

Kasashen Qatar, Masar da Amurka sun yi fatan kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a daidai lokacin da ake gudanar da azumin Ramadan, wanda zai hada da sakin dimbin Yahudawan da aka yi garkuwa da su da kuma fursunonin Falasdinu, hadi da bude hanyoyin shigar da kayayyakin jin-kai, amma tattaunawar ta ci tura a makon jiya.

Hamas dai na neman a ba da tabbacin cewa wannan yarjejeniya za ta kai ga kawo karshen yakin, yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare har zuwa lokacin da zai kawar da Hamas din da kuma kwato sauran Yahudawan da ke hannun kungiyar.

Yakin ya kori kusan kashi 80 na al’ummar Gaza mai mutane miliyan 2.3 daga gidajensu tare da jefa dubbai cikin matsananciyar yunwa.

Jami’an lafiya sun ce akalla mutane 20 galibi yara kanana ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin ruwa a Arewacin Gaza.

Sojojin Isra’ila sun rufe arewacin kasar tun daga watan Oktoban 2023, kuma kungiyoyin agaji sun ce takunkumin da Isra’ila ke ci gaba da kakabawa yankin da tabarbarewar doka da oda, sun sun hana isar da isasshen abinci zuwa Gaza.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa akalla Falasdinawa 31,112 aka kashe tun bayan fara yakin, ciki har da gawarwaki 67 da aka kai asibitoci cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?
Kasashen Ketare

Wadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa?

September 28, 2025
Next Post
Za Mu Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Azumi – Sufeton ‘Yansanda

Za Mu Tabbatar Da Tsaro A Lokacin Azumi - Sufeton 'Yansanda

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
peter

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025
Jonathan

Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole

October 10, 2025
Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka

Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka

October 10, 2025
Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya

October 10, 2025
Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata  

October 10, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

2027: INEC Ta Nemi A Gaggauta Amincewa Da Ƙudirin Sake Fasalin Tsarin Zaɓe

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.