A bana za a bude sabon babin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, duba da cewa, an cika shekaru 11 da gabatar da ita. A cikin wadannan shekaru da suka gabata, shawarar ta samar da damar cudanya da cin moriya cikin hadin gwiwa da dama, har mabambantan kasashe sun amince cewa, wannan shawara ta kasance wani muhimmin dandali na hadin gwiwar kasa da kasa mai samun karbuwa matuka. A halin yanzu, duniya na shiga wani yanayi mai cike da sauye-sauye, al’ummar duniya na mai da hankali matuka kan yadda za a ci gaba da amfani da wannan shawara a nan gaba, da ma yadda kasashe mabiya wannan shawara za su ci moriya tare. An kira wani taron karawa juna sani a jiya Talata a nan birnin Beijing, don samar da karin haske game da hakan.
Daga shekarar 2016 zuwa 2024, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira irin wannan taro mai alaka da ayyukan shawarar har sau 4, inda ya gabatar da alkiblar da za a bi wajen raya wannan shawara. A gun taron na wannan karo, Xi ya amince da manyan ci gaban da aka samu da bayyana ayyukan da za a gudanar nan gaba wajen raya shawara mai inganci, da kuma jadadda muhimmancin samar da damammaki mafiya kyau da dorewa wajen samun bunkasuwa tare.
Tabbatar da zamanintar da al’umma buri ne na kowace kasa, shawarar na mai da hankali kan wannan batu dake jan hankalin kasa da kasa. A cikin shekaru 10 masu zuwa, raya ingantacciyar shawara za ta samarwa duk fadin duniya karfi a bangaren raya tattalin arziki, da ma samar da sabbin damammaki ga kasa da kasa wajen zamanintar da al’umomminsu, ta yadda za a gaggauta raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)