• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Zan Samar Da Sabuwar Nijeriya – Kwankwaso

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa, wanda shi da kansa yake jagoranta.

Kwamitin mai mambobi 1,053 a Abuja, wanda Kwankwaso ya tabbatar da cewa samar da sabuwar Nijeriya abu ne mai yiwuwa a karkashin shugabancinsa.

  • 2023: Irin Alkawuran Da Kwankwaso Ya Yi Wa ‘Yan Jihar Delta

“Yawan mutane masu daraja da mutunci da suka taru a wannan babban dakin taro da nufin a hadu a yi tafiyar mai matukar muhimmanci. Dalilin da ya sanya aka gudanar da taron a haka shi ne don a sami natsuwa tare da la’akari da yanayin tsaro a Nijeriya a halin da ake ciki ta yadda ba za a sanya mutane cikin hatsari ba, sakamakon tsaro don dai kawai halarci taron kaddamar da dan takara,” kamar yadda ya fada.

Ya kara da cewa kwamitin yakin neman zaben na shugaban kasa tare da miliyoyin ‘yan sa-kai da magoya baya da suke dukkanin jihohin Nijeriya 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja za su ci gaba da aiki kafada da kafada domin tabbatar da nasarar jam’iyyar NNPP a babban zabe.

A cewarsa, samun sabuwar Nijeriya a karkashinsa na nufin, “Nijeriyar da za tabbatar da adalci da tsoron Allah, Nijeriya da za a tabbatar da samun ingantaccen tsaro, Nijeriyar da za a tabbatar da zaman lafiya da lumana, Nijeriyar da za a tabbatar da daidaito ga kowanne dan kasa, Nijeriyar da za a sami ingantaccen ilimi da kula da bangaren lafiya ta hanyar samar da kayayyakin aiki na zamani ga kowa, Nijeriyar da za a rika gudanar da shugabanci na adalci da tausasawa ga kowa.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

“Wannan shi ne sabuwar Nijeriya da mu a jam’iyyar NNPP muke aiki ba dare ba rana da za a fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2023 da izinin Allah.”

Kwankwaso ya ce zai fara gudanar da yakin neman zabensa a yanki Bauchi a ranar 12 ga watan Janairu na Arewa maso Gabas. A cewarsa, kwamitin yakin neman zaben da ke sadaukarwa da gaskiya da rikon amana da aiki tukuru ga su da kwarewa da tsoron Allah da zai amfanar da ‘yan Nijeriya wanda za su tabbatar da samun nasarar Rabiu Musa Kwankwaso a zaben 2023.

A hannu guda kuwa, mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Buishop Isaac Idahosa ya kaddamar da sashin bayar da tallafin kudi don yakin neman zabe mai adireshin donation.rmkidahosa.com.
Ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su bayar da tallafi na yakin neman zabe. Ya ce a duk lokacin da kake son abu, dole ka zuba jari a cikinsa.”

Haka kuma ya ce, kwamitrin yakin neman zaben shugaban kasa ba zai yi siyasar kudi ba ne, amma yana bukatar kudi na tafiye-tafiye. Ya tabbatar da cewa za a rantsare da shi mataimakin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
Babu Barazanar Kai Hari A Kano – ‘Yansanda

'Yan Bindiga Sun Sace DPO A Jihar Filato

LABARAI MASU NASABA

Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala

November 2, 2025
Yaya Da Kani Sun Mutu A Cikin Ramin Masai A Kano

An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano

November 2, 2025
Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.