Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya dakatar da Musa Isah Achuja, Ohi na Eganyi, bayan kashe ‘yan sanda da ‘yan banga a karamar hukumar Ajaokuta da ke jihar.
Achuja shi ne shugaban majalisar sarautar gargajiya na yankin Ajaokuta.
Gwamnan ya ce ya dakatar da sarkin na da nasaba da harin da aka kai wa jami’an tsaro a ranar Asabar.
An ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna a unguwar Jidda-Bassa da ke karamar hukumar Ajaokuta a jihar Kogi, inda suka kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biyar.
Gwamnan ya sanar da dakatar da sarkin ne a wata sanarwa da Onogwu Muhammed, babban sakataren yada labaransa ya fitar.
Ya yi gargadin cewa gwamnatinsa za ta hukunta duk wani basaraken gargajiya da ke da alaka da ‘yan ta’adda.
Bello ya aike da takardar gargadi ga Mustapha Aka’aba, shugaban karamar hukumar Ajaokuta, ta hannun kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, inda ya bukaci amsa cikin sa’o’i 24.
Gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da shugabannin kananan hukumomin daga yankunansu har zuwa wani lokaci.